Chapter 31
Chapter 31
abinda kuke ciki na sani, da zaryar da kake tayi a gidan su, har kuka yi kulla-kullar da kuka nemo ta kuka dawo da ita unguwar nan duk don kana kulafucin ta”. Malam Isa bai iya tsayawa ya cigaba da sauraron ta ba ya juya da sauri ya bi bayan Innar Hauwa. Tana isa gidan shima ya iso sabida saurin da yake yi saura kadan babbar rigar sa ta tadiye shi. Tana shiga gidan ya doka sallama sai Inna ta dauko mayafinta data rataye a jikin kofa ta fito. Sabanin da da zata yi masa iznin shigowa yanzu sai ta fita ta tadda shi a zauren. Suka gaisa Malam Isa yanata rawar jiki yana bata hakuri wai bai san me Maikosai ta gaya mata ba. Inna ta dube shi da manyan idanun ta irin na Hauwa masu neman fadowa kasa sabida girma ta ce. “Malam Isa, mutunci da makwabtaka ne tsakanin mu, ina ganin girman ka da mutuncin dake tasakanin ka da maigidana, da hakkin makwabta da kake saukewa dare da rana, bai kamata kuma ka yi min kazafi ba ban ji ba ban gani ba, yaushe nace zan yi GAIBA? Balle har na aure ka?” Malam Isa ya hau gumi yana bata hakuri yace wallahi shi da bakin sa bai yi zancen nan da Maikosai ba, ya dai yi zancen cikin hira da Dan ta Sunusi, inda yace masa “da ace zata yi Gaiba….”. Bayan wannan bai kara komai ba, watakila Sunusin ne ya gaya mata, ita kuma ta canza maganar yadda taga dama, amma ta yi hakuri. Inna tace “baka yi min laifin komai ba sai alkhairi Malam Isa, amma ka sani ko Malam Bilyaminu bai dawo ba bazan yi wani aure ba, daga nan har gaban abada! Burina kadai a duniya “Hauwa ce”. In rayu tare da ita, in kula da ita, in tsare mata mutuncin ta. Amma bayan wannan bani da wani sauran abu da ya rage min a rayuwa ta sai fatan cikawa da Imani”. Malam Isa dai hakuri yake bayarwa, ya kuma roketa kan kada hakan yayi sanadin bacin zumunci da makwabtakar su, ya bar zancen har abada ba zai sake tada shi ba, don Sarham ma ya hanashi. Maikosai kuma zai ja mata kunne itama. Inna tace babu komai. Ya wuce. Daga nan ya gaya mata maganar dabbobin ta daya kiwata mata, suna nan garke guda a cikin kangon gidan sa. Inna ta rasa da me zata godewa wannan karimin makwabci, ta yi masa godiya mai tarin yawa don tana matukar son dabbobin ta. Tace ya bar su anan su cigaba da zama tare da nasa, zata cigaba da bada abincin su. Wanda yayi a baya Allah ya biya shi da aljannah. Nan yake gaya mata ai SARHAMU yafi shekara yana sayen dussar su da harawar su. Mamakin Inna da Sarham ya kara ninkuwa, ta ji yaron ya kara kwanta mata a rai, wato ba ita kadai ba, ba ‘yar ta kadai ba, hatta dabbobin ta ababen kulawa da darajjawa ne a gare shi. Ya Allah! Da me zata biya wannan bawan nasa banda addu’ar alkhairi mara yankewa gareshi, da iyayen da suka kawo shi duniya da zuri’ar sa??? Sukayi sallama ya tafi, ta koma gida tana labartawa Hauwa abinda ya faru a gidan Malam Isa da zauren su. Hauwa tafi Inna fusata, tace zata je ta tadda Talatu Maikosai ta gaya mata ba abinda zai kawo su gidan ta koda zasu koma kwana a kan kwalbati in sha Allahu. Inna ta hana ta tace “tura mata aniyarta mutuncin Malam Isan zaki duba, na gaya miki ashe dabbobina duka suna garken sa yana kiwata mini har yau”. Wannan ne ya dan sanyaya ran Hauwa ta daina jin haushin Malam Isa amma sosai ta shaka da Maikosai. **** ***** ***** RACE COURSE, KANO A wajen kallon Polo na Dawakai wato a filin sukuwa (Race Course) dake unguwar Nassarawa, Salele ya ga Jamil Zakari a matsayin wanda ya lashe kofin gasar dawakai (sukuwa) wanda akayi a ranar, dama dai Jamilu kwararren dan Polo ne, sun dade suna haduwa da Salele a wurare mabanbanta na tseren Dawakai, suna gaisawa, don ya san shi tun a jinyar da Hauwa tayi, sanda ya kadeta da mota. Yau da Jamil Zakari ya lashe kofi Salele ya shiga sahun samari masu kutsawa suna gaisawa da Jamil Zakari Dan Agundi, Salele yana cikin samari ‘yan kallo masu cike da fata da burin watarana su zama manyan ‘yan Polo kamar Jamil Zakari Dan Agundi. An fara watsewa kenan Jamilu ya shiga farar motar sa kirar (kia picanto) zai tafi sai ya hango Salele yana ‘waiving’ dinsa daga nesa wato yana ta dago masa hannu, har ya kunna motar ya dakata har Salele ya iso da gudu yana haki yana dariya. Jamilu ya fiddo gudar naira dari ya baiwa Salele, wadda a yanzu zata yi kimar kamar ace naira dubu daya. Salele don murna bai san lokacin da ya hau barin zance ba. “Yaushe zaka zo gidan su Innar Hauwa ne? Sun dawo bada jimawa ba, sun gine gidan su ya koma sabo dal, sun tare tuntuni, jiya ma Innar Hauwa ta shiga gun Innata sun gaisa har Innata ta zo gidan ta yiwa Hauwa kitso”. Jamilu yayi sakare! Yana sauraron Salele, kafin ya ji zuciyar sa ta harba, tsohon mikin son Hauwa-Kulu da yake kwana yake tashi da shi ya motsa kansa a kasan ransa, bai san sanda yace da Salele ya shigo gaban motarsa su je ba. Salele ya kame a gaban mota suka dauki hanyar Kofar Na’isa. Inna da Hauwa a tsakar gida, Inna na tankaden garin tuwo Hauwa na sallar la’asar akan dardumar sallah anan tsakar gidan su mai yalwa da sanyin sabon siminti, saidai yanzu babu shukokin su na Umbrella da bishiyar dalbejiya, don haka basu fiya zama a tsakar gidan da rana ba sai da yamma irin haka ko da daddare. Sai sallamar Salele suka ji, yace Inna kuna da bako” Inna da yake ta san Sarham zai zo sai tace “gidan bakon sa ne da zai tsaya a waje ya turo ka? Ko ba sallama yake da kansa ya shigo ba? Yau nake ganin sabon salo banbarakwai wai namiji da suna Hajara, kace ya shigo, kuma daga yau kada ya kara aikomin yaro idan yazo, shi da gidan su?” Salele ya koma yace da Jamilu Inna tace ya shiga. Inna da Hauwa sai ganin Jamilu Zakari suka yi a kan su, yayi sallama kamar an jefo shi. Ya shigo tsakar gidan su cikin kyakkyawar shiga ta hawan Polo. Idanun sa akan Hauwa ya hau sakin Hamdalah a fili kafin ya zube gaban Inna kamar mai neman gafara. Zai fara gaisheta Inna ta ce “tsaya-tsaya, wa nake gani kamar Jamilu? Wai dama kai ne ka aiko Salele?” yace “ni ne Inna” tace “to sawunka a likkafa Jamilu ka juya ka koma inda ka fito, kafin ka janyo min tijara, yau ko gaisuwa babu tsakanin mu wallahi ka ji na rantse ka tashi ka fice mana daga gida, kada ka kara zuwa balle ka janyo min bacin rai Ina fama da ciwon zuciya, zuciyata tayi rauni kuma bata da lafiya bazata iya daukar bakin cikin ubanka ba”. Inna ta soma hawaye, tana rokon Jamilu ya tafi. Tun ba'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36