Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

don zan koma wajen aikina babu jimawa, na rako matata wankan jego ne, amma mun koma Jeddah da aiki tun da jimawa”. Hauwa ta fiddo manyan idanun ta cikin mamaki ta ce “likita dama kana da mata?” Ya yi murmushi ya ce “mamakin na menene haka? Amsarki a baya itace, a’ah, na dai aure ta babu jimawa, bayan na kammala karatun dana tafi yi a Jeddah, a can muka hadu, duk da dai ba haduwar mu ta farko kenan ba”. Hauwa tace itama likitar ido ce?” Dr. Sarham Yayi dariya yace “exactly! Amma ya akayi kika sani?”. Tace “na dade da sanin likitoci basa aure sai da liktoci ‘yan uwan su, watakila don kada a shafa musu cuta?” Sarham me zai yi ba dariya ba yace “wato shi likita bashi da cuta a jikinsa Maijidda?” Tace “da sauki dai” anan ma ta kara bashi dariya sosai, yace “ni kuwa da har na yi miki takwara, na dauka kema likitar zaki so zama?” Kafin Hauwa ta kara magana sai Malam Isa ya fito yana musu sallama zai wuce gida, tare da Salele. Salele yaga Sarham, nan da nan ya shaida shi, ya hau yage baki don bai manta shi ba da tarin alherin da ya dinga yi masa don ya dinga raka Hauwa Makaranta. Suka gaisa da Salele suka yi sallama da su suka wuce, shi da Hauwa suka koma wajen Inna. Hauwa na tambayar sa cikin mamaki. “Da gaske likita ka yi min takwara da ‘yar ka?” Zancen a kan kunnen Inna, ta dago tana kallon shi da mamaki itama, tace. “Sarhamu kayi aure ne banida labari?” Sarham ya sunkuyar da kai yana dan murmushi yace “eh Inna, har an samu karuwar Hauwa’u, HAUWA-KULU!”. Ya dauko wayar sa daga aljihun sa ya nunawa Inna hoton Waheedah cikin pink shawul daya dauketa dazu. A takaice ya basu labarin yin auren sa da Dr. Madinah bayan ya kammala karatun da ya kai shi Jeddah, da irin neman da yayi musu kamar ya zautu bayan dawowar sa. A ranar ya jima tare da su suna ta labarin rayuwar su a kurna, rijiyar lemo da kuma unguwa uku, da ta karatun Hauwa da aka samu kammalawa da kyar, da sudin ludayi, ta gaya masa Hauwa ta fiddo da kyakykyawan sakamako sosai, wanda ba kokarin kowa bane nasa ne, madallah da shi, madallah da haihuwar ’ya’ya irin sa, masu zamewa al’umma fitilar rayuwa kuma bango abin jingina, madallah da tarbiyyar iyaye irin nasa, madallah da shigowarsa cikin rayuwar su”. Sarham (feeling overwhelmed with joy and happiness) saboda ya sha addu’a yau a bakin Inna, ‘yar sa Hauwa ma ta sha addu’a, tace yadda ya tsayawa Hauwa-Kulu wadda a yanzu za’a kira maariniya miskiniya ta samu ilmi daidai gwargwado duk da makantar ido, Allah ya tsayawa tashi Hauwar ko bayan ransa, yasa tayi ilmin da zata zamo mai amfani ga al’ummar duniya. Ita da kan ta Inna data nisa, taji yadda lafiya ta wadace ta, bata san sanda ta ce ta tuba tabi Allah ta bi asibiti ba! Daga yau ta daina kin asibiti tunda gashi ciwon shekara da shekaru ya tafi cikin sati biyu. Ta kara da cewa Sarham “ashe abin naku dace ne!”. Sai bayan kwana uku da yin haka aka sallami Inna, Sarham ya zo da mota ya dauke su zuwa gidan su na unguwa uku yace “Inna koda abinda zaku dauka a gidan ku dauka, ku fito ina jiran ku” Inna tace “ai nan ne gidan mu likita, yanzu anan muke zaune tun da jimawa” ya ce “na sani Inna, zaku raka ni unguwa ne bazamu jima ba, amma dai in har kin yarda da ni, to ki kwaso komai naku”. Inna ta hau kwasar kayan tana kaiwa boot din motar Sarham tana fadin “yarda da musulmi irin ka wajibi ne!”. Haka Hauwa ma, ta dauki kayan ta tsaf, suka kama hanya, Hauwa na gidan gaba Inna na baya. Sarham na tuki cikin nutsuwa da kwarewa, bai tsaya a ko’ina dasu ba, sai a kofar gidan su, gidansu na BADALAR Kofar Na’isa, dama sun riga sun shirya gidan dai dai gwargwado da taimakon Malam Isa da Salele. An zuba komai na amfani mai saukin kudi. Inna tunda taga an doso kofar Na’isa ta soma hawayen tuna baya, kirjinta ya hau yin sama da kasa, ita ta dauka zai kaita ta gaisa dasu Maikosai ne. Amma sai ta ga anyi fakin a kofar wani sabon gida a bayan Badala, in har bata yi kuskure ba, kuma idan har ba idon ta ke mata gizo ba nan din lungun su ne kuma unguwar su, da ko daga makanta irin ta Hauwa ta warke itama zata gane su, tunda ga gidan Malam Isa nan ba abinda ya canza shi. Sai ta kalli Sarham a gigice, bayan ya kashe motar a kofar gidan. Sai a lokacin yayi musu bayani cewa gidan su ne ya karba musu. “Ka karba mana kamar yaya?” Inji Hauwa, (sounding extremely puzzled). Inna kuma tace “ko dai ka gina mana?” Muryar Inna ta tambaye shi cikin kuka, don dai a kan idon ta taga lokacin da aka rushe gidan nasu wato gidan Malam Bilyaminu. Sarham yace “Allah ne ya nufa gidanki ya dawo gare ki Inna, ni kawai na taimaka ne, kuma kiyi hakuri zan yi wani shishshigi, a gaskiya zan yi karar kanin Baban Hauwa akan abinda yayi”. Inna ta fara kukan farin ciki da dariya a tare, ta ce “Dan nan me zan ce maka? Wace irin addu’a ya kamata in yi maka? Na rasa kalma a bakina da zata gode min kai. Amma ka bar maganar Zakari, ni kam me zai sake hada hanyata da Zakari? Na roke ka ka rabu da shi Allah na kaiwa karar sa kuma na tabbata zai saka mini. Na bar shi da fitowar rana da faduwar ta”. Ta share hawaye da habar mayafinta ta sake cewa. “Dan nan me zan ce maka?” A karshe Inna ta fashe da kuka tana ce da Hauwa “gidan mu ne Hauwa-Kulu! Sarhamu ya kwato mana da karfin mulkin Allah”. Hauwa wani irin shock ta shiga na wucin gadi bayan fahimtar hakikanin halin da ake ciki. A yau ma dakacen nan ta kara yi na shekara da shekaru, mai fatan “INAMA TA GA FUSKAR LIKITA SARHAM!” Suka karasa cikin gidan Inna rike da hannun Hauwa shikuma ya dauko bakko kayan su ya kai su har dakin da ya zama na Inna, an saka katifa a kasan kafet dirkekiya an shimfide ta da sabon zanin gado. A gefe ga kwabar saka kaya an yi mata. Haka dakin Hauwa ma amma ita a daki aka yi mata toilet don kada ta sha wahalar fitowa tsakar gida. Ga safayan daki da ba kowa yace na Baban Hauwa ne duk ranar da Allah ya dawo musu da shi. Sai kamshin sabon fenti da suminti gidan yake yi gwanin dadi. Dakuna uku ne aka yi musu kamar da, kitchen kuwa da toilets na zamani aka yi masu masu tangaran (tiles) da Inna tayi ta shafawa da hannun ta a gaban Sarham tana shi masa albarka. Hauwa duk jikin ta yayi sanyi musamman in ta tuna yadda ta ke share Sarham a baya, da kullacin wai ya makanta ta, Sarham is beyond her imagination

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});