Chapter 28
Chapter 28
A jikin barandar dakunan ya same ta a tsaye fuskar ta ta hade kamar kunun kanwa. Tana tsaye kawai harde da hannuwa a kirji. Ya lallaba ya tsaya dab da ita shima ya harde nasa hannuwan a kirji irin yadda ta yi. Ya ce. “Kuluwa, ni fa ba ke nake yiwa dariya ba, labarin da Inna ta ke bayarwa ne ya bani dariya”. Hauwa tayi narai-narai da idanu kiris ya rage ta fashe da kuka, tace “idan makanta abin dariya ce ai bata wuce kan kowa ba, idan gorin ido abun yi ne, ba komai ku cigaba da yi min”. Sarham ya kama baki cikin jin wani iri a ransa yace “kina nan a Kulun ki, Kululu, Kulun Majadun sarka mai rikicin gangan, har gobe baki canza ba, dama Inna ta ce ayi magana cibi ya zama kari. Yanzu saboda Allah ba dama muyi dariya sai ki ce rashin idon ki ake wa gori? Idanun nan fa mun fi ki son su dawo, ta yaya zamu yi murna da halin larurar da suke ciki? Kawai dai kina ji da rikicinki ne na gangan. Kullum addu’ar mu shine su dawo da gani kamar na kowa, idan masu dawowa ne, idan kuma ba masu dawowa bane Allah ya sa rashin su ya zama silar kaffara a gare ki da iyayen ki, ya baki aljannar Firdausi a madadinsu”. Hauwa ta dan saki rai, sai Sarham yace, “Maijiddah, tunda muka hadu bamu gaisa ba, bamu zanta ba, bamu yi fadan namu ba, koda yake yau mun dan taba. Anyway, nayi kewar ki MAIJIDDAH, bayan a baya na zaci bazan taba yin kewar ki ba, tunda baki damu da ni ba”. Hauwa ta yi murmushi ta ce a ranta, “kwarai kuwa, don ni dai kam in ba na dauko littafin makaranta ba, sam-sam bana tuno ka, gara-garama a lokutan da kalamanka masu haska min rayuwa ke sawa in tunaka”. Unfortunately, bata san cewa a fili ta fada ba. Sai ji tayi Sarham yace cikin rashin jin dadi da sosuwar rai, “I know, ba tun yau ba na sani ai, Inna ce kawata, uwata, kuma ita ta damu dani. Ni din a wurinki ba kowa bane face…”. Yayi shiru cikin tsananin damuwa da rashin sanin ta yaya zai yi ya kankare wannan tunanin daga zuciyar Hauwa-Kulu? Wanda ba tun yanzu ba ya lura yayi mugun samun muhalli a cikin ranta? Hauwa tace “kaima da ita kadai ka damu (Innar), daga zuwan ka ai ko la’akari da halin dana ke ciki baka yi ba ka fara tsokanata a kauyen Albasu, wai idona kamar ana soya kosai cikin mai, baka san cewa kukan farin cikin ganin ka nake yi ba, baka san halin dana ke ciki ba a lokacin, don ji nayi kamar Yayana Zulkifilu ya dawo, kamar farin-cikin rayuwa gabadaya ya dawomin, duhun zuciya ya gushemin, haske ya dawo a cikinta”. Da mamaki da jin dadi a muryarsa Sarham yace “to kiyi hakuri Maijidda, mu ajiye wannan a gefe, I’m happy to be your sourse of happiness, koda wannan kadai yau kin karramani, yanzu inaso ki bani labarin bayan rabo, da rayuwar ku gabadaya daga farkon tafiyata har ranar zuwan ku Albasu gidan mai magani”. Hauwa ta nisa, kafin tace “dogon labari ne likita, amma mun sha wahala wajen neman na kan mu a tashoshin mota, mun yi girki iri-iri ba hutu tamkar injin girke-girke a kowacce rana daga safe har yamma hakarkarinmu bai hutawa, ba don komi ba sai domin kada mu yi bara. Allah ya sani, ba abinda nake gudu da nakasata irin bara! Alhamdulillah for being alive, and for everything, musamman karatuna na sakandire, wanda (against all odds) sai da Allah yasa na kammala shi. A kullum inna sare da karatun, saboda wahalar zirga-zirga ta rashin idanu, kalaman ka nake tunawa suke zame min ‘inspiration’, kuma madubin dubawata a rayuwar lalurar dana tsinci kaina. Kalaman ka likita sunyi tasiri sosai wajen karafafani domin ina matukar jin dadin su a lokutan da na bukacesu, cewa da ka yi “akwai iyawa cikin nakasa”, kuma ka ce min “ba nakasashshe sai kasashshe”. Wadannan jimlolin naka guda biyu su suka zame min food for thought; su suka sa na dage na jure da zuwa makaranta ba ido. ‘Obstacles’ da ‘hindrances’ da ke cikin lalurar makanta duka basu sa na bari ya salwanta ba. Babu wani abin karaswa cikin labarin namu a bayan tafiyar ka, sai na bacin rai da wahala na zallan zalunci wanda kanin mahaifina ya sanya mu a ciki, a dalilin kwace gidan mu ya rusa shi. Ni ban sani ba ashe tun lokacin batan Baba, Inna ta fara ciwon zuciya, don likitan dazu ya tabbatar min ramin ya dade a zuciyar ta yayi akalla shekaru biyar, tana dai yin cuwuka a tsaitsaye tana kuma kula da shan magungunan gargajiya dake kara mata ‘immunity’, shiyasa bai ci karfin ta da wuri ba, bamu ankara ba sai da ya kayar da ita kasa warwas. Likita rayuwar da muka yi gabadaya kaji-ka ji….” ta zayyano masa daga farko har karshe har labarin bugeta da Yaya Jamilu yayi da mota ya kuma dage daga baya zai aure ta, wanda duk shi ya janyo musu komai. “Yanzu ina Jamilun? Me zai aura a wannan kankanuwar yarinyar? Bana jin lokacin ko SS2 kin gama, haba! This is sheer abuse. To ya san abinda Baban nasa yayi muku?” Sarham ya tambayi Hauwa, (furious in anger), ji yake idon sa idon Jamilu da Babansa Zakari sai ya shake su. Hauwa ta ce. “Yaya Jamilu ban kara haduwa da shi ba, bamu kara jin duriyar sa ba tun tafiyar sa Delta, kuma bana jin ya san abinda Baba Zakari ya yi wa gidan mu, saboda a lokacin yayi tafiya, ban dai sani ba ko idan ya dawo daga tafiyar da yayi wani ya bashi labari”. Sarham ya dade kan sa a sunkuye, yana tunanin ta wace hanya zai gayawa Hauwa ya sake gine musu gidan su, da gini irin na zamani? Jira yake a sallami Inna daga asibiti ya dauke su ya maida su gidan su na asali, ya kuma yi karar Baba Zakari kan abinda yayi, ko ba’a yi masa komai ba hukuma ta shiga tsakanin sa da su”. Sun dade a wajen suna labari shi da Hauwa, irin yadda bai taba jin tayi magana mai tsayin ta yau ba, sai da mamakin sa ya kasa boyuwa yace. “Maijiddah, ashe dama kina magana haka? Da ni ne ba kya yi? To meyasa Maijidda? Me nayi miki haka da zafi?” Ya tsareta da ido cikin tuhumar dalili, kai kace kamar tana ganin sa, Hauwa ta rufe ido cikin jin kunya, ta ce “ai don na dade ban ganka bane, daga yau zan rufe bakin ya koma kamar da” Sarham ya lumshe ido kamar tana ganin sa, idonsa a kan zara-zaran ‘yan yatsunta ya ce “a’ah ban yarda ba, a bude shi muyi ta shan hira abinmu, irin ta Yaya da kanwar sa da sukayi kewar juna, kin san ni mai baki ne, mai yawan hira ne, shiyasa tamu ta zo daya nida Inna. Maijiddah ina so in zama babban Yayanki daga yau, wanda kafin kowa ya ji damuwar ki nine mutum na farko da zan ji. Zan bar miki waya don mu dinga magana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36