Chapter 32
Chapter 32
kaiwa Zakari labarin an ganshi a gidansu ba. Jamilu ya mike ba shiru, yana kallon Hauwa da wani sabon so a cikin idanunsa, musamman da yaga ta kara girma tayi wani irin kyau ta yi bulbul da ita, datar ta tayi sumul. Likita Sarham ya tsaya mata da shan (freshmilk) wato danyar madara tana Nan fal firinjinta tun dawowarsu ita take daddaka don bata iya cin abinci sosai. Jikin sa yana rawa ya soma ja da baya. Tace “ko a lahira wani kan ci albarkacin wani, albarkacin ka Zakari ya ci ban yi karar sa hukuma ta kwatar min hakkina da tozarcin da yayi min a kan ka ba. Don haka tun muna shaida juna muna kuma ganin sauran mutuncin juna to ka fita daga inda muke”. Jamilu ya juya a hankali ya fice, saida ya tsaya a zaure ya share zufa da hawaye, shi ya san da gaske yake son Hauwa, son da yake mata ba shi ya dorawa kansa ba Allah ne. Saboda ita har yau ya kasa yin aure, alhalin ba abinda bai mallaka ba na rufin asiri a rayuwar sa. Daga nan gidan su Inna gidan Hajiyar sa ya wuce, ya kafa mata kahon zuka kan taje ta baiwa Inna hakuri, kada ta hukunta shi da laifin da ba nashi ba. Hajiya Rumanatu na jin an ga su Inna ta dauki mayafin ta tace su je ya kaita. Don dama zaman Jamilu har yau ba aure ya dameta. A mota Jamilu ya zauna, bayan Hajiyarsa ta shiga gidan, ya kifa kai a kan sitiyari ya rasa inda zai sa kansa da damuwa. Bai san yana son Hauwa bama sai yanzu, data kara girma ta zama cikakkiyar budurwa komai ya kai ya kawo. Hajiyarsa ta shige gidan da sallama. Inna sai ganin Haj. Rumanatu tayi tayi sallama, Inna ta amsa fuska ba yabo ba Kuma fallasa don ta gaji da nacin Jamilu da uwarsa. Inna ta yiwa kawarta tun ta kuruciya wato Rumanatu tarba ta mutunci, irin ta tsofaffin kawaye, bayan sun gaisa kafin Hajiya Ruma tace komai Inna ta hau rokon ta kan ta raba Jamilu da zuwa inda suke, ya rabu da Hauwa. Tace, “ku yi hakuri, ni babu wani aure da zan yi wa Hauwa-Kulu fau-fau, balle na dauketa da hannuna na kaita cikin zuri’ar Zakari a hallakamin ita da niyya sabida ‘yan ubanci irin nasa, muddin Zakari yaji labarin Jamilu na zuwa wallahi zai juyo da rashin mutuncin sa kan mu”. Iyayen suna can dakin Inna suna zantawa suna kuma fahimtar juna, Haj. Rumanatu na mai gamsuwa da hujjojin Inna akan bazata iya aurar da Hauwa ba, ba ga Jamilu kadai ba har ga kowanne namiji ma. A lokacin Salele yazo zai wuce, sai Jamilu ya roke shi ya sadada a hankali don Allah ya kira masa Hauwa su gaisa. Nan da nan Salele yabi umarnin ubangidan sa ya je yace da Hauwa tazo ana kiranta za’a bata sako, tace a baiwa Inna mana! Yace tana da bakuwa ne sun kule suna sirri. Haka ya kalallameta ta taso ta tako da hijab mai hannu har kasa a jikin ta zuwa soron su. Sai ta ji muryar Yayan ta Jamilu ya ce “Hauwa!” Ya saki ajiyar zuciya ya sake cewa, “Hauwa nine Jamilu, ni nace Salele ya kira ki, Hauwa ina kuka tafi duk tsayin shekarun nan kusan uku sai dawowa nayi daga Delta na nemeku na rasa? Ko kinsan har yau ban yi aure ba ina tsumayin dawowar ki Hauwa?” Hauwa ta dan waiga kamar me tsoron ko Inna na wajen, tace “Yaya Jamilu ne da gaske?” “Nine Hauwa’u, I missed you so much, and I truly love you kin sani Hauwa”. Hauwa ta ji duk ta rikice, ta kasa cewa komai domin maganar sa ta yau ta mata gingiringin, ta mata nauyi, rana ta farko da wani da namiji ya furta mata kalmar so da bakinsa da nata, taji kunya har kasan ranta, Jamilu yace. “Ki bani dama don Allah Hauwa, in turo magabatana gun Inna, in sha Allahu zamu yi aure ko a boye ne in ya so mu bar Kano gabadaya ba tareda Babana ya sani ba, ina mai baki hakuri kan abinda ya faru, na ji komai bayan dawowata kuma ba inda ban neme ku ba cikin Kano da wajen ta ban samu ko wanda yace ya san inda kuke ba. A kan ki Hauwa Babana ya kusa tsine mini, Inna kua ta kasa gane karfin son da nake miki ba irin wand azan iya hakura bane, don Allah Hauwa ki manta da komai, ki duba ‘yan uwantakar dake tsakanin mu, mu yi auren mu cikin alfarmar zumunci da kaunar juna, dama Bankinmu zasu yimin transfer kwanannan zuwa Ikeja, in yaso sai mu koma can”. Hauwa ta rasa abinda zata ce, domin Jamilu ya matukar bata tausayi, ya tafi da imaninta, ya kuma gama saye zuciyarta da wannan kauna da ya nuna mata, tayi shiru kawai tana sauraron Jamilun da zuciyarta da kunnuwanta, tana mai yarda da kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakinsa, zuwa can ta ce. “Ni fa Yaya Jamilu banida matsala, amma babu ruwa na a kan maganar aure. Allah ya sani ban rike ka da komai a raina ba, sannan kuma bana kin ka, ina ganin abinda yafi, ka nemi amicewar Inna ba tawa ba, ni din da komai nawa ababen ikonta ne kuma ni mai son yin biyayya ce a gareta, don haka duk wani hukunci da Inna tayi akaina, inaso ko bana so, bani da ja a kansa”. Jamilu ya gyada kai cikin gamsuwa da kalamanta, at least ya fahimci Hauwa bata kin auren sa koda bata furta tana son shi ba, tofa babu kiyayyarsa ko kadan a tare da ita, ya rausayar da kai yace, “ni kuma na yi alkawarin zan lallashi Inna, idan ta bani ke zan kuma kula mata da ke kamar yadda zan kula da kaina. I can understand her fear, kuma kwarai nake la’akari da abida take hangowa (taking the marital responsibility of a blind person will never be easy) amma abinda ta manta ni dan uwanki ne, jinin ki ne, I can possibly endure it fiyeda bare, aure sunnar Manzon Allah ne SAW bai yuwuwa ace saboda lalura ta makanta baza’a yi shi kwata-kwata ba tunda ke din ‘yar adam ce kamar kowa mai lafiyar yin aure, ni Jamilu na yi alkawarin zan zame miki miji abin alfahari kuma dan uwa wanda zamu raba rashin idanun ki tare, sannan wanda zai tsaya wajen ganin kin zamewa ‘ya’yan ki uwa tagari a yadda Allah ke son ganin ki, tsan tsaya tsayin daka wajen ganin cewa lalurar rashin gani bai sa kin kasa basu kulawa ba. Ni da kaina zan taya ki rainon ‘ya’yan mu Hauwa’u”. sai Hauwa ta kai tafuka ta rufe fuska cikin jin kunya tana murmushi kamar tace kasar ta tsage ta shige cikinta. Maganar Jamilu ta karshe kai tsaye ta sauka a kunnuwan Dr. Sarham Abbas ne, a lokacin da ya kashe motar sa “opel astra’, ya tako zuwa gidan ya sawo kai soron, cikin takunshin nan mai sauti gab-gab-gab na bakin cover shoes ma matukar daraja, ya shigo zauren su Hauwa, yayi harr da idanunsa a fuskokin su. Yana sanye da shirt
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36