Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da a kira, “na dade da baiwa wannan tatsuniyar baya” ne. A fili kuma yace “Madinah Soron Dinki, takamaimai me kike so da ni yanzu a takaice, da yasa kike min wannan binbinin haka?” Ai jin haka Madinah ta tabbatar yanzu kam Sarham ya gama da babin ta, yau ita Sarham ke cewa tana masa binbini! Wannan ba Sarham din data sani a baya bane halinsa duk ya canza, wancan jovial ne mai saukin kai da dadin sha’ani, ko dai wani ne mai tsananin kama da shi da irin sautin sa ta gamu da shi saboda yadda ta saka shi a ranta??? Sai kawai Madinah ta durkushe anan inda take tsaye, cikin korran grass carpet (ciyayi) ta saki kuka mai cin rai. A can zamanin baya Sarham ba abinda ke daga masa hankali irin damuwar Madinah Attahiru, amma wallahi yanzu bai ji ko gezau ba wai an tsikari kakkausa, ya yi kuka har fiye da wannan da take yi yau akan rashin Madinah, da kuma wulakancin da mahaifin ta yayi masa ranar da yace “ba zai taba baiwa dan almajirin gwamnati (dan malamin makaranta) ‘yar sa ba”. Ita nata kukan kuwa a yanzu ai na jin dadi ne, abinda bai sani ba, kukan Madina yau ya kunshi abubuwa masu dimbin yawa, har da wadanda tunanin sa da tsinkayen sa bai bashi ba. Bata taba daina son sa ba, a duka wadannan shekarun daidai da rana daya, ta yanke alaqar su ne domin ta samu damar yin biyayya ga mahaifin ta, wanda ba abinda bai yi mata a duniya ba, ya kuma fifita soyayyar ta akan ta ‘yan uwanta maza bakidaya kasancewar ita kenan masa diya mace, kuma auta a cikin ‘yan maza bakwai. Wannan shine dalilin nata. Sarham bai tsaya Madinah ta gama kukan bay a cika bujensa da iska ya bar wurin, sai dagowa tayi bayan ta share hawaye ta neme shi a filin wajen ta rasa. A lokacin ta cigaba da tuno rayuwarta ta baya tare da Sarham, abinda ya faru shekaru bakwai da suka gabata, ta tuno asalin ta, haduwar su, lokutan su tare a campus, da abubuwan da suka faru da ita bayan rabuwar tasu……. **** ***** **** WAIWAYE ADON TAFIYA! (2) DR. MADINAH ATTAHIRU A salin mahaifin ta Bakano ne dan asalin Soron Dinki, Soron Dinki wata karamar unguwa ce mai tsohon tarihi a jihar Kano, wadda ta haifi fitattun malamai da alkalai a tarihin jihar. Tana nan dab da gidan Sarki (Emir’s Palace). Mahaifin Attahiru wato Kakan su Madina tsohon Alkalin Alkalai ne na jihar Kano kuma fitaccen mutum akan sha’anin shari’ah a Kano. Tun a tsakiyar shekarun 80’s Attahiru Habibu Sorondinki ya tafi Jeddah kan wani kwas na aikin Banki, tare da matar sa Hajjah Ramlah da manyan ‘ya’yan sa maza uku a lokacin, Abubakar da Omar, da Osman inda daga wancan lokacin ya fara aiki da wani tsohon bankin kasar ta Saudi-Arabia. Da tafiya tayi tafiya, zamani na garawa da shi a harkar aikin banki a can, har zuwa lokacin da aka bude ISDB wato (Islamic Development Bank) Allah kuma ya zabe shi ya kai shi ISDB a babbar ‘headquater’ din su dake birnin Jeddah. Ya rike kananan mukamai da dama a cikin ta, kafin ya iso wannan matakin na yanzu. Domin kuwa a halin yanzu mahaifin na Madinah Alhaji Dr. Attahiru Soron Dinki yana rike da matsayin (Chief Financial Officer) na ISDB. Alh. Attahiru na auren Hajjah Ramlah, wadda ta kasance ‘cousin’ a gare shi, ta cika masa gida da kyawawan ‘ya’ya maza har su hudu, Abubakar, Omar, Osman da Aliyu, a Kano ta haifi manyan su uku, wato Abubakar, Omar da Osman. Da suka zo Jeddah ba jimawa ta haifi Madinah da Aliyu anan. Akwai ratar haihuwa sosai tsakaninta da Osman kafin su samu haihuwar auta “Madinah”. Daga Abubakar har Umar har Aliyu da Usman ma’aikatan bankuna ne a kasar Saudi-Arabia, saboda mahaifin su dake da wuka da nama a harkar aikin banki. An haifi Madinah ne a garin Madinatul-Munawwarah lokacin sun je aikin omrah duk gidan, shi yasa Baban ta ya kira ta da suna Madinah. Madinah ta ga gata tun daga haihuwar ta har girman ta, Madinah bata taba sanin wahala ko babu a rayuwar ta ba, ta tashi a gida na ilmi da tarin dukiya, wanda ya sa koda ta shiga jami’a maza ke rububin ta, da yawa ko don su rabi alfarmar ISDB, da yawa kuma saboda kyawun ta ne. Amma wani ikon Allah babu wanda tasu ta zo daya irin coursemate dinta Sarham Abbas Shanono, wani siririn sardidin yaro, dan ajinsu, wanda ta fahimci yafi kowa a ajin su kokari, kamun kai da kula da abinda ya kawo shi, shima kuma ya fahimci Madinah Attahiru tafi duk matan ajin su kokari, ga aji ga kasaita kamar wadda ta hada jini da sarauta, amma shi bata yi masa ko daya sai ma wani ‘special respect’ da take bashi, sai suka hade daga haka, suka zama abokan karatun juna, daga abotar karatu da karawa juna sani abin nasu ya fara, kafin ba da jimawa ba ya rikide zuwa zazzafar soyayyah wadda ta isa a bada labarin ta a ko’ina, amma irin soyayyar nan ta sa’annin juna. Wadda bata fiya ‘actualizing’ ba. Domin kuwa shekaru uku kacal Sarham ya baiwa Madinah Attahiru. Duk da kasancewar Madinah irin mutanen nan da basa so ka shiga harkarsu, masu halin da kai tsaye za’a ce na nasara ne kamar ba tashin Saudi Arabia ba, amma duk da wannan hali nata bata da wulakanci da raina mutane. Personality dinta kawai za’a ce na nasara ne (musulma mai halin nasara), tanada wani zazzafan hali na kada ka sake ka shiga harkar ta, itama kuma bata shiga harkar kowa, saboda mugun jan ajin ta, ta kasance mace ‘yar I don’t care attitude. A hali iri na Madinah ko kai waye wajen isa, ko wane irin laifi kayi mata, ko wane irin aibu kake da shi, Madinah bazata zauna tana gulmar ka da wani ba, tafi karfin haka, saboda she is frank, bata iya boye me take ji akan mutum, zata tare ka ne gaba da gaba ta gaya maka, da dai ta zauna tana zunden ka da wani. Wato dai a takaice Madinah bata iya munafurci ba, sannan bata so a yi mata. Wadannan halaye nata sun taimaka kwarai wajen ribato zuciyar kyakkyawan Bakanon matashin Sarham Shanono a kan ta, babban jigon son da ya samu kan sa da yi mata shine yadda gatan data ke da shi bai hanata tsayawa tsayin daka wajen yin karatun da zai amfani al’umma ba. Sarham Abbas da Madinah Attahiru duk abokanan karatun su na MBBS sun san su tare, ko’ina tare suke zuwa, soyayyarsu mai tsafta, mai ban sha’awa ta ‘yan bokon da, ba irin ta wannan gurbataccen zamanin ba, Madinah kullum kawo ta ake a kuma zo a dauketa a motar gidan su, shikuwa a nan kusa da makaranta ya kama hayar gida mai daki biyu (flat). Sun tsayar cewa da zarar sun yi bikin kammala karatu zasu yi aure, Madinah ta yarda zata bi Sarham Najeriya ta zauna cikin iyayen sa da kannen sa duk da cewa itada kasar Kano sai da ziyarar dangin su kawai su kan shigo ta, ita dinma sai suyi shekara

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});