Chapter 1
Chapter 1
‘YAR CIKIN BADALA (HAUWA-KULU) 2 SUMAYYAH ABDULKADIR HAUWA-KULU-2 Mota na tsayawa agaban su ta ce masa “Kurna”. Ba don ta san kowa a Kurnan ba, sai don ta san tayi nisa dai da cikin gari, ta tafi can wajen fita garin Kano, shi kuma mai mota ya ce naira biyar, duk da Inna ta san zuka musu kudin yayi don ya gansu hajaran majaran amma bata ko nemi ragi ba, ta kama hannun Hauwa suka shige da katon bakkon kayan su. Aka zo Kurna, sai ta rasa inda zata ce ya sauke su, shi kuma ya gaji da yawo dasu a Kurna sai yace ko tasha zan kai ku in gari zaku bari? Inna ta samu kanta da cewa “eh”, sai ya kai su tsohuwar tashar nan wato Tashar Kuka ya ajiye su. Inna ta kama hannun Hauwa duk sun yi wujiga-wujiga da gajiya da yunwa, suka je rumfar wani mai shayi, a daidai lokacin hantsi ya dubi ludayi, ta zaunar da Hauwa a bencin da babu kowa, mai shayi ya zo wajen su yace “Iya lafiya? Ba’a bara a kan benci na, na sana’a ne”. Hauwa ta fiddo manyan idanun ta tana sama tana kasa da su, wai dai ya san hararar sa take yi, don ba abinda ta tsana a ambata mata irin a dangantata da kalmar “BARA” don tana makauniya mara ido, ba don Inna ta koyar da ita kyakkyawar tarbiyyar rashin saka baki a maganar manya ba, da ta zage shi, mai shayi ya ce, “bayin Allah ku kara gaba don Allah, kada ku kashe min kasuwa da wannan daurin bakkon naku duk warin tsummokara”. Inna ta daure ta ce “don Allah zuba mata shayin ta sha, zan biya ka, nawa ne kofi daya? Ka yanka mata biredi”. Nan ne Hauwa ta kasa daurewa, ta ce “Inna ko wannnan shi ya saura shayi a duniya, ko yunwa zata kashe ni, ba zan sha ba, tun da ya ce mana mabarata” ta fashe da kuka, sannan ta mike tana laluba bakkon su, ta dauka ta dora akan ta, Inna ta mike ta kama hannun ta suka tafi, yana cewa “Umma ta gaida ashsha, dama makafi akwai fadin rai, da zuciyar tsiya kamar kutare, ni bana son harkar mabarata da nakasassu”. Inna ta hango rumfar wata mata mai saida abinci, ba yawan mutane a wajen, sai ta ja Hauwa suka nufi wajen, matar tana ta kai kawo da masu sayen abinci uku dake kan tebur, da ganin ta ka ga ‘yar Kano-Jeddah, Inna tayi mata sallama, da mutuntawa ta amsa ta ce “Iya sannu ko? Abinci zaku saya?” Inna tace “eh, zuba mata ta ci ta koshi kisa mata yankan nama, nawa ne kwanon shinkafa da miya?” Matar ta ce “naira bakwai”, haka ta zuba ma Hauwa abinci mai rai da motsi ta shigar da ita rumfar da babu mutane sosai ta bata ruwa ta wanke hannu. Inna tana zaune tana sakawa da kwancewa, ko yunwar ita bata ji saboda duhun zuciya da bakin cikin abinda Zakari yayi musu. Tana matukar son gidan ta, duk wani tarihin ta da mijin ta da ‘ya’yan ta, duk wata dabdalar gidan aure, dama jin dadin rayuwar ta ya ta’allaka ne a cikin gidan nan na bayan BADALA. Amma ace yau rana daya….??? Ta sa gefen zaninta ta share hawaye tayi sharbe, wanda Hauwa ta ji shi. Tadago gululun manyan idanun ta zuwa sashen da taji sharben Inna “Inna ke bazaki ci ba ke?” “Ci Kulu ki rabu da ni kinji, ba zan iya kai ko ruwa baki na ba yau”. Sai itama ta tsame hannunta, ta koma jikin bangon wurin ta jingina itama, kamar yadda Inna tayi, ta hade jikin ta cikin hannayenta ta takure kai a cikin kafafunta, ta ce “to shikenan nima ba zan ci ba, tunda kema Inna ba zaki ci ba”. Inna ta ce “Kulu yunwar ce bana ji sam”. Hauwa ta ce “na san bacin rai ya hana ki ci, amma abu daya nake so ki tuna Inna, idan Kawu Zakari ya rushe gidan mu, ya kwace ta karfin tsiya saboda iya zaluncinsa ai Allah ba azzalumin bawanSa bane, kuma baya yafe hakkin wanda aka zalunta. Ba kuma zan gushe a cikin sujjadar salloli na biyar na farillah ba face ina mai kai karar sa wurin Ubangiji. Inna ki manta da Baba Zakari, mu fuskanci wadda zata fishshe mu. Son samu Inna mu fara sana’ar abinci muma a tashar nan, tunda na lura akwai kudi a jikin ki”. Inna ta ce “eh da kudi, wadanda yaronnan Jamilu ya bani kan ya tafi, amma Hauwa ai baka fara sana’a farat daya baka zauna a wajen ka fuskanci yanayin wajen dana mutanen wajen ba, da irin zaman da ake yi a wajen, dabi’un su da yanayin mu’amalar su. Ta yaya zamu zauna a Tasha bayan matattara ce ta rashin arziki ga ‘ya’ya mata? Ki dai bari mu kara gaba, in ya so ko a masallaci sai mu dinga kwana”. Duk hirar nan da suke yi a kunnen Hajiya Ladi mai abinci, tana kirga kudin cinikin ta tana sauraron su da kunne daya, don ta gama da girkin safe, zata fidda riba ta dora na rana. Ta ji tausayin Inna ta kuma ji Hauwa ta burge ta, wadannan idanu na ta da alama basa gani, amma duk da haka zuciyar ta bata mutu ba, ba ta ce tunda gasu a tasha su yi bara ba, don ita makauniya ce zata zamewa uwarta hajar samu, gata budurwa son kowa, sai ma cewa uwarta take su kama sana’a. Hajiya Ladi ta matso inda suke ta zauna, tace “naji duk abinda kuka tattauna a junan ku, duk da ban san daga inda kuke ba zan baku masauki a gidan da nake zaune, in kuma dinga baku aikin abinci kuna taimaka min, sai mu dinga zuwa nan tare kullum in mun sayar mu koma gida tare, ni kuma zan dinga baku abinci sau uku a rana. Ban yi karyar biyan ku ko sisi ba, abincin da zaku dinga ci da wajen kwanan da zan baku shine ladan aikinku, in ya so in kika gane yadda ake sayar da abinci a nan tashar kina iya kafa naki tebirin daga baya. Baiwar Allah muma da Allah ya rubuta mana samun na abinci a Tasha, ba zabin mu bane ba, da gaske akwai bata gari, kuma matattara aikin ashsha kala-kala, amma yaya zakayi da abinda Allah ya rubuta cewa anan samunka yake?”. Inna da Hauwa suka hau godiya ga Hajiya Ladi mai abinci, kuma tun daga ranar ta basu daki guda a gidan ta wanda ke nan unguwar Rijiyar Lemo, ta kwashe shirgi tace su dinga kwanciya a dakin. Amma da wuri zasu ke tashi su tafi tasha a dora mata abincin safe, zuwa karfe hudu sun saida na rana sais u dawo gidanta tare. Ta koyawa Inna kalolin irin girke-girken da take yi, ga mamakin ta sai ta samu Innar Hauwa kwararriya ce a fannin girki har ta fita kwarewa. Gata da tsaftar jiki data muhalli, tuni ta kara rike Inna da kyau. Tun daga ranar suka soma yi wa Haj Ladi aiki, Hauwa ma ba’a barta bata aikin komai ba, ita ke wanke wanke na kwanukan da aka bata, tsaf take wanke su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36