Chapter 24
Chapter 24
roke ki da Allah da Manzon sa ki raka ni gidan nata yanzunnan”. Numfashin sa har gwamuwa yake tsabar yadda ya saka Innar da son ganin su a ransa, dama tace watakila bazasu kara ganawa ba, watakila sallamar su kenan, Allah ya gani yayi duk iya kokarin sa a kan ya san halin da suke ciki a wancan zuwan nasa Allah bai yi sun hadu ba. Matar ta sallami kwastomomi sannan ta baiwa ‘yammatan sallahun abinda zasu yi mata kan ta dawo, daga nan ta bi bayan Sarham da Malam Isa zuwa mota. Suna tafe tana basu labarin ai Innar Hauwa ta dade a kwance, watakila tayi shekara tana jinya, shagon ma yanzu ya zama nata. Don dama haya muke kamawa, a da ina mata aiki ne da ta kwanta ta bar sana’ar sai nikuma na kama rumfar hayar, ba don ‘yar ta makauniyar nan mai kokari ba da tuni Innar Hauwa babu, da tuni ta kashe kanta da ciwo a gida, don bata son maganin asibiti. Sarham ko magana ya kasa, yana jin ta ita da Malam Isa suna ta maganar kin asibiti irin na Innar Hauwa, yace ai tun sanin da yayi mata a haka take da akidarta ta amanna da maganin gargajiya. Malam Isa yace “kuma fa akan kin asibiti ne har idon Hauwa ya mutu da hakiya, ni nan ba yadda ban yi da ita ba akan ta kai ta asibiti tun yana apolon sa, sai da ta ga ‘yar ta gama makancewa sannan ta kaita, a lokacin aka ce ido ya mutu, yadda suka je haka suka dawo. Matar na nunawa Sarham hanya har suka isa wani dan mitsitsin gida a wata unguwa can ciki, kamar duk rabin unguwar kwatami ne, kasancewar unguwa ce ta masu karamin karfi sosai. Amma gidan nata sai suka same shi a kulle. Sarham kamar ya dora hannu aka yayi kuka, don matuka ya saka ran sa da ganin Innar Hauwa da Hauwa a yau ba sai gobe ba, koma musu yayi kamar sabon kamun hauka, don cewa yayi da matar ba inda zai bari ta je sai ta hada shi da Innar Hauwa, ta ce itafa bata san gidan mai maganin da aka kaita ba, sai yace to su kai shi gun makwabcin nata da ya kai ta Albasu ne koma ina ne, in ba haka ba itada makwabcin na Inna zai yi karar su ga hukuma kan cewa sun batar da bayin Allah. “Yau nake ganin abun da ya gagari Kakata” in ji Tafada mai Tuwo, daga abun arziki zaka daura min jakar tsaba kaji su bi ni, ni fa tsakanina da Innar Hauwa mutunci ne kawai, Allah ya gani ko a kwanciyar nan da tayi sau biyu ina taya Hauwa kinkimar ta ta kai ta asibitin Kuroda amma bata yarda ta kwana, yadda kake tunanin mu muka batar da su, to akan me? Daga zaman amana???” Malam Isa ya lallashi Tafada yace, “kada ki damu ba kya ganin a fusace yake? Ina ne gidan makwabcin nasu?” Ta nuna gidan dake jikin na Innar. Aka yiwa makwabcin su Inna sallama ta hanyar tura yaro cikin gidan sai gashi ya fito, suka gaggaisa da Malam Isa yace “Tafada ya akayi? Tace ga masu neman makociyarka nan, har suna neman kala mana sharri wai mun batar da ita”. Malam Sani Albasu yayi dariya yace, “Innar Hauwa mai jama’a, ho! Tana can kauyen mu gidan Malam Bagobiri mai maganin gargajiya na Albasu, in kuka je Albasu duk wanda kuka tambaya gidan Malam Bagobiri ya sani, ko daga tashar Albasu ne kukayi tambaya za’a kai ku har gidan sa”. Sarham yace “me zai hana ka daure ka rakamu kawai, ina ganin zaifi sauki, tunda kai ka kai ta? Malam Sanin ya yarda zai rakasu har Albasu, Amma yace saidai su dawo gobe yanzu yamma tayi. Sarham, Wanda hakurin sa ya tuke a lokacin sai yace da Malam Isa su je kawai su yi tambayar har su samu gidan. Malam Isa ya yarda don yaga damuwar sa karara, ya yarda cewa wannan bawan Allah Sarham, da gaske ya damu da Innar Hauwa Allah kadai ya san tsakanin su. Musamman filin gidan su da ya saye dinnan ya hau ginewa, duk da bai yi masa wani bayani ba ya fahimci yana da niyyar sake mayar musu da gidan su ne. Wanda baya ko tantama kulafucin ta da gidan, da unguwar bakidaya, da mutanen ta na arziki da aka raba ta dasu rana daya, sannan da makancewar tilon diyar ta rana daya, da kuma damuwar batan mijin ta Malam Bilyaminu dare daya, su suka taru suka haifar mata da kamuwa da ciwon zuciyar da ake cewa tana fama da shi a yanzu. Malam Isa ya tuna Innar Hauwa yanzu mijin ta ya fi Shekara biyar da bata, me zai hana ta yarda tayi GAIBA in ya so shi ya aure ta ya rike mata 'yar ta guda daya ya killace su a gidan sa su daina rayuwar sayarda abinci a Tasha? Shi kadai yake wannan tunanin na babu gaira babu dalili har suka isa Albasu. Malam Isa ya tafi tunani bai san har sun shiga garin Albasu ba, sai da Sarham yayi masa magana yace “gamu cikin Albasu” suka tsayar da motar a gefen titi Malam Isa ya tambayi wani mai Amalanke ko ina ne gidan Malam Bagobiri mai maganin gargajiya?” Mai Amalanke yace “kun baro gida can farkon shigowa gari, ku koma da baya ku tambaya” Sarham yace “in dai ka san gidan shigo ka kai mu, zan baka kudin Babur ka dawo”. Hakan kuwa aka yi, mai amalanke ya shiga bayan motar yana nuna musu hanya har kofar gidan malamin. Wato abun babu kyawun gani, Yaa Subhanallah! Marassa lafiya ne rututu a zube a kasa tun daga zaure, cutututuka iri daban daban masu tasa tsigar jiki. Sarham sai da ya dauke numfashin sa na lokaci mai tsaho sabida kazantar gidan da cunkoson marassa lafiya. Tausayi da haushin Inna ya kama shi, wato har yanzu tana nan da halin ta na rashin yarda da asibiti kamar bai isa ace ta dau darasi tun akan Hauwa ba? Ganin cewa jinin sa na neman hawa, sai ya umarci Malam Isa ya yi musu sallama da malamin, aka ce ai sai sun hau dogon layin ganin sa yanzu kuma dare yayi, saidai su dawo gobe da safe. Malam Isa yace da Tafada “shiga kawai ki fito mana dasu, ya gansu hankalinsa ya kwanta, don ni kam ban iya kwana garin nan”. Tafada ta shiga gidan da sallama, wani ikon Allah da Hauwa ta fara tozali, wadda ke bakin kofar dakin da Inna ke kwance, Hauwan kuma nan da nan ta dauki muryar ta, ta kira sunan ta da ‘yar dusassar murya. “Tafada, kamar muryar Tafada nake ji”. Tafada ta isa ga Hauwa da sauri, wadda tayi kozai kozai tayi zuru-zuru, rabon ta da wanka yau kwana bakwai, wato tun kawo su da Malam Sani yayi kauyen nan ya tafi, ya kuma karbe duk ‘yan kudaden hannun su da sunan yana biyan mai magani, amma kullum jiya I yau, babu wani sauki a tare da Inna sai na Allah. Yau kam wuni tayi tana suma babu wanda ya tsaya a kanta sai Hauwar da ba gani take ba,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36