Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a gabana, in kula da ita, tayi ta karatu, duk da ni ma ba karatun nayi ba, amma alhamdulillahi ni lafiya ta kalau, zan rayu ko ba ilmin zamani ba tare da na zamewa kowa labiliti ba. Amma Hauwa fa? Ai duk wanda na bawa auren ta na kware shi, domin na hada shi da aiki da jidali. Itama kuma na sayo mata rashin kwanciyar hankali. Don haka maganin kada a ji, kada a soma. Gashi bani da matallafi namiji wanda zai tsayawa Hauwa ta samu ta yi karatun nan tunda ni bansan kansa ba, da wannan yau nake baka amanar Hauwa-Kulu Sarhamu, ina mai baka amanar ta don na amince maka, na kuma amince bat un yau kaunar ka damu ta saboda Allah ce. Don Allah likita ka taimaka min, wajen cikar burika na a kanta, na tayi karatu mai zurfi wanda zai amfani al’umma ya kuma amfane ta duk da nakasar ta. Bana so nakasar nan tata ta zame mata rauni, so nake nakasarta ta zama ado a gareta. Inna ta soma sharar hawaye ta ce “gashi Bilyaminu ban san inda yake ba, bansan a halin da yake ciki ba, yana mace ne ko yana raye Allah masani, na tabbata da ace yana tare da mu, shima burin sa zai zama irin nawa ne akan Hauwa, don a komai muna kasancewa da ra’ayi daya ni da shi. Allah ya gani bazan iya baiwa Jamilu auren ta ba duk da na san a shirye yake da ya tsayawa Hauwa, ba don komai ba sai don ubansa, amma ba don yayi min wani abu ba, ko bai cancanta a bashi aure ba. Ko Hauwa-Kulu zata tsufa ba aure, tana nan a kwibi na, (a kusa da ni) ba inda zata da sunan aure”. Hauwa daga dakin ta duk tana jiyo abunda Inna ke fadi akan ta, sai ta samu kanta da dimaucewa, don fisabililahi ko ba’a fada ba ta san zuciyarta ta amince da Yaya Jamilu dari bisa dari, yau ga Inna na cewa a dakin ta zata tsufa. Ya Allah! Itafa mantawa take da makantar nan tata, idan har ba bude littafi da zummar yin karatu taga duhu didim tayi ba, mantawa take bata da ido, saboda rayuwar ta cike take da baiwarwaki da kuma alfarmomin Ubangiji masu yawa da wadatar zuci. Ji take babu wani abu da mai lafiya yake yi a rayuwar duniya wanda bazata iya ba, musamman aure da hayayyafa. Inna da Sarham sun jima suna hira, yana zaune dirshan a gabanta. Inna nata kashe zuciyar Sarham da kalamanta masu nuna hakikanin MOTHERHOOD a kan diyarta Hauwa-Kulu, yau ya fahimci ba karamin so Inna take yi wa Hauwa ba. Ya ci tuwon da Inna tayi kafin ya tafi wanda tuwon masara ne miyar yakuwa, ta zuba masa soyayyen manshanu a ciki da yankan naman rago biyu. Ta kuma hada masa lamurje/zobo mai sanyi wanda tasa a firjin Hauwa yayi sanyi. Dr. Sarham tunda ya bar gidan su Hauwa ba tareda yau ma ya iya tsayawa a kofar dakinta yadda ya saba ya yiwa Hauwa sallama ba, kasa shiga Sorondinki yayi yau, saboda halin da ya samu zuciyar sa a ciki a kan maganganun da suka yi yau shi da Inna heart-to-heart, ta gama fede masa zahirin abinda ke karkashin zuciyar ta akan miskiniyar diyar ta, HAUWA-KULU, wanda dan cikin ta kadai zata iya gayamawa, amma shi yau ta zaunar dashi ta gaya masa duk wani abu dake karkashin zuciyarta a kan future dinta bisa radadin da take ji na nakasar diyarta. Kai tsaye ta bayan gidan ya wuce ya lallaba ya shige dakinsa, ba tareda kowa ya san da dawowar sa ba. Sarham ya kulle kansa don kada Sumayyah ta zo ta dame shi da dumi, dama kuma Inna ta ciko masa cikinsa taf da abincin ta, don haka baya bukatar karin cin abincin Mama yau. Ya kwanta a ranar a tsakiyar gadon sa yana tunanin maganganun Inna, ya kuma debo na kanwarsa Sumayyah na rannan ya kara akan su, wato yayi addition, yana tarawa yana debewa, tsakanin maganganun Inna da maganganun Sumayyah…. Sumayyah ta ce “Hauwa mutum ce kamar kowanne dan adam, tana da right din yin aure da bukatar yin sa kamar kowa ‘in spite of her disability’, Uwarta kuma ta ce ko zata tsufa a gida bazata bata wannna damar ba. Ba don komai ba sai don tana guje mata wulakanci da tozarci a dalilin nakasar da shi Sarham yayi mata lasisin ta. Bayan kuma addini da al’ada da ‘yancin dan adamtaka duka sun bata damar yin aure. Shin tsakanain Inna da Sumayyah, waye mai gaskiya akan future din HAUWA-KULU??? A take kaso mafi rinjaye na zuciyar Sarham ya ce “Sumayyah ce mai gaskiya!!! Ita Inna ba wai bata so Hauwa tayi aure bane a’ah, gudun kada a wulakanta mata ita ne da sunan aure, da guje mata tozarci da dawainiyar aure da take da tabbacin bazata iya ba sabida rashin ido, yasa ta gwammace tayi ta ajiyar ta a daki. Wato abinda ka san bazaka samu ba hada shi da bana so! Amma ita Hauwa din tunda har take kula Jamilu, to ya tabbata tana son tayi auren kenan ko bata furta ba. Don Inna ta gaya masa yadda Hauwa ke sakewa da Jamilu ita kanta abin yana bata mamaki matuka. Sai ya samu kansa da tambayar kan sa to KO DAI HAUWA SON AUREN JAMILU TAKE YI? Sarham sai yaji ran sa yayi wani iri mummunan baci, a take wani tunani ya bijiro masa, me zai hana shi Sarham din ya aure Hauwa kowa ya huta (ko da baya son ta so irin na soyayyah irin wanda yake yi wa matarsa Madinah, don shi kadai ne solution ga rayuwar ta (shi Sarham din), da zamowa maslaha ga mahaifiyar ta, hakan zai fi alkhairi fiye da auren Jamilu ko wanin sa ga Hauwa. Tunda maganar Hauwa ta dauwama ba aure ba dabara bace so-karbau, a matsayin ta na ‘yar adam mai cikar lafiya da ‘sexual hormones’ kamar kowa dole tana bukatar yin aure. A take Sarham ya shiga gayawa kansa; zai auri HAUWA-KULU domin wasu dalilai masu tarin yawa da ya dade yana dambarwa da zuciyar sa a kansu, amma ba don kalmar SO ta gitta ko zata gitta nan gaba a tsakaninsu ba. SO guda daya ne a zuciyar sa; kuma na matar sa MADINAH uwar Hauwa-Waheedah ne. Zai auri HAUWA ne a dalilin ya san ta kullace shi, akan-karan kan sa kuma yana son kankare wannan kullacin nasa dake kasan zuciyarta, har gobe ya kasa yafewa kansa zama sanadin makantar ta. Babu kuma ta hanyar da zai iya kankare wannan tabon nasa daga ran Hauwa in ba ta sanadin aure da hayayyafa ba. Zai kuma yi amfani da kwarewar sa ta yanzu, wajen ganin ganin ta ya dawo, koda ba duka ba, da iznin Ubangiji. A karshe ya gayawa kansa zai auri HAUWA domin yana tausayin Inna, kuma yana kaunar ta, don haka zai karbi amanar nan data bashi ne ta hanyar AURE wanda ta hanyar sa ne kadai zai iya cika mata burin ta, na kular mata da ilmin Hauwa da rayuwarta gabadaya, zai yi kokari wajen cikawa Inna burikan ta a kan HAUWA-KULU ne kadai idan ya samu

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});