Chapter 18
Chapter 18
ya karu nesa ba kusa ba akan sanin da yayi musu, sosai ya jinjinawa Malam Isa da iya kiwon dabbobi da zuciyar makwabtaka irin ta mutanen da, ya kuma yanke shawarar taimaka masa akan kiwon dabbobin shima daga ranar da kudin abincin su. Malam Isa yana ta murnar mallakar waya, saboda a lokacin bata zama a hannun talakawa, ya sakawa Sarham albarka yafi cikin carbi. Da zasu rabu kuma Sarham ya gaya masa niyyar sa, wato yana so ya gine filin nan, so yake ya a gina musu gida kwatankwacin nasu a filin su, gini na zamani, ya ce shi ba mazauni bane don haka zai turo magina kuma zai bar komai a hannun sa da masu ginin, yana so Malam Isa ya kula da ginin har a gama, don zai jima bai dawo Kano ba. Malam Isa yana ta mamaki, ko meye alaqar wannan matashin mai kirki da kyakkyawar zuciya da su Innar Hauwa haka, haka suka yi sallama bayan Sarham yayi masa kyautar kudi, kuma a washegari aka saka tubulin harsashin ginin gidan su Inna da kudin da jima yana Tarawa don yin nasa ginin gidan. Kwana uku bayan nan, ba abinda Sarham yake yi sai yawo a cikin garin Kano yana faman neman INNA da HAUWA har tambaya yake yi ko an san su, ya fasalta kamannin su, maimakon ya maida hankali wajen shirin taryar amaryar sa Madinah-Munawwarah mai isowa daga Jiddahn Saudi Arabia. Amma ko wanda yace ya san mai kama da su bai samu ba. Wannan yasa duk zaman garin Kanon da dokin amarcin dake gaban sa ya kara fita a ran sa. Ya sa a ransa da Madinah ta zo bazasu dade ba kamar yadda yayi niyya zasu koma Jeddah, in yaso ya karbi tayin aikin da aibitin “SAUDI-GERMAN” suka yi masa, wanda a baya yaki karba, don ya so ne ya dawo gida kwata-kwata ya cigaba da aikin gwamnati a manyan asibitocin Kano da ya tabbatar sun fi bukatar sa, in yaso ya bude private clinic nasa na kansa ya hada, amma a yanzu bai san haka zuciyar sa ta dauki su Inna da matukar muhimmanci ba sai yau da take gaya masa rashin su ba zai sa ya ji dadin zaman Kanon bakidayanta ba, duk da gatan iyaye dana ‘yan uwa dake baibaye da shi, ga na cikar buri, wato na mallakar Madinah abar son sa. Amma duka ya kasa enjoying ko daya. Saboda wasu bare? Ya ilahi, wane irin abune haka??? Shi kansa yana mamakin karfin ‘bond’ din dake tsakanin sa da ‘Inna’ don bazai ce ‘Hauwa’ ba. Don haka sai mu ce Amarya Madinah ta shigo kasar Nigeria da kafar hagu, don kuwa likitan zuciyarta Sarhamu babu walwala kota kwabo a tare da shi, gabadaya ya birkice da neman Inna da Hauwa, har iyayen sa suka fara damuwa da saka ayar tambaya, suka zaunar da shi suka ce ya gaya musu gaskiya, bayan tausayi da taimako, meye alakar sa da mutanen nan ne? Ta yaya zai yi sabon aure amma ya raba hankalin sa da nutsuwar sa, ai sai suma ya saka su a damuwa. Sarham ya ce babu wata alaqa tsakanin sa da su, sai kauna ta fisabilillahi da haduwar jini, yace shi kawai yana tunanin a wane hali suke ciki ne, yana tsoron fadawar su mugun hannu ko fadawa hannun kanin uban Hauwa wanda baya kaunarsu kuma azzalumi ne, sannan basu da kowa da zasu kira nau in ba shi din ba (Zakari). Mama tayi fuska ta ce daga yau bana son ka kara fita neman su tunda dai ba kananan yara bane, Allah shi yake kula da bayinSa marassa karfi da masu karfi, kafin ka shiga rayuwar su ai babu uban nasu, kuma hakan bai hana su rayuwa mai kyau da shaker numfashi ba. Saidai ban sani ba ko kana da wani dalilin a kasan ran ka a kansu bayan wannan?” Wai meyasa mutane suke kasa fahimtar sa ne akan Hauwa da Innarta? Zai iya rantuwa babu wani dalili a kasan ransa a kansu bayan wanda ya fada musu. Kwatakwata kenan babu alaqa ta mutunci da zumunci a tsakanin al’ummar Annabi sai mai kunshe da MANUFA? Haka mafa Sumayyah ta taba cewa wai….. abun babu ko dadin ji domin kuwa yadda yake kallon ta muharramar sa haka yake kallon HAUWA-KULU. Can tsakar kansa ya tsinkayi sautin Abba yana cewa “talakawa nawa ne a Nigeria da suke cikin halin kaka-nikayi? In ka ce duka sai ka tsayawa rayuwarsu ka hada kan ka da abinda ba zai taba yiwuwa ba, tunda dai kayi taimako iya yinka wanda dace ya kamata ka bar su a hannun Ubangijin da ya halicce su haka, ka maida hankali ga abinda ke gaban ka yanzu. Wato sabuwar rayuwar ka ta girma da yah au kanka”. **** **** **** THE ARABIAN BRIDE M adinah na gidan kakannin ta bayan saukarsu a Kano, a daren ranar za’a kawo ta wajen Mama, an gyara dakin Sumayyah da kyau wato inda za’a sauke ta da ‘yan uwanta. Gidan ya dauki kamshin turaren wuta dan Maiduguri ko ta ina mai dadin kamshi, Mama da kawayen ta su Barr. Hannatu Mahdi da ’yan uwanta suka shirya karbar amarya da danginta. Har falon Mama aka shigar da Madinah-Munawwarah cikin lullubi, kafin a yi addu’a ta musamman ‘yan rakiyar amarya da ‘yan karbar amarya duk suka watse, gidan ya rage sai mutanen gidan kadai. Rana ta farko dasu Mama suka ga fuskar Madinan Sarham. So beautiful da ita, karshen gayu karshen class, Masha Allah. Mama ta ce a ranta dole kam Sarhamunta ya kamu ya tsunduma iya wuya, Madinah ko daga cikin lullubi kafin a ganta a zahiri an san matar manya ce kuma ‘yar manya ce. Tayi fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a mai alkbarka. Ya kade fitina, ya basu ikon sauke amanarta da aka damka musu. Yau Madinah ta samu kanta a gidan surukan ta wato iyayen Sarham suna ta haba-haba da ita. Sumayyah da Surayyah ma ba’a bar su a baya ba wajen kula da bakuwar tasu, Surayyah kuwa duk da ‘yar tsamar dake tsakanin ta da Sarham sai da ta kasa shiru, da ya shigo gaida Mama bayan ya dawo gidan da daddare sosai tace dashi. “Yaya Doctor, wallahi ka iya zabo mata, class iya class malam, kyau iya kyau, dubi mata kamar hurul- eeni, kamar ita tayi kanta don kyau da gayu. Wata mummunar harara Sarham ya zabga mata yace “ki fita idona in rufe, ki bar shiga harkata, na rantse Mama ki raba ni da Surayyah”. Sannan ya gaida Mama da gajiyar hidimar jama’a, wadda keta dariyar masifarsa, Mama tace “ban taba ji ko ganin ango yana masifa ba, duk wani ango far’a yake yi da farin ciki banda kai, tashi ka shiga dakin Sumayyah Madinah din tana can”, cikin jin nauyin Mama irin wanda bai taba ji ba a rayuwarsa yace, “Mama ki barta, sai da safe in Allah ya kaimu zamu gaisa in sha Allah, a barta ta huta, na san ta gaji, gata bata jure hayaniya”. Nan kuwa kunyar idon Mama ya hana shi zuwa yiwa Madinah barka da sauka cikin rayuwarsa. Sai da ya koma dakin sa yayi shirin kwanciya sannan ya kirata a waya, Madinah ta fito wanka kenan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36