Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dace ta bi shi har gidan sa ba, kai baima dace ba mace kamar ta ta dinga bin namiji komai tinkahon sa yana yarfata irin haka, balle ita Madinah Attahiru, da bayan aji har ajujuwa gare ta. Amma haka ta take PRIDE din nata, da kafarta ta taka zuwa gidan da ta san acan yake da zama, bata da tabbacin har yanzu acan din yake, ko kuma ya canza gida, amma dai tace bari ta fara duba can din ko zata dace. Ubangiji da kan sa yace “SULHU ALKHAIRI NE!” To gata ta zo neman sulhun abin kaunar ta yau da kafafunta, kamar yadda tasan tana cin alfarmar sunan ta kullum a wurin sa, haka yau ma take da wannan kyakkyawan fatan, tana da yaqinin wannan karon ma zata ci wannan alfarmar daga gareshi, wadda tafi ta koyaushe girma a wurin sa, wato ya sauke fushinsa ya tsaya ya saurareta ko na minti biyu ne albarkacin sunanta da yake girmamawa na MADINATUL MUNAWWARAH… Madinah garin Manzo, Madinah mafaka ga dukkan musulmi, duk da tabbas ta san an bata masa, kuma laifi kan laifi ta san ta yi masa. Ko tace sun taru sun yi masa itada Daddy dinta. Ilai kuwa tana tura karamin gate din ta hange shi daga can saman bene, tsaye a jikin balcony, ya harde hannayen sa a kirjin sa ya juya bayan sa daga kofar shigowa, don haka bai ga shigowar ta ba, da alama yayi zurfi a cikin tunani. Madinah tana tura kofar cikin sa’a ta taddata a bude, don haka kai tsaye ta sa kai, ta kuma haura ta matattakalar benen ta cimmasa har inda yake. Kamar cikin mafarki, kamar kuma irin gizon da ta saba yi masa cikin ido biyu, haka ya ga Madinah Attahiru tsaye a gaban sa, (for the second phase) na rayuwar su. Tana sanye da shudiyar abaya kirar Dubai da mayafin ta, ya sha mamakin biyoshin data yi, a irin sanin da yayi mata wajen tsare mutuncin ta da tsare ajin ta, wato tun saninsa da ita… maintaining self-esteem dinta yana sama da komai a gareta, a kuma irin yarfawar da yayi mata dazunnan. Wadannan, dama wasu dalilan, su suka sa ya kasa wofintar da ita, ko bar mata wajen kamar yadda yayi niyya da farko. Musamman ganin kyawawan idanun ta sun cika taf da kwallah, gab suke da ballewa bisa sassalkan kundukukinta, tace cikin rishin kuka. “Yau ma in ci albarkar garin MADINAH……Madinah garin Manzo, in ci albarkar kasancewa ta MADINAH AL-MUNAWWARAH, mafaka ga kuncin dukkan musulmi, a lokacin da suka shiga cikin matsin mushrikai, da abokan gaba, suke neman inda zasu samu tsaro da kwanciyar hankali, Madinah ta zamo mafaka ga Manzonmu (SAW), don haka nake rokon albarkacin ta ka saurare ni, ka bani mafaka daga kuncin zuciyar dana ke ciki a cikin kirjina”. Bai ce komai ba, amma a fuskarsa wannan karon akwai sassauci, a idanun sa wannan karon akwai rahma, kai har da wani boyayyen sirrin da baya so ta ankara da shi. Yace. “Me zan saurara daga gareki Madinah? Kada ki manta ni Sarham ba kowa bane, ba kuma dan kowa ba, dan Malaman makaranta ne, wadanda basu aje ba, basu kuma ba wani ajiya ba,” Madinah ta runtse ido kalamansa na mata zafi, tace “ka saurare ni ko na minti biyar ne, in labarta maka duk abubuwan da suka faru dani a lokacin”. Sarham yace “abu daya zan saurara daga bakin ki shine, meye DALILIN KI na kin nema na duk tsayin wannnan lokacin?” Madinah ta ce “ban da dalili, bani da hujjar kare kaina” “then why are you here?” Tace “saboda in baka hakuri, in kuma kai ka gaban Daddyn nawa, don ya dade yana neman ka, ya gana da kai”. Sarham yace “ai in baki sani ba, duk wani mumini sau daya maciji yake saran sa a rami guda bisa kuskure ko kaddara, amma sara na biyu, saidai idan shi ya kai kansa da kansa”. Madinah ta ce “duk da haka Sarham, na kuma yarda da kai. Wancan lokacin haka nazo na daukeka na kaika gabansa ba tare da sanin zai ci mutuncin ka da zarafinka ba, to yau ma hakan, at the same time, wannan lokacin ma ban san meyasa yake neman naka ba. But do me this favour, ko da itace alfarma ta karshe da zaka yi min a rayuwarka!”. Daga wannan Dr. Sarham bai san meyasa bai kara musawa ba, ya samu kansa da bin bayan Madinah zuwa motar ta tamkar rakumi da akala. **** **** **** SULHU S un zauna shi da Daddyn Madinah a falon ganawa da bakin sa, Alhaji Attahiru yace “Sarhamu ba wani abune dalilinta ba, wanda ya hanata nemanka all this while, face BIYAYYAR IYAYE, ina fatan hujjarta wadda ta isa hujja a takaice, ta samu karbuwa a wurin ka, tunda kaima kana burin naka ‘ya’yan watarana su yi maka biyayya irin wadda Madinah take yi min. Autata Madinah mai gudun zuciyar iyaye ce da son gamawa dasu lafiya, shiyasa bata daga ido akan duk wani umarninmu zuwa gareta, ba don ta daina son ka bane taki neman ka, a duka shekarun nan tana dakon soyayyar ka ne, ni da bata fadawa hakan ba amma nine shaidar hakan, amma a haka na rufe ido nayi mata aure da wanda hankali na ya kwanta da shi. Wani irin dago kai Sarham yayi cikin slow motion, jin furucin Baban Madina na karshe, Alhajin bai damu da reaction dinsa ba ya cigaba da bayani, “kafin Allah ya nuna min ayar sa a kan ku, wato kafin in kai ta gidan mijin ya dauke abin sa, a hanyar sa ta zuwa daukan ta zuwa gidan sa, ta sanadin hadarin jirgin sama. Idan nace maka I was extremely shocked da mutuwar AVM as at that time, kaima ka san yayi kadan ya bayyana dimuwar tawa. Da albarka ta yau nake cewa idan har yanzu kana ra’ayin auren Madinah to kaje ka turomin mahaifan ka su karba maka auren ta, bana bukatar komai sai sadaki”. Duk da haka, duk da wannan ban hakurin da dattaku da Daddyn Madinah ya nuna a yanzu, da cewa da yayi yayi nadamar abinda yayi masa, ya kuma ce baya bukatar komai na auren Madinah daga gareshi sai sadaki, bai wanke zuciyarsa ba. Madinah ta sha matukar wahala kafin Sarham ya sauko, wato kafin ta samu ta shawo kansa ya sakar mata fuska ma kadai, domin wata ‘yar karamar zautuwa ce ta same shi akan maganar auren ta da marigayi AVM. Duk da maganar ta zo masa bagatatan, amma bai yi mamakin jin ta ba, sabida shi kansa ya san Madinah ba matar bari bace ga maza ‘yan uwansa, ya kasa sake mata fuska in ya tuna wai har aure aka daura mata, shi bai yarda bama wai bata je gidan mijin ba, watakila Daddynta ya fada ne don ya rage masa zautuwa, amma dai ko yaya Madinah take Madinah ce a wurin sa, ya sani ba zai iya daina son ta ba, ko da kuwa ‘ya’ya goma ta haifawa AVM din, yaki yarda sam ya koma mata ‘jovial Sarhamun sa’, duk wani annuri ya kau daga kyakkyawar fuskarsa. Rabuwar su ta wadannan shekarun da maganar daura mata aure da mahaifin ta ya sanar

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});