Chapter 30
Chapter 30
a kaunar fisabilillah da yake yi musu. Aka kai Hauwa nata dakin aka nuna mata direction na sallah dana zuwa toilet da madannin flushing. Ga dan karamin firji a gefen katifar ta (bed side fridge) Sarham ya ajiye mata don ya san ta da son shan abu mai sanyi tun baya, kai yau Inna da Hauwa farin cikin ya fi gaban ayi masa kuka ko dariya sai dai kawai ayi kurum, kamar yadda Hauwa tayi kurum! Bayan sun gama zaga gidan sun zauna suna hira shi da Inna. Ya ce “wai ta yaya ma aka yi takardun gidan suka je hanun Zakari? Bayan kowa ya shaida ya sayarwa da malam Bilyaminu gidan kamar yadda Malam Isa ya bashi labari?” Inna ta ce “umh, ai in kana neman hatsabibi ka samu Zakari ka gode Allah, maiyuwuwa yana da na kwarai dinne ya bawa Malam na jabu, ko kuma yasa an yi masa na jabu, oho, tunda har gobe na gonar su Baban Hauwa ya gayamin suna hannun sa, gab da batan Baban Hauwa, yace min sai ya karbi hakkin sa gun dan uwansa Zakari, wanda yake boyewa don a tunanin sa ya dauka Malam bai san da su ba. Ina nufin gonar mahaifin su ta Panshekara wadda girman ta ya kai na naira miliyan daya”. Sarham ya shiga mamaki mai yawa, ashe shiyasa Baban sa baya son sake aure? Kullum sai yace masa yana tsoron rarrabuwar kan su ne, shiyasa bai yi musu ‘yan uba ba. Sun dade suna zantawa kamar Da da uwar sa, Hauwa kuwa tunda ta shige daki ta kwanta a sabuwar katifa bata kara fitowa ba don daga baya ma wani ni’imtaccen barci ne yayi awon gaba da ita, irin wanda rabon ta da shi tunda Inna ta fara kwanciya ciwo. Da ya zo tafiya ne jin ta shiru ya dan leka dakinta, nan ya ganta tayi dai-dai tana kwasar barci da nutsuwa da kwanciyar hankali, numfashin ta yana hawa yana sauka freely, ashe tafi kyau in tana barci irin mutanen da ake kira sleeping beauty. Ya dan kalleta na ‘yan sakanni yana jin ta kamar Sumayyah a ran sa, ya kudurce a zuciyar sa zai tsayawa rayuwar ta, zai ingantata, zai mata abinda idan Sumayyah ce nakasar idanu ta sameta zai tsaya ya yi mata. Daga nan gidan su ya koma, a falo ya tadda iyayen sa, kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham yanzu ka tabbatar yana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba kamar watannin baya ba, gashi Madinah ta cika masa ciki da abinci mai dadi, so bai waiwayi abincin sa dake bisa tebir ba ya zauna gun Abba Prof. amma ya killace bakin sa baiyi zancen su Hauwa ba, don ya lura bat un yau ba Abban (is not interested) akan zancen su, musamman da ya ga ya dauki al’amarin su da muhimmancin da yake neman wuce kima, kuma ya tambayeshi meye alaqar su ta hakika ya tsaya yi masa kame-kame. Tun daga lokacin yace, “to in babu wata kebantacciyar alaqa da musuluci ya yarda da ita, to ya cire damuwar rashin ganin su daga ran sa, ya bar su a hannun Ubangijin da ya halicce su, tunda uban su ma da ya bar su ai basu kasa rayuwa ba. Don haka baima kowa zancen ya ga su Hauwa ba, bai sani ba tuni Mai Shari’ah wato Barrister (Mama) ta dade da ramfo shi. Kafin kwana uku duk makwabta sun san da dawowar Hauwa da Innar ta, aka yi ta shigowa ana ma Inna barka da arziki, da dawowar ta gidan ta, ana hirar yaushe gamo, aka yi ta tuna baya ana tattaunawa kan girman yara na yanzu, musamman ‘ya’ya mata da ba wuya sun girma, dubi dai yadda Hauwa ta gandame, ana tattaunawa a kai, kusan duk jama’ar Badalar Kofar Na’isa sun san Inna da abinda Zakari yayi mata saboda kyakkyawar mu’amalar ta da kowa, sannan yanzu sabon gidan nasu ya fito da gidan sosai. Har an sawa gidan suna sabon gida. A yanzu sai ya zamana babu gida mai zubin zamani da kuma kyawun nasu a bayan Badalar ta Kofar Na'isa. Washegari da suka wayi gari a kwana na uku da tarewar su. Inna ta ce da Hauwa zata shiga gidan Malam Isa su gaisa da iyalinsa, tace saboda ta ga kowa ya shigo mata murna banda Maikosai. Hauwa tace “toh Inna kada ki dade” tace “kada ki damu bazan jima ba”, ta fita. Tayi sallama gidan Malam Isa, Maikosai, wadda sunanta na ainahi Talatu, ta gama suyar kosan safe ta sayar, tana wanke kayan suyar ta a gindin rijiya ta amsa sallamar Inna, sannan ta juyo don ganin mai shigowa sai ta ga Innar Hauwa, nan da nan ta yi fuska ta juya ta cigaba da abinda take yi ta barta anan tsaye, sai da ta kammala tas ta zo ta zauna ta baiwa Innar Hauwa kujera ‘yar tsugunne, itama ta samu waje ta zauna akan tabarmar kofar dakin ta, suka gaisa kadaran kadahan sai Inna tace. “Zuwa nayi mu gaisa Maikosai, naga kowa na zuwa muna gaisawa, ke kadai ce ban gan ki kin zo ba, shine na shigo in gaida ke, Allah dai yasa lafiya”, inji Inna. Mai kosai ta ce “in kinji shiru ai shine lafiya, lafiya ke buya ba rashinta ba, don haka ni lafiya ta kalau, har kin yi GAIBAR ne kin dawo?” Cikin rashin fahimta Inna tace “menene kuma GAIBA?” Maikosai ta kalle ta a lalace tace “kina nufin ni zaki binne a baibai? Ko ba da hausa nake magana ba? Kin dauka ban ji me kuke shiryawa ke da bazawarin ki Malam Isa Mai Itace ba, na kiyi Gaiba ki dawo ya aure ki? Allah na tuba ko meye abin likewa tsoho kamar malam Isa oho, yana fama da kakhi da majinar tsufa?” Inna tace “innalillahi wa’inna ilaihi rajioun, ni Safiya me nake ji haka? Da auren nawa na likewa Malam Isa? Ni Safiyar ko dai wata ce kike nufi kika dauka ni ce?” Maikosai tayi tsaki tace. “Ahap! Da bakin sa ya gayamin kin dawo zakuyi Gaiba ya aure ki, ko kin dauka akwai abinda yake boye min?” Inna ta mike tsaye tana fadin “Maikosai baki da lafiya, ina rokon Allah ya baki lafiya”, daga haka ta fice ta barta tana ta sakin maganganu marassa kai bare kafa. A zaure ta ci karo da Malam Isa zai shigo, cikin far’a Malam Isa yace “a’ah, Innar Hauwa da kan ta yau a gidan mu? Maraba lale”, wani kallo da Innar Hauwa ta yi masa yasa nan da nan ya sha jinin jikin sa, yayi tsuru-tsuru kamar bafaden da yayiwa sarki karya, tasa kai ta wuce abinta ba tareda ta ce masa kanzil ba. Malam Isa ya fada gidan sa kamar an jefo shi, yana kwalawa Maikosai kira, a zaune ya sameta tana ta kunkuni ita kadai yace “uban me kika cewa Safiya?” Tayi tsaki tace “munafurcin da kuke kullawa na gaya mata na san komai” Malam Isa ya yi salati yace “amma Maikosai anyi dabba a cikin garke, kin jika min aiki, tsakanina da ke Allah ya isa”. Maikosai ta tafa hannu tace “kace haka mana, saboda kafi so ku cigaba da ninke ni a baibai, saidai inji sallamar kishiya a kaina, duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36