Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fara kyautatawa Sumayyah. In har kyautatawa na sawa a so mutum, to Sumayyah sai ta so ta, don an ce zuciya na son mai kyautata mata. Sun je sun gaida Haj. Kulu Surayyah ce ta tuka su a motar Mama su uku, daga nan suka dan zazzaga da Madinah taga gari, sune har Gidan Makama Museum da Gidan Dan hausa, Madinah ta roki Surayyah bayan sun gama zagayen da su je ‘main house’ din su a SoronDinki. Tun daga gate suka tabbatar sun zo babban gida, kuma tun daga karbar da akayi musu suka yarda gidan su Madinah gidan karamci ne da karrama baki. Sannan ana ji da Madinah a family dinta. Basu jima sosai ba tayi sallama da Kakar ta da sauran ‘yan uwan ta suka koma gida. Washegari ya kama ranar da zasu koma Jeddah, shiri sosai Mama ta yi musu na kayan abincin da babu a can, su maggi dunkule, ta kuma yi musu dambun nama mai yawa, gasu alkaki, dubulan, nakiya, bakilawa da gireba na cikin garar Madinah da aka kawo, duk tasa an shirya musu a jakunkuna daidai kilo dinsu, Sarham yayi sallama da iyayen sa da Kakar sa Haj. Kulu. Surayyah ta dauke su a motar Mama tayi musu rakiya zuwa filin jirgin malam Aminu Kano, suka tashi su uku wato, Sarham da Madinah, da kanwar sa Sumayyah wadda zata fara karatun medicine karkashin kulawar Yayan ta a birnin Jeddah. ****** ***** ***** S umayyah Allah-Allah take su sauka a Jeddah, ta kama hanyar makaranta, ta kyale Sarham da matar sa, don ta gaji da ganin salo da rashin kawaici irin na Madinah. Bayan saukar su a Jeddah hidimar makarantar Sumayyah ya fara yi, tun ma kafin su tare a gidan su, Madinah ta sauka wajen iyayen ta kafin a gama shirya musu gidan su da Saudi-German suka basu a gidajen likitocinsu, cikin kwanaki uku da saukar su har Sumayyah ta fara karatun ta, aka bata daki a hostel din dalibai kamar yadda tafi so, shi kuma yayi ‘documentation’ na karbar aikin sa a cikin kwanakin da asibitin kwararrun ido na Saudi-German. Dr. Sarham Abbas Shanono ya zama cikakken likitan fidar ido (ophthalmic surgeon), daya daga cikin manyan likitocin idon da Saudi-German ke ji dasu da alfahari su. Saida ya kammala ‘documentation’ din sa aka kuma gama shirya musu gidan nasu daga dukiyar gidansu Madinah, daga nan gidan su ya dauketa suka wuce babban birni wato (Riyadh) ta jirgin sama domin barje gumin amarci, abinda larabawa suke kira ‘Shahar Al-asal’ wato (honeymoon) da harshen larabci, inda acan Sarham ya gama gane aya da tsakuwa wato AVM Alkali bai yi masa barnar da yake tsoro ba, tuni ya ware aka barji amarci gangariya da matar da yakewa so gangariya, wanda shi kan sa ya san son da yake wa Madinah mai yawa ne, da har wani lokacin yake tausayin kan sa. Daga ‘first-night’ din su, Madinah ta idasa tashin kan Sarham, domin abinda yake zato ba haka ya sameshi ba. AVM bai yi masa barna ba, bai kuma bar masa sudi ba, domin kuwa shi ya bare alewar sa a leda. Suna Riyadh ana barzar amarci a wani babban hotel na kasar, har tsayin sati guda kafin su dawo Jeddah. Dr. Sarham Abbas, ya kama aikin sa ka’in da na’in a asibitin “SAUDI-GERMAN”. **** **** **** Kullum amarcinsu sabo dal yake komawa basa taba gundura da juna. Amma duk da haka Madinah tana ta zuba idon taga Sumayyah ta dawo wajen su da zama bayan dawowar su gida daga honeymoon, amma bata gan ta ba, bata kuma ji Sarham yayi maganar dawowar ta wajen su ba ko sau daya, sai ta tambayeshi a wani maraice. “Ni Dr. ina Sumayyah ne? Sumayyah ba a wajen mu zata zauna bane? Ta yaya muna gari daya amma zamu barta ta zauna a hostel?” Yace cikin rashin damuwa da maganar “kada ki damu, zabinta ne”. Madinah bata gamsu ba, tace “amma dai Mama bazata ji dadi ba in taji bama tare da ita, kamar mun kasa rike ta zata gani” ya ce cikin kosawa da zancen “Madinah ki yi abinda ke gaban ki kin ji! Ki manta da Summy. Ban san ki da shiga sharo ba shanu ba. Summy wata irin hutsuwa ce, bata son shiga harkar mutane kamar yadda kema bakiso kowa ya shiga taki in ba ke kika saka kanki ba, itama haka take”. Ya fadi hakan ne don bazai iya gaya mata gaskiyar cewa Sumayyah bata yin ta ba, wanda gaskiyar maganar kenan, jininsu bai hadu ba, wato bata a layin mutanen dake son ita Madinar, ta bangaren ahalinsa. Amma duk da hakan data fahimta da kanta ba tareda ya fito fili yayi bayanin ‘fear’ din Sumayyah a kanta ba, Madinah bata fasa kyautatawa Sumayyah ba, haka kawai zata yi shopping niki-niki ta dauka a bayan mota ta kai mata har dakinta na hostel din, ko kayan abinci ko na shafa. Daidai gwargwado Madinah tayi kokarin jan Sumayyah a jiki ko don ta samu ‘yar uwa mace, kasancewar nata ‘yan uwan duk maza ne amma abin mamaki ko kadan Sumayyah ta kasa son Madinah, ta ki sakar mata jiki. Sarham ya sha zama yana lallashin Sumayyah a bayan idon Madinah, kan ta bude zuciyar ta wa Madinah, ta dauka ita da shi ba banbanci, wato ta dauketa matsayin Yayar ta kamar yadda ta dauke shi Yayanta, amma taurin kai irin na Sumayyah akan Madinah ya ki canzuwa, Sarham ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai a tsakanin su, tunda shi kam ai zuwan Madinah bai sa ya canza ma kannen shi ko iyayen shi da komai ba. To haka Surayyah ma dake can gida tana shan aiken kaya daga Dr. Madinah duk lokacin da ta samu mai zuwa Kano, lazim ne ta yiwa Surayyah aike. Haka koyaushe suna like a waya tasu kam ta zo daya, amma Sumayya kullum ranta kara nesanta yake da shiga harkar Madinah, saidai ta yarda auren sa da Madinah, da kuma uwa uba zazzafar soyayyar da yake mata kamar ya hadiye ta duk basu sa Sarham din ya canza musu ba su kannen sa da iyayen sa. “Madinah-Munauwarah”, cikin watanni uku ta zama GIWAr mace a gidan ta, shi da kan sa Sarham in yayi nishadi GIWAR SARHAM yake kiranta, Madinah ta samu fada a wajen mijin ta yadda ba’a zato, saboda tarin baiwarwakin da Allah yayi mata musamman na iya masa da duk fitinar sa a shimfida, Madinah ta yarda da gaske ko a cikin maza nata mijin daban ne a fannin shimfidarsa da matar sa, ta iya kalamai masu sanyi da sanyaya zuciyar miji a duk halin da yake ciki, ta kalmashe shi da iya girki na zamani, da iya kula da shi a shimfida, ta kware wajen taya shi kula da tsaftar jikin sa, kula da kannen sa wadanda ta gama lura baya hada kaunar su da komai a ransa saboda irin ‘upbringing’ din da iyayen su suka yi musu kenan na kaunar junan su da hadin kai a junansu, kasancewar basu da yawa a wurin iyayen su. Madinah irin matan nan ne masu nacin shiga (educational programs) da ake yi a Saudi-Arabia, duk wasu programs irin na (marriage coaches) na mata musulmi masu burin karawa juna

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});