Chapter 20
Chapter 20
dawo ta tsaya a gaban sa tana tura baki gaba, ya ce “kin gama hada kayan naki?” Ta ce “hada kaya kuma? Ina zani?” yace “eh, Abba bai gaya miki da ke zamu tafi Jeddah ba, zaki zauna a gida na ki fara MBBS? Tukunnama wai me nayi miki kike gaba da ni haka? What’s wrong with you?” Sumayyah mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta soma hawaye na babu gaira babu dalili, tace “wallahi in dai a gidan ku zan zauna to na fasa karatun a can, ni ba don kai da matar ka zan je Jeddah ba, ba ‘yar zaman daki kuka samu ba, zani jami’ar Sarki Abdulazeez ne, zaman karatun kaina, kowa yayi rayuwar sa a inda yake zaune duk da muna gari daya”. Cikin madaukakin mamaki Sarham ya ke duban Sumayyah, da babbar murya yace “Summy! Kina cikin hankalin ki kuwa? Ko kin fara shaye-shaye ne?” Sumayyah ta murgude baki gefe tace “Allah ya sauwake in yi shaye-shaye, kawai dai… ni bazan zauna a gidan ku bane, in ba hostel za’a kaini na zauna ba, to a nema min admission a BUK”. Cikin kokarin hadiye fushi da bacin rai da ke tunkudo masa Sarham ya ce “to na ji, matsalar ki ce wannan yin karatu a Jeddah ko barin sa bakidaya, amma ki gayamin dalilin ki na kulla gaba da ni, da fita sha’ani na alhalin ba haka muke nida ke ba, sai yanzu da na yi aure, bayan kinsan mata ta bata tare ba balle ta cigaba da yimin hidimar da kike yi min”. Sumayyah ta ce “Bhaiya, kaima gashi nan aika fada da bakin ka, “KA YI AURE!” Tunda kayi aure ni ba ruwa na da harkar ka gaskiya, kada wataran azo an araba ni dambe da matarka don na fahimce ta mai kishi ce, sannan na san wannan matar taka mai kama da larabawan aljannah, ba zata barni da kai ba sai ta raba mu, ga shegiyar kissa da kinibibi da rashin kawaici a kanka, tana wani kalmashe murya kamar kyanwa, shiyasa tun yanzu na raba kaina da kai, ba sai ta raba mu in zo ina jin zafin ta ba”. Sarham baki bude yake kallon Sumayyah, yaki yardarwa kansa bata sha kwaya ba, yana ji ana cewa wai kanne na kishi da matan yayyun su, bai taba yarda ba sai yau. Sai ya kwantar da ido da murya ganin Sumayya na share hawaye kuma, tana tuno irin tsananin shakuwar dake tsakanin ta da Bhaiya, yau ga wata ta zo ta shiga tsakani, ta fita kusanci dashi, kuma ta san ta shigo rayuwar su kenan har abada, bazasu kara samun kusancin da suke da shi ba ita da shi yanzu, saboda matar sa. Yanzu kam ya yarda Sumayyah bata sha komai ba, ‘inner feelings’ dinta kenan, wanda ya sabawa hankali, shi take fada masa ba karya take ba, ba kuma hassada take yi wa Madinah ba, a’ah tata damuwar ce ta karan-kanta, saboda yadda ta damu da zumuncin da ke tsakanin ta shi. Yace “Sumayah kada Allah ya baiwa kowacce irin mace da zan aura iko a kaina, ba a kan ki ke kadai ba, har iyayena da Surayyah, kada Allah ya dora min soyayyar da zata rufe min idanu in canza muku da wani abu saboda mace, ko in yanke zumuncin dake tsakanin mu, ko in kasa kyautata muku da kula da rayuwar ku”. Sarham ya ja mumfashi a hankali, kafin yace “My sister Sumayyah, ki taya ni addu’a kin ji?” Sumayyah tace “ai son da kake mata yayi yawa ne, Yaya Sarham ban so ka auri macen da son da kake mata ya rinjayi nata ba, don tsaf! Zata raba ka da kowa naka”. Sarham yace “Sumayyah wannan tunanin ku ne irin na mata, ki bari ki ga kamun ludayin Madinah tukunnah, ina tabbatar miki Madinah daban take da sauran mata, don bata tashi anan ba, kuma bata tashi cikin mata ba sai ‘yan maza, duka wadannan halayen na mugunta bata san su ba, I assured you. Madinah mai ilmi ce kuma mai hankali, ta san abinda take yi kin ji?” Da wadannan kalaman ya samu yayi ta lallashin Sumayyah, har ta dan saki fuska ta daina kukan, amma tayi masa rantsuwa akan ita ba zata zauna a hannun Madinah a Jeddah ba, a makaranta zata zauna. Sarham yace “in aka barki kika zauna a makarantar shikenan baki da damuwa?” tace “eh, saboda matar ka ce raina baya so” ya ce cikin rashin jin dadi, “to na yarda, ban kuma isa in sa ki so ta dole ba, amma don Allah Sumayyah kada ki kulla gaba da Madinah akan haka, mai son naka masoyinka ne ba makiyin ka ba, ki bata dama ki ga irin halayenta”. Sumayyah tace cikin jin tausayinsa “toh!” ya ce “zaki gyara min dakin nawa yanzu? Yau kwana bakwai baki share min ba, ban ci girkin ki mai dadi ba kanwata ta kaina”, tayi dan murmushi tace “zan gyara dakin, for now, amma ka cire ni daga dafa maka abinci da gyara maka daki kaima daga yau, ka koyi cin na matar ka”. Da wannan suka tako a tare zuwa cikin gida. Sumayyah ta je ta gyara masa dakin sannan ta tafi hada kayan ta da zata tafi da su Jeddah, tana cikin hada kayan Mama ta kirata tace taje ta zo da Madinah, zasu fita ssallama gidan Hajiya Kulu su kuma gaishe ta bata jin dadi. Sumayyah ta bata rai, tace “Mama why not Surayyah ta kira miki ita? Tunda tasu ta zo daya?” Mama ta ce “ke bana son rashin hankali kishin kannen miji, ki raba kan ki da wahalar da bata da amfani, tunda ke dai bazai aure ki ba, ita din da baki so ita Allah ya halatta masa”. Sumayyah tana kokarin ta hadiye bacin ranta, ta ce “Mama Allah ya sawwake in yi kishin Yaya na, kawai ni I DON’T LIKE HER! AND I DON’T KNOW WHY?” Sai tasa kuka. Mama ta rungume Sumayyah tana lallashin ta, a lokacin tayi ta kokarin ganar da ita hakan bashi da amfani kuma kuskure ne, in har tana so ta zauna lafiya da dan uwanta dole taso matar sa wadda bada jimawa ba zata zama uwar ‘ya’yan sa. Ta tilasta mata kan ta je ta kira Madinah da kanta su tafi Gadon Kaya tare. Ko da ta shiga dakin Madinah na waya da Sarham, ana kalmasa harshe da larabci ziryan, cikin wani ‘accent’ dinta da shi kadai take yiwa magana da shi. Kyabe baki Sumayyah tayi ta ce, “in kin gama an ce ki zo mu tafi Gadon kaya”. Ta juya tayi ficewar ta. Batun yau ba Madinah ta fahimci Sumayyah bata yin ta, ba kuma don tayi mata wani laifi ba sai don a matsayin ta na masaniya akan halayen mata ‘yan uwanta psychologically ta gane Sumayyah irin kannen mijin nan ne masu kulafucin zumunci da yayyensu. Wanda hakan ke sawa su kasa shiri da matan su na aure don a ganinsu zasu raba su, amma ta san Surayyah sosai take yin ta, halinta daban dana ‘yar uwarta, itace ‘yar dakin ta, tasu tafi zuwa daya, kullum sai ta zo mata hira. Madinah tasa a ranta daga yau zata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36