Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kofa, kafin ya isa kofar Nassarawa ya dawo da baya ya isa kofar Dan agundi yana ta fatan Allah yasa ya ga Inna da Hauwa koda a hanya ne, amma har duhu ya baibaye sararin samaniya, wanda yasa ya daina shaida fuskokin mutane, kuma man motarsa ya kusa kafewa, ko mai kama da su bai gani ba, duk kuwa da irin kallon kurillar da yake yiwa mata da musaki bisa tituna da Kofofin Kano, da cikin unguwannin Badala. Allah sarki Dr. Sarham! Kafin ya koma gida har rama yayi, yayi zuru-zuru yayi dan wuya sabida yunwa da damuwa da gajiya da bacin rai. Kamar ba sabon ango ba, na Madinah bada kanka a sare! Ya koma gida a jigace, wajen karfe goma na dare, amma sai ya kasa zaman falon duk kuwa da cewa ya gansu a zazzaune duk zaman jiran dawowar sa suke yi har Abba, domin a bashi hakurin laifin Surayyah gareshi. Ganin yana nema wucewa dakin sa bayan ya gaida Abba da Mama, ba tare da ya ko zauna an yi hira yadda aka saba ba. Abba ya dakatar da shi, ta hanyar bashi kujera da hannun sa ya ce ya zauna, Sarham ya tsaya a tsaye kamar mai ciwon kafa, sai Abba yace, “lelen Abba daga ina kake haka, kamar an maka dukan tsiya? Ka gan ka kuwa?”. Sarham bai yi aune ba yaji wata irin hajijiya na neman kayar dashi saboda yunwa da gajiya, ba shiri ya lalubi kujerar ya zauna yace “wash! Abba, kai na!” Ya kama kannasa da hannu bibbiyu. Abba ya ce “sannu, Sumayyah kawo masa ruwa da abinci, hajijiya ai yunwa ce, me ke faruwa?” Sarham bai san lokacin da yace “Abba na neme su na rasa, ba inda ban dub aba, ba Badalar Kano da ban zagaya ba, ko mai kama dasu ban gani ba, duniyar nan cike take da azzaluman ‘yan uwa Abba, kowanne dan uwa ya samu faraga sai ya ci amanar dan uwan sa in baya nan, why?” Surayyyah ta saka kuka don ta dauka wannan maganar da ita Sarham yake ta ce “wallahi Bhaiya ban yi da niyyar cin amanarka ba, na tuba ni kam na shiga uku! Ka dauki abinnan da zafi har fiye da kima Bhaiya” wata uwar harara daya zabga mata ya ce a fusace “na saka ki a cikin magana ta? Kin san wa nake nufi ko su wa nake magana akan su?” Mama ta ce “kayi hakuri Sarham, zancen nan ya wuce don Allah bazata sake ba na mata fada sosai”. Yace Mama ni ba zancen ta nake ba Mama, already na yafe mata, na fadawa kaina da kaina na yafe mata yafi sau shurin masaki, tun fita ta ban fita da ita a raina ba, zancen su Inna da Hauwa nake,” “Su waye kuma Inna da Hauwa kuma?” Abba da Mama har suna hada baki wajen tambaya, da tunanin ko gamo yayi, ya ce “yarinyar da ta makance a hannu na, (excuse me) na makanta ta by mistake, tun daga lokacin kuma nake kula da karatun ta.” “Au ho!” in ji Mama, ai kuwa ban manta da zancenta ba, da yadda ka shiga damuwa a lokacin, har yanzu idon nata bai gyaru ba? Kuma wai basu da Uba ne?” Sarham ya baiwa iyayen sa kaf labarin su Inna, tun ranar da suka fara haduwa a asibitin Murtala, da aikin da yayi mata da sabon da ya shiga tsakanin su aftermath wato bayan hakan, da yadda aka yi ya kai Hauwa makarantar (Special School Kano), da yin sallamarsu lokacin da zai tafi Jeddah, zuwa yanzu da ya dawo yaji abun da ya faru da su daga kanin Baban ta, ya kuma gaya musu batan Malam Bilyaminu tun kafin haduwar sa da su. Mama don tausayi har da kwallah tace “Allah to ya jefa su a hannu nagari, ya kuma bata lafiya a duk inda take, kai kuma ya baka ladan taimako”. Abba yace “amin, Allah kuma ya saka musu. Ya bi musu hakkin su. Amma don Allah ka ci abinci, ka huta, ka nutsu, ka tuna cewa kaifa sabon Ango ne akwai nauyi yanzu a kan ka. Ya gaya masa cewa sunyi waya da Daddyn Madinah dazu, nan da kwana uku za’a taho da ita Kano, ba sai ya koma Jeddah dauko ta ba, Babanta yace ya daina cewa ango ya zo ya dauketa kasa-ya-kasa tun daga abinda ya faru kan mijin ta na fari, ina ya tanadar mata domin a sauke ta? Sarham babu wani doki a tare da shi don zuciyarsa bakidaya bakikkirin take, yace shi ginin da ya fara bai kammala ba, sai dai Abba ya ara masa gidan sa na Rimin Gata (nan baya sabuwar jami’ar Bayero) a sauketa acan. Yace amma in son samu ne shi ya fi so Madinah ta zauna a nan gidan su tashin farko, ba don komai ba sai don ta saba da su Mama tunda na dan lokaci ne zasu koma Jeddah. (A baya baiyi niyyar komawa Jiddah ba amma yanzu Kano ta fice masa a rai). Daddy ya ji dadi sosai, don a yadda na gina rayuwar iyalinsa da so da kaunar juna, kwarai yake so matar duk da Sarham ya aura ta zamo daya daga cikin iyalin sa, baya so don yayi aure yayi nesa dasu, musamman saboda shakuwar sa da kanwarsa Sumayyah, shakuwar dake tsakanin su har tsoro yake kada yayi aure mace ta zamo sanadinta, Abba ya ce, “shike nan hakan yayi kyau, madallah, ita Sumayyah sai ta koma dakin Surayyah, su zauna tare for the mean time, sai a gyara ma Madinah dakin Sumayyah ta zauna har zuwa lokacin da zaku koma Jeddah din, Abba ya tambayeshi ko ya gama kwas din sa? kuma yaya batun aikinsa na Murtala da yake batun komawa? Ya gaya masa cewa ya gama, amma zai koma bikin kammalawa da karbo shaidar kammalawa, shi da Madina har yanzu basu zauna (officially) sun magantu sun yanke shawarar inda zasu zauna ba. Amma yanzu kam yafi so ya koma Jeddah. Bayan ya koma dakin sa yayi wanka ya yi sallolin dake kansa sai ya samu kansa da zama dirshan akan dardumar sallahrsa ya rasa abinda ke masa dadi, abun mamaki ga kiran Madinah na ta shigo masa akai-akai don tun bayan da aka daura musu aure basu yi magana ba, amma ga mamakin sa ya kasa dagawa, a lokacin damuwar da yake ciki tasa komai ya fita kan sa, ya samu kan sa da daga hannu yana yiwa su Hauwa addu’a, damuwa tasa a ranar ko runtsawa na awa guda bai iya yayi ba. Washegari yaje ya kai kudin filin gidan su Hauwa, ya karbi takardun filin a gaban kwararan shaidu dattijan unguwa su malam Isa da sabon mai unguwa, kowa yana ta mamakin ko me zai yi da filin, shi ba dan unguwar ba, ba kuma dan Malam Bilyaminu ba, amma dai ai yace shi dan uwan Innar Hauwa ne. Wayar da ya sayawa Inna sai ya samu kansa da mallakawa Malam Isa, ya kuma karbi lambarsa yace zasu dinga gaisawa kuma zai dinga turo masa kudin abincin dabbobin Inna da yake kiwata mata, ya fadi hakan ne a lokacin suna cikin garken dabbobin, suna zagawa yaa kallonsu, ya ga yawan su

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});