Chapter 11
Chapter 11
da shi sun sa ya canza da yawa daga halayen sa data sani na sakin fuska dayawan walwala, ko ace ita Madinah ta canza shi, ta mayar dashi tattaura, mai tsauri, kuma mai wuyar sha’ani. Duk da haka yana nan a ‘jovial’ Sarham din sa, wato mai far’a da faram-faram da mutane amma banda ga ita Madinah, sau tari sai yayi ra’ayi zata ga hasken hakoransa, ko inda wasu mutane daban yake tare. Duk Madinah ta jure wannan punishment din da bata da laifi, ta san wuyarta kawai su yi aure kawai komai zai zama labari. Wani irin kishi ke cin ransa akan maganar auren Madinah da wanin sa, kuma taki su magantu akai sam, da ya kawo zancen zata bata rai, ta ki tankawa. In ya takura da tambayarta wani abu akan aurenta da AVM ko makamancin haka sai kawai ta saka masa kuka. Ko yaki ko yaso dole ya bar zancen. Ba kamar can baya ba da kullum zaka tadda fararen hakoran sa (in yana gaban Madinah) a warwaje, ya kasa rufesu, kamar na mai tallan makilin dinnan ‘colgate’. Yanzu kam saidai ka ganshi bay abo ba kuma fallasa, fuskar ta koma kadaran-kadahan a gaban Madinah. Itama dole yasa saida ta rage nata far’an gareshi, ayi mutum kamar mutanen farko ba yafiya ba afuwa ba manta abinda ya shige? Aka koma kadaran-kadahan din ita da shi, amma dai suna tare koyaushe a cikin asibiti ko a cikin campus, ko a gidansu a weekend, haka suka kasance har zuwa ranar da Surayyah ta gaya masa ‘graduation’ din ta daga BUK. A ranar ne kuma Daddy, wato Alhajin su Madinah ya tabbatar masa ya bashi auren Madinah halak-malak, yaje ya zo masa da iyayen sa a tsayar da magana kawai. Ko yaki ko yaso, hakika yaji farin cikin hakan maras misaltuwa akan wannan albishir din na Alhajin kamar yanzu ya fara jinsa, komai pretending dinsa kuwa, musamman da Daddyn da kansa ya kira shi a waya ya gaya masa da bakin sa da nasa, don haka ya ajiye maganar kishin matacce a gefe, yana cewa da sannu zai rama ne. Madinah bazata ci sadakin maza biyu abanza ba dole ta gane shima yanada ajinsa in ta shigo gidan sa, sai ta gaya masa ko sau nawa AVM ya samu alfarmarta, kafin ya yarda su yi rayuwar farin ciki irin wadda ya dade da yi musu tanadi. Da wannan shawarar da yayi da zuciyarsa ya ajiye kishi a gefe ya koma na shirin tahowa gida, domin ya kammala kwas din da ya kaishi Jeddah gabadaya, a ranar yayi booking, zai taso a washegari, suka yi sallama da Madinah a asibitin Sarki AbdulAzeez, yau kam taga ‘yar walwalar Sarham, domin da zai tafi har yake ce mata duk ta yi baki ta rame, ina dalili? Madinah taji wani irin sanyi a ranta sai ga hawaye sun digo. Shi bai san yadda canza matan da yayi completely da yadda yake treating dinta yanzu ne wai don ta auri wani kafin shi bisa rubutacciyar kaddarar ta ya ramar da itan ba, ya kuma maida ita bakar ba? A lokacin sai bata bashi amsa ba, maimakon hakan, sai ta mika masa kyakkyawan kwalin dake sunke a hannun ta, mai dauke da kyawawan furanni da katon HAPPY BIRTHDAY card mai zanen zuciya. Sai a lokacin Sarham ya saki dariya don shi ya manta ma wai yau ne ya cika shekaru talatin da uku a duniya. Tunda ya hawo jirgi yake tunani, Allah dai yasa Surayyah na kaiwa su Inna kudin da yake aikowa ta account din ta da yace ta dinga baiwa Sumayyah tana kai musu, ta san gidan, don sun taba zuwa tare, ya san dai Innar Hauwa jarumar uwa ce, cikin kowanne hali zata kula da kanta, kuma zata kula da Hauwa-Kulunta, ba zata bari ta zama (drop out from school) ba. Dan abinda yake tura musu duk wata ya san zai ishe su cin abinci har wata ya zagayo, duk da ya san Inna bazata zauna haka babu sana’a ba, Allah yasa Sumayyahn kuma tana jure kai musu, kodayake Sumayyahn sa ba daga nan ba, wajen aikin zumunci da taya shi son duk abinda yake so, balle wadannan bayin Allah data fahimci sun mamaye rabin zuciyar sa! Jirgin su ya taso daga Jeddah a washegari bayan sun yi sallama emotionally shi da Madinah a filin jirgi, yanata kissima abubuwa daban daban a ransa, wadanda zai je ya tarar a Kano, akan dai Inna da Hauwa, da rayuwar da suka samu kan su a bayan babu shi. Sarham ya sa a ransa ba zai koma Jeddah dauko matar sa Madinah ba wannnan karon sai ya mallakawa Inna wayar tafi da gidan ka komai kankantar ta, don dai ya dinga jin lafiyar su kai tsaye, ba tare da ya saka ‘third party’ a tsakanin su ba. **** **** **** T axi din da Dr. Sarham ya dauko shata daga filin jirgi bata sauke shi a ko’ina ba sai a kofar gidan su. Wanda ke cikin rukunin gidajen malamai na sabuwar jami’ar Bayero. Surayyah ce ta fara hango shi daga tagar dakinta, daidai lokacin ta dage labule don samun iska kasancewar ‘nepa’ sun yi mata halin su na dauke wuta tana tsaka da shaqar barcin rana cikin A.C, wani hucin zafi ya tada ta, don haka ba shiri ta tashi ta dage labulen ta don ta samu ‘natural’ iska ta shigo mata, wannan ne yasa duk gidan ita ta fara ganin sa yana fitowa daga mota. Banda ‘jini’ sunan sa ‘jini’ da Surayyah bazata gane Bhaiyan Sumayyah ba sam, ko ta ce Yaya Doctor yadda take kiran sa ita, sabida girman da ya kara da irin canzawar da yayi a shekaru ukun da ya kwashe a kasar Saudi-Arabia, ilhamarsa da cikar zati sun karu, sun ninku akan wadanda ya bar gida dasu. Yayi haske kadan, fatar jikin sa ta yi ‘fresh’ kamar wanda ya shiga injin wankin fata. Karadin Surayyah shi ya tashi Sumayyah dake falo a gaban TV tana kallon diramar Hausa, ta yo dakin nata a guje don ta dauka wani abu ne ya same ta, da karfi Surayyah tace, “Summy Bhaiyan ki ne, Yaya Doctor ke shigowa”. To amma me? Sai ta tuno wani abu, wanda yasa nan da nan ta nutsu, ta daina murnar dawowar Bhaiya, gashi dai ya dawo ‘unexpected’, gashi ta masa babban laifi, tace cikin damuwa. “Summy na dauka ba yanzu zai dawo ba, na saka a raina kafin lokacin da zai dawo na hada kudin nan na baki sakon nan na mutanen nan kin kai musu duka a dunkule”. Sumayyah ta ce cikin mamaki “wane sako? Wadanne mutanen?” Cikin damuwar data fi ta baya Surayyah ta ce. “Ki min afuwa Summy, ban taba gaya miki Yaya Doctor yana aiko kudi ta account dina in baki ki dinga kaiwa mutanen nan nasa talakawa da ya likewa na kofar Na’isa ba, ni wallahi na ma manta, sai yanzu dana ganshi na tuna”. Ta kara da cewa “Summy don girman Allah ki rufa min asiri in ya tambaye ki kice ina baki duk wata kina kaiwa, in yaso zan dunkule duka abinda ke hannu na a yau in baki ki kai musu kafin ya je gidan, wallahi cosmetics (kayan kwalliya) and
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36