Chapter 25
Chapter 25
itama an gaya mata dai uwarta na suma. Don haka yau Hauwa ta wuni kuka wurjanjan har ta gode Allah, idan ta rasa Inna, bata san yaya zata cigaba da rayuwa ba. Tafada ta gaisa da mutanen data gani a zazzaune kafin ta kama Hauwa ta ce “nice Tafada, ina Innar taki wani ke ta son ganin ta tun daga Kano ya sako mu a gaba saida muka kawo shi nan, kamar dai dan uwanku ne”. Babu wanda ya zo wa Hauwa a rai da zai biyo bayan su har nan, cikin ‘yan uwan su duka sai Yaya Jamilu! Watakila yayi ta tambaya ne a kansu har ya gano inda suke. Tafada tayi mata jagora suka fito, a yadda Hauwa ta lalace ba don yayi mata farin sani ba da bazai gane ita ce ba, sabida yadda tayi baki ta kuma rame, Sarham ya runtse idon sa cikin tausayi marar misali, muryarsa na shakewa da sarkewa yace. “MAI-JID-DAH!”. Sai tayi sak! Da rai da kwakwalwarta cikin son tuno inda ta san sassanyar muryar, da kuma inda ta taba jin an kira ta da wannan kebantaccen sunan. Duk fadin duniya mutum daya ne ya taba kiran ta da “Maijiddah”, ya kuma ce sunan nashi ne shi kadai, bai yarda kowa ya kwaikwaya ya kira ta da shi ba wato LIKITA SARHAM!!! Hauwa-Kulu ta yi shiru na wucin gadi, kwakwalwarta na faman processing tattausar muryar data kira sunanta. Muryar Likita Sarham ce tabbas, wadda ko mutuwa tayi ta dawo bazata manta ‘accent’ dinta ba. Wani kwayan mutum guda daya da komai nisan shekaru bazata taba mantawa da shi ba, saboda kyakkyawar rawar da ya taka cikin rayuwar ta da gudunmuwar da ya basu, a lokacin da rayuwarta gabadaya ta dauko nakashewa. Duk da a cewar Hauwa, shi Sarham din shi ya karasa mata idanu, wato shi ya karasa makantata, amma bayan faruwar hakan ya kyautatawa rayuwar su, ya kuma taimaka ya hana rayuwar ta karasa rugujewa, ya karfafa mata da cewa kada ta bari ta durkushe a dalilin makanta. Rawar da Dr. Sarham Abbas Shanono ya taka cikin rayuwar su, duk da cewa ta dan lokaci ce, to fa hakika mai girma da muhimmanci ce domin ya nuna musu kauna da mutunci na masu ilmi. Da wuya ka samu mutum irin sa a wannan zamanin da yake yiwa talakawa da yafi matsayi da ajin rayuwa kamar su daukar mutane. Balle don wani tsautsayi ya faru a dalilin aikinsu su tsaya su yi waiwaye a kai. Ta tabbata da ace bai tafi inda ya tafi ba, da ba’a kawo wannan matakin ba a lafiyar Inna, da karatun ta, da komai ma na rayuwar su, ta tabbata zai cigaba ne da tsayawa rayuwar su kamar Baba da Zulkiflu na raye. Da bazai bari Zakari ya tozarta rayuwar su ba ya raba su da farin cikin su. Bata yi masa farin sani ba, saboda ko sanda yake tare da su kullace take da shi, bata tsaya ta saki jiki dashi ba, balle ta saba da shi, ko tayi masa kyakkyawan sani, amma ko daga sanin nesa nesa din data yi masa a gidan su ta shaida cewa shi din mutumin kirki ne, mai taimako ne, mai yawan alkhairi ne, ya san (human dignity), kuma yana matukar kaunar su sosai. Sai hawaye ya soma zubo mata, don ji tayi ma kamar BABANTA MALAM BILYAMINU YA DAWO! Tamkar wani ‘SAVIOUR’ (mai ceto) ya iso cikin rayuwar su, koko tace kamar wani Mala’ikan rahma ya riske su, a lokacin da Inna ke kan gargarar mutuwa cikin rashin gata, kuma a lokacin data fidda rai da tashin Inna. A can cikin kunne da kwakwalwarta, Hauwa ta tsinkayi muryar nan ta Dr. Sarham mai sanyi da gardi tana tsokanarta, zolaya irin wadda baya rabo da ita, kuma ya saba yi mata don ya samu ta kula shi. Aka ce a bar hali a ci me? Dr. Sarham har yanzu yana nan da (jovial personality) din sa. Hausawa suka ce in ka shekara baka ga mutum ba, ranar da kuka hadu, tambaye shi wani abun daban amma banda halin sa. Wato a nufin bahaushe halin mutum baya taba canzawa sai dai ko mu ce Sarham ya rage wasu daga cikin halayen sa na sakin fuska, da yawan magana, a dalilin girma da nauyin iyali da yanzu ya hau kan sa. “A yi magana ki ce an yi miki “GORIN IDO”, dubi kwala-kwalan idanun nata a jike jagab, jawur dasu, kamar kosan da ya soyu a cikin mai don kuka, maimakon ta saki far’a tace “Jabbama-jabbama…lale-maraba da bakon KANO. Ko tace YAYA SARHAM SANNU DA ZUWA”. A’ah ta tsaya tana mana ambaliyar hawaye, watakila anan garin nasu na Albasu, da haka ake saukar bako”. Sarham ya fada cikin zolayar Hauwa-Kulu, don rabata da hawayen dake ta satatar mata, da kokarin sa na hadiye nasa hawayen. Ba kankanin abu ke sa shi kuka ba, amma a yau ya san in bai yi da gaske ba ‘he cannot control his tears’ a gaban Hauwa, abinda bazai so hakan ba ko kadan. Kokarin gaske yayi da ya iya hadiye hawayen sa a kan idon Hauwa, wadda yake ma kallon kanwa ta jini, kamar Sumayyah, yadda ba zai iya bari Sumayyah ta ga raunin sa ba, haka ba zai bari Hauwa ta gani ba, ba don haka ba da tuni ya sake su sun shatato shima akan kundukukinsa, kamar yadda Hauwan ke faman yin nata, amma fa ita nata na farin ciki ne. Ganin yanayin wahala da rashin lafiya da ya same su ciki kuma a kauye ya karya zuciyar sa, wanda ba cikin sa ya tafi ya barsu ba. Cikin muryar kuka Hauwa ta ja sheshsheka ta ce “Likita sannu da zuwa”, tana mai yi ma saitin da muryarsa ke fitowa kallon ga ZULKIFLU YA DAWO. Sarham ya matso gaban ta har tana iya shako kamshin hamshakin turaren sa na ‘Oud Abyad’ ya ce “to ko ke fa Maijiddah! Amma kawai daga ganin mutane sai ki balle da bokitin hawaye? Ai sai su Malam Isa da Tafada su dauka baki yi maraba da zuwa na ba sam”. Tayi murmmushi, har kuncinta ya lotsa ciki sosai, wani abu da ke kara ma Hauwa’u kyau, yace “maza je ki kwaso kayan ku, Inna Tafada taimaka min ki dauko Inna don Allah a sa min ita a bayan mota, in yi maza in kaita asibiti, a kula min da ita da kyau”. A yau yana dakacen inama shi ba likitan ido bane, na zuciya ne! So that ya iya duba Innarsa da kansa”. Hawayen dadi ya sake kecewa Hauwa, don ita ai tayi-tayi Inna ta yarda ta zauna a asibitin Murtala a cigaba da dubata ta ki, tace in mutuwa ce ta isko ta, a barta ta mutu a cikin dakin ta yafi mata, ta fi so ta mutu a gida akan gadon asibiti, kada taje a kai gawarta mutuware a ajiye a firinji, a kuma jinkirta yi mata janaza. Kuma ita har gobe bata yarda da maganin asibiti ba, don bata ga ranar da ya yiwa idanun Kulu ba, aikin Kulu yasa ta kara nesanta kanta da asibiti, dama dole ce ta kaita a kan Hauwa dinma, shi yasa tunda ta fara ciwon nan suke dambarwa ita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36