Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sabon darasi Hauwa zata cafke, musamman da yake akwai kishin abun a ranta da kulafucinsa, hadi da tsoronta na zama MABARACIYA saboda rashin ido. Hauwa ta jajirce, ko barci bata yi kullum ta dawo zaka samu tana karatu da Braille, har sai Inna ta kwace littatafan ta, ta kashe fitila, ko ta ce, “karatun ya isa haka, dare mahutar bawa ne”. Ba jimawa da komawar ta makaranta aka yi jarrabawar kwalifayin, aka yi hutu, wanda in sun koma su Hauwa zasu shiga aji shidda na sakandire. Sakamakon jarrabawar qualifayin din ta lokacin da ya fito, yafi na kowa a makarantar kyau, yafi na kowa daraja, komai nata daga ‘A’ sai ‘B’. A lokacin kam makerin budurci ya gama kera Hauwa Bilyaminu, da ka ganta kaga kyakkyawar bakanuwar budurwa, mai samun kulawar Uwa da tsaftar jiki da abinci mai gina jiki, yadda ya kamata. Kafin su Hauwa su koma hutun da zata fara aji shidda suka bar sayar da abinci a tashar kuka, suka dawo sayarwa a tashar Kano-Line, ba don komai ba sai don yafi kusa da makarantar Hauwa kuma samarin tasha sun fara son matsawa Hauwa a can tashar Kukan, da cewa suna son ta har da masu neman ta da sakarci, duk da idon uwar ta kuwa. Wannan ya tadawa Inna hankali ba kadan ba, ta ga dole su bar tashar kuka zuwa inda basu saba da kowa ba. In yaso ta hakura da ko me take samu a tashar don kare mutuncin Hauwa. Don da yawa suna amfani da sabo da mutuncin dake tsakanin su da Innar ne, su soko mata zancen suna son Hauwa, sabida kirkin Inna da yadda ta ke sakarwa kowanne kwastomanta fuska yasa take da jama’a, yawanci matafiya da masu shigowa Kano ta tashar tasu da direbobi dake cin abinci wajen ta. Ga ita Hauwar kam! Ai duk iya rashin kunyar mai zuwa cin abinci teburin su, bai ma isa ya tunkare ta da wata magana wadda ba ta sayen abinci ba, don babu fuska sam. Zata iya wuni bata yi koda murmushi ba. abinda Kawu Zakari yayi musu yayi mata illah a zuciya sosai ya rage mata walwala. “Hauwa-Kulun–Majadun” kenan. Duk da cewa bayan sun dawo tashar Kano-line sun kama gida a unguwa uku shima mai daki biyu ne, amma sun fi ciniki sosai a tashar kuka, wani ko ba don Allah ba zai sayi abincin Inna a tashar kuka saboda daukar hankalin sa da makauniyar ‘yar nan tata tayi, wadda ke taya Innar ta aikin abincin da sayar da shi wa masu bukata da zarar ta dawo makaranta. A wancan lokacin Hauwa ta gama isa aure har ta na neman wucewa don gab take da zana jarrabawar fita sakandire wato SSCE, ta samu damar da ‘yammata da yawa a zamanin basu samu ba, saboda da sun fara makarantar ake cire su ayi musu auren wuri, amma Inna bata bada fuskar da wani zai zo mata da zancen son Hauwa ba kwata-kwata, itama Hauwan ba fuska ko kadan. Don kullun Inna na gaya mata “da tun farko baki baiwa Jamilu fuskar zuwa inda kike da sunan neman aure ba, da har yanzu muna zaune gidan mu cikin sutturah, rufin asiri da kwanciyar hankali, da yanzu bamu zama masu sayar da abincin tasha ba”. Sai Hauwa ta cuno baki gaba tace cikin kunkuni “to Inna Yaya jamilu ba dan uwana bane? Duk kin bi kin tsani Yaya Jamilu, kamar shine Baba Zakari, ina laifin sa? Halinsa daban na uban sa daban”. Inna ta kama baki, ta bude shi ta mayar ta sake rufewa cikin al’ajabi, wai ta san soyayya, ta ce “hakane, dan uwan ki ne, na jini ma kuwa, amma wallahi ki sani ko shi ya saura da namiji a duniya, kema kika saura diya mace a duk fadin duniyar nan in dai ni SAFIYA ni na haife ki, kuma ina raye, to baza ku yi aure ba, ke ko ina gargarar mutuwa zan bar wasiyya ga duk wanda na samu cewa ba zuri’a ta babu ta Zakari”. Hauwa aka kumburo baki sai ka ce zumbutu ta ce cikin wani sabon kunkunin “to ai ni dama ban sa aka ba, in dai maganar aure ne Inna, kawai na san ba’a raba hanta da jini, Yaya Jamilu dan uwana ne dana ke kauna tunda ba wani jini na da ya taba nuna min kauna bayan shi, kogobe na kara ganin sa In sha Allahu zan kula shi, zan tsugunna har kasa in gaida shi don bana manta alkhairin da yayi min, kuma bani da masoyi duk duniya bayan ke irin sa”. Inna ta harzuka, yau akan Jamilu tana fade Hauwa na mayar mata? Tace “hantar taku sai in ba’a saka mata soson karfe da farin omo da sabulun dan jangabo ba, tuni in taji karta jinin zai rabu da ita koda zata kukkuje ta karce, wawuya kawai, mara kunyar wofi. Ke na bi zumuncin naku da soyayyar taku da gudu na tattake su ba takalmi a kafata!”. Hauwa sai ta kama dariya ta ce “tsakani da Allah Inna ban san ki da dorawa mutum laifin da ba nasa ba, duk da haka Inna Allah ya huci zuciyar ki, ni ba bakuwar zafi bace a kan Yaya Jamilu, ina ni ina wani aure alhalin ba ido? Kawai ina son Yaya Jamilu a rai na, kasancewar duk cikin ‘ya’yan Baba Zakari wa ya taba nuna min zumunci da kauna ta fisabilillahi idan bashi ba? Kiyi tunani Inna, ki rage kin Yaya Jamilu, laifin Baban sa ne ya shafe shi, yasa kike ganin bakin sa. Shiyasa kome zai yi bazai burge ki ba, tunda Baba Zakari ya riga ya shafa masa, amma ko kadan bashi da laifi”. Haushi ya ishi Inna, tayi mata shiru ta rabu da ita ta kaiwa banza ajiyarta, don ta dade da sanin in za’a kwana ana kushe Jamilu, to kuwa Hauwa bazata gaji da kwana a hanya tana kare shi ba. Rayuwa ta mikawa Hauwa da Innar ta cikin rufin asirin Allah a tashar Kano-Line, inda suke gudanar da sana’ar su. Har gashi yau Hauwa sun fara zana jarrabawar WAEC wadda aka fi sani da SSCE a wannan watan da muke ciki. Wadda da zarar sun kammala ta, Hauwa tayi sallama da makarantar kwalejin ilmi na musamman. Tunanin Hauwa kullum a yanzu shine, shin ko yaya rayuwa zata kasance mata bayan kammala sakandire? Tunda dai Innarta ta ce bazata taba yi mata aure kamar kowacce mace ba wanda shi tafi bukata a wannan matakin? Ta sani ba don komai Inna take wannan kaffa-kaffan da ita ba, sai don kare mata martaba da mutuncin ta, har ma da tattalin kwanciyar hankalin ta, Inna tana bata kariya ne daga shiga matsalar gidan aure alhalin tana fama da wannan nakasar mai girma. Har ila yau, Inna tana guje mata shiga jami’a ne domin bata kariya daga fadawa ga soyayyar duk wani namiji da zata wahalar da ita a matsayin ta na karamar yarinya kuma mai raunin halitta na nakasar idanu, wadda har yau bata kai ga cika shekaru ashirin da haihuwa ba. A wannan gabar da Inna ta san aure ne kadai ya ragewa Hauwa-Kulu, kuma ta fahimci tana ra’ayin yin sa da dan uwanta Jamilu ko bata furta ba, to bazata taba bari

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});