Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Shi yasan inda abinda iyayensa ke so su ji a yanzu to bai wuce yayi aure hakanan ba, iyayen sa sun matukar daga hankalin su a kan rashin auren sa a wannan dan tsakanin ya rasa meyasa, ya manta shekaru talatin da biyu a wancan lokacin har ya wuce matakin samartaka, ya shiga na tuzuranci a al’adance, har hakan na neman ya shafi zaman lafiyar sa da su, don Mama ta dade da daina kiran sa a waya tace yayi abinda yake so tunda ya badawa idon sa toka ya ki auren diyar aminiyar ta Barr. Hannatu wato Sadiya Maijama’a, har wani ma sa’ar yayi wuf da ita (ya aure ta). A yanzu kam Dr. Sarham Abbas yana cikin wani farin ciki maras misaltuwa. At last, at very long last, he found his first and true love, bama mai kama da ita ba, ba mai irin kokarin ta ko kamanninta ba (kamar yadda Mama tai masa fata), a’ah, ita din ce da kanta ba sako ba, wato (his ex) Madinah Attahiru ba wata ba! Kuma har sun daidaita sabanin dake tsakanin su, duk tsayin wannan lokacin na komawarsa Jeddah suna tare da Madina Attahirusun sake hadewa acan jami’ar sarki Abdul Azeez (KAU) Jeddah. **** ***** **** WAIWAYE ADON TAFIYA (1) (DR. SARHAM SHANONO A JEDDAH) Abinda ya faru shekaru ukun baya shine tun saukar sa a birnin Jeddah cikin wani ikon Allah suka hade shi da ‘ex’ dinsa Madinah Sorondiki a cikin asibitin koyarwa na ‘KING ABDUL’AZEEZ’, inda duk a can ne dukkansu suke kara zurfafa karatu. Ba zai manta ba kwanansa uku da zuwa ranar nan ya zo wucewa, kamar daga sama ya hangi Madina Attahiru tana shiga wata farar mota kirar ‘Audi’ don fita daga asibitin. Sarham ya mutstsika idon sa, don da farko ya dauka gizo idon nasa yayi masa, irin wanda dare da rana ya saba yi masa a kan ta, har saida ya dinga neman taimakon Ubangiji da sallolin dare kafin ya samu Madinah ta daina yi masa gizo a kowacce kusurwa ta dakin sa. A ranar da yayi mata wannan ganin a asibitin kusan karamin hauka yayi, bai iya yayi barci a daren ranar ba ko na minti daya, ‘fade memories’ na komai nasu a can baya ya dawo masa sabo, ya dawo da tsohuwar Madinah sabuwa a ran sa. Amma a washegari da ya sake ganin ta, sai ya kuma tabbatarwa ba gizo idon sa ke masa ba, Madinah ce. Har yau bayan rabuwar shekaru bakwai, tana nan a Madinah ‘yar gayun ta. Fara, doguwar nan sambaleliya da ya sani hamshakiyar ‘yar hutu. Madinah siririya mai yalwar gashin ido dana gira, ta kara tsayi da cikar halitta, ga sabon aji na musamman data kara a kan wanda ya santa da shi a baya, ko dama can Madina classique lady ce balle yanzu da ta ke kusan shekaru Talatin. Tana takunta akan kasa cikin rangaji da rangwada tamkar basarakiya, tabon sallahr nan har yau yana nan a kan goshin ta, ya kara fitowa radau, shi ya kara tabbatar masa har gobe tana nan a “Madinah” mai yawan ibada. Madinah (Munawwararsa da ya sani) tuntuni mai aji ce, iyayenta sun wadatata da komai na bukatar rayuwa, balle yanzu da ya san ko yaya ta zama babbar likita tana aikin kanta kuma kallo daya zaka yi mata ka san hankalin ta a kwance yake, tana neman cika shekaru talatin. Abinda bai sani ba shine tana da aure ko bata da shi? Wannan tunanin, da kuma sanin halin mahaifinta da yayi, su suka sa yayi maza ya shiga taitayinsa, ya soma yaki da fade memories masu neman dawowa muhallinsu saboda ganinta. Sosai ya kama kan sa, bai bari ma ta san ya gan ta ba har bayan sati guda da ganin da yayi matan. Amma wani coincidence din, ashe ajin su daya a wannan karon ma, itama ta zo yin irin kwas din da yazo yi, duk a specialization nasu na ‘ophthalmology’. Bayan kwashe shekaru biyu tana practicing aiki a Dr. Siddiqah Hospital anan Jeddah. Ranar da yi mata gani na biyu da yamma ne, ya je shan Gahwah (coffee) a wani Mud’am dake cikin asibitin koyarwar nasu na Sarki Abdulazeez, bayan ya gama sha, ya tashi ya nufi kantar biyan kudi, ya zaro khamsoona riyals dinsa daga aljihu zai biya, kawai ya ji cashier din ya ce ai an biya kudin gahwar da ya sha. Ya juya cikin tsanaki da mamaki, nan yayi ido hudu da Madinah Attahiru, his ex Madinah Sorondinki, tana masa kallon ashe kana duniya? Zuciyar sa ta harba. Makwallaton wuyan sa ya motsa, amma ya kasa hadiyar miyau. Donhaka wani abu ya tokare a wuyansa. Madinah muguwa ce ta karshe ya sani in dai akan soyayyah ne, idan ta samu dama zata iya kisa, har lahira kuwa, don haka nisa da ita shi ya fi wa bawa kamarsa kwanciyar hankali. Juyawa Dr. Sarham yayi cikin daure fuska kamar bai san ta ba, ya soma takawa don barin mud’am (restaurant) din gabadaya. Madinah ta saki malalacin murmushinta, ta riga ta san halin kayanta bashi da jarumta in dai a kanta ne, tanada yaqinin bazata sha wuya ba wajen dawo da shi ruwa tsundum cikin soyayyah. Ba da sanin sa ba Madinah har sujjadah ta fadi ta yi a nan inda take zaune, (for the second phase) na rayuwarta ta sake haduwa da Sarham Shanono, a muhallin da ta fara haduwa da shi a can baya. Ta tako cikin kasaitar ta har inda yake tsaye yana shirin barin wurin shan coffee din, ba tare da ko an gode yace ba, daga abinda aka biya masa. Madinah ta sha gaban sa, ta kashe shi da murmushin nan nata kamar na koren furen fulawa, da ya dade da daina gani, zuciyar sa kuma bata bar mararin ganin murmushin ba all those years, Madinah ta ce, “ai in da alkawari zai zamanto cewa ko gaisuwar musulunci ce akwai a tsakanin mu Dr. Sarham, idan ta SO da KAUNA ta gushe ko tayi fading, a matsayin mu na dalibai duka, sannan ‘yan kasa daya kuma ‘yan aji guda, dana tabbatar abinda nazo yi shi ka zo yi, ba laifi bane don hanya ta hada mu mun tsaya mun yi gaisuwar musulunci”. Wannan karon ma bai yi niyyar bata amsa ba yasa kai zai wuce abinsa, a ran sa yana fadin “Allah ya shiga tsakanina da ke Madinah! Mumini na kwarai sau daya maciji yake saran sa a rami guda”. Amma sai Madinah bata yi fushi ba, ta sake shan gaban sa. Ta ce, “Assalamu alaykum warahmatullah wa barakatuhu!” Kamar yadda ta dade da sani, Sarham Abbas nada wani hali daga halaye masu kyau, wato baya iya maida gaisuwar musulunci a kwandon shara, ta hanyar kin amsata, wato duk inda ya ji ta sai ya amsa koda ba da shi ake ba, ba don komai ba sai don cika sunnar Manzo SAW. To yau ma hakan ce ta faru kuma yanzun ma. Sarham ya kasa kin amsawa don cika umarnin addinin musulunci, sai ya ce kasa-kasa kamar yaci madaci, “wa alaykumus salam warahmatullah wa barakatuhu”. Daga wannan sai aka shiga kallon-kallo, koko in ce ‘kallon kuda’ kallon debe shakku ko debe tsammanin gizo ido ke yi, kallo ake babu

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});