Chapter 4
Chapter 4
Hauwa ta kai kanta ga kowacce matsala ba. Da dukkan karfin ta zata kare Hauwa-Kulun ta daga duk wata soyayyar da bazata yi mata amfani ba. Inna tayi wa kanta alkawarin bazata bar Hauwa-Kulu taje jami’a ba, koda tana da ido kamar kowa, balle kuma BABU! Bazata lamunci shigar Hauwa jami’a bane don kada a gurbata mata tunani, ko kuma wani da yafi Jamilu iyawa ya hilace ta ya hure mata kunne, a karshe ya saka ta a matsalar da bazata iya fiddata ba. Tana da yaqinin yadda Ubangiji Subhana ya nufe ta da yin ilmin sakandire ba tareda dabararta ba, ya kuma tsara mata yin rayuwa cikin nakasa ba tare da ta tagayyara ko ta tozarta a dalilin nakasar ba, (kamar yadda dan uwan mahaifinta ya so su wulakanta), sannan rashin mahaifinta tare da ita duka bai sa sun kasa numfashi da motsi cikin kudurar sa cikin duniya ba, ta tabbata shi din dai sarkin wannan kudura da iradar wato (Ubangiji Subhana) bai manta da it aba, shi zai cigaba da tsara mata sauran rayuwarta ta can gaba, kamar yadda ya tsara ta baya ta hanyar da bata taba tunani ko tsarawa kanta ba, tunda shi dai Ubangijin KOWA. In tace KOWA tana nufin KOWA, har da ita HAUWA-KULU! Abin nufi anan, daga mai lafiya har mai nakasa duka nasa ne. shi ya halicci abunda yadda ya ga dama wato “Fa’alun lima Yureed ne”. Shi din, (Ubangijinmu), mai yawan hikima ne ga rayuwar duka bayinSa. Bai kuma halicci wani a mai nakasa wani a mai cikar lafiya don baya son dayan ba, ko don ya kaskantar da shi cikin bil adama, ko don ya saka shi cikin bakin cikin rayuwa mara yankewa, kamar yadda ya dade da fada mata ne; “Nakasa ba komai bace face jarrabawar Imani ga wasu daidaikun bayin Allah - (LIKITA SARHAM)”. Idan haka ne kuwa zata tsaya tsayin daka wajen ganin cewa ta cinye wannan babbar jarrabawa da DR. SARHAM ya kwadaitar da ita muhimmancin cinyeta da TAUHIDI da IKHLASI (ta bakinsa), daga yau ta daina fito na fito da Innarta akan Yaya Jamilu, daga yau zata yi wa mahaifiyarta biyayya irin wadda wani da bai taba yi wa Uwarsa ba (koda ya san abun da take so din ba daidai bane), ita HAUWA_KULU zata yiwa Inna biyayya kan jiki kan karfi, akan duk abinda take so da ita da rayuwar ta, musamman hakura da rayuwar aure domin tserar da kwanciyar hankalin su. Ta san Inna tana yi ne don amfanin ita Hauwan ba don nata amfanin ba. Hauwa-Kulu ta cigaba da gayawa kanta daga yau ta cirewa ranta burin yin aure kamar kowacce mace mai lafiyar yinsa, ta barwa Allah ikonsa a kanta, ta daina yarda zuciyarta na kwadaita mata Yaya Jamilu, kai dama duk wani Da namiji bayan shi da zai biyo hanyarta, ta yarda da nakasarta babban gibi ce da zata hanata jin dadin rayuwa ta wani bangaren, ta kuma karbeta hannu bibbiyu, ta yarda nakasar ido bazata bata damar yin abinda ke kira “MARITAL LIFE” da “MOTHERHOOD” ba, wadanda sune ginshikin rayuwar kowacce diya mace, kuma su suka fi komai dadi da muhimmanci ga rayuwar kowanne dan adam. **** **** **** (A GIDAJEN MALAMAI NA SABUWAR JAMI’AR BAYERO). G idan Prof. Abbas Shanono ya kacame da hayaniya a tsakanin jama’ar gidan da kawayen ‘ya’yansu da jama’ar mahaifiyar su da aka gayyato domin taya Surayyah Shanono, murnar kammala digirin ta na farko, bayan dawowar su daga filin ‘convocation’ na cikin jami’ar Bayero. Anan cikin gida bayan kawayen Surayyah sun gama dabdalar su sun tafi, Mama ta hada musu (get together party) su’I’su, domin kwarai tayi alfahari da sakamakon Surayyah, koda yake abin kamar a jinin ‘ya’yan ta ne, in dai ta fannin karatun boko dana addini ne basu da na biyu. ‘Get together party’ din da Mama Mai Shari’ah Haj. Maimuna ta shirya na abu biyu ne; bayan taya Surayyah murnar kammala karatunta da kyakkyawan sakamako (first class degree) ya kuma kunshi sallama da auta Sumayyah, wadda ita kuma zata tafi Jeddah nan da kwana uku domin fara nata karatun, can a jami’ar da Abba Prof. yayi mata alkawari tutuni, wato Sumayyah zata tafi inda Bhaiyanta (SARHAM) yake itama a cikin satin nan da yardar Ubangiji. Tsananin kaunar juna irin na wannan family, da yadda basa yin wani abu babu sanin dayan su, yasa sun kasa cika farin cikin ranar yau ba tare da shi ba, musamman da ya kasance a lokacin wayar zamani ta tafi da gidan ka ta fara yawa a Najeriya (amma dai ba a kowanne gida ba), to shima dai Abba Prof. kamar sauran manyan ma’aikatan gwamnati a Kano ya mallaki tasa, har yana arawa iyalin sa lokaci-lokaci su kira dan uwan su dake nesa su gaisa. To yau ma hakan ce ta kasance. Sumayya ta ce “Abba ka kira mana Bhaiya ayi komai ‘live’ a kunnen sa”. Abba yace “kin manta Sarhamu jarrabawa yake yi?” Sumayyah ta hau roko “Abbah don Allah, ko na minti biyu ne, bazan ja shi da surutu ba”. Surayyah kuma ta ce “Abbah ni zan biya ka kudin da zamu cinye maka a wayar”. Abba Prof. yace “da can dana ke baku aron wayar kuyi wayar da shi biyana kuke yi?” Suka hada baki wajen cewa “tuba muke Abbanmu! Abbanmu like no other Babanmu maganin kukan mu”. Prof. yayi dan murmushi kafin ya danna masa kira, ba jimawa Sarham ya amsa masa da cikakkiyar amsa sallama, da muryarsa dusassa, wadda a kullum yanayinta kamar na mai fama da mura. Sarham yace (cikin hausar shi wadda yanzu ta daina fita sosai yadda ya kamata). “Daga bangarena ina kokarin kiran ku ne fa Abba, naka kiran ya shiga nawa shiga, in ban manta ba yau ne graduation din ‘Surry Darling”. Surayya ta saki dariyar farin-ciki jin yau wai Bhaiya ya kira ta da ‘Darling’ tana fadin “yau kuma?” Shima daga nasa bangaren dariyar yayi, yace “Surry rigima, Surry masifa Surry mathematician, Surry Darling!”. Duk falon aka kwashe da dariya da alama yau dukkansu cikin nishadi suke, abinda basu sani ba ya fi su nishadin wannan ranar, domin tayi daidai da ranar zagayowar haihuwar sa, kuma a daidai lokacin wani babban abun farin ciki ya same shi, wanda daga shi sai Allah suka san shi, wato wani ‘gift’ ne na musamman na taya murnar zagayowar ranar haihuwa Madinah ta kawo masa... Don haka don yau ya kira abokiyar fadansa da ‘darling’ bai ji faduwa ba ko kankani, karewa ma, har shirin fita ‘outing’ (picnic) na musamman ya yi niyyar shirya mata shima idan yazo, ko a TIGA DAM ko a DAMBATTA DAM, inda suka saba zuwa don ‘celebrating’ wasu ranaku masu muhimmanci da suka shafi dayan su. Sannan kuma gashi yana shirin ‘surprising’ dinsu su duka, domin a lokacin ya riga ya yanki tikitin tahowa gida kwatakwata, ba tare da ya gayawa kowannen su ba, tuni kuma yayi ‘booking’ din jirgin dare, bayan kwashe shekaru uku yana zullewa Mamansa Haj. maimuna, a kan dai maganar aure. Yanzu kam da kwarin guiwar sa zai iso gida, kuma da abinda ya tabbatar zai baiwa kowa a gidansu kwanciyar hankali, abinda ya tabbata zai faranta ran Mama, ya kuma wanke bacin ranta da shi, wato maganar auren sa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36