Chapter 33
Chapter 33
fara kal, wadda aka yi rubutun ‘Dolce&Gabbana’ a jikin ta, da bakin Trouser ne na ‘Tokyo Jeans’. Kansa babu hula, sumar nan tasa baka wuluk ta fulanin Shanono ta cika kan sa har ta nannade (curl), a kafafun shi bain takalmi ne sau ciki na bakar fata kirar Italy. Da farko he was shocked, da ganin Hauwa tsaye da namiji a zaure, da abinda kunnuwansa suka jiye masa Jamilu na fade, da kuma yanayin da yaga Hauwa wanda kiri-kiri yana nuna tadin soyayya. Amma da yake shi din shine Sarhamu, sai ya bagarar, yashare, ya hadiyefirgicewarsa yayi kamar bai ji kalaman Jamilu ba, yayi musu sallama da dusassar muryarsa ya kuma baiwa Jamilu hannu suka yi musabiha, ya dan kalli Hauwa yana mamaki yana karawa, sannan ya shige cikin gidan. Inna ta rako Babar Jamilu zata tafi suka yi kacibusa da shi yana shigowa tsakar gidan, kafin Jamilu ya samu zarafin tambayar Hauwa ko wanene shi ya isa dakin Inna, shigowarsa tasa hankalin Inna ya koma kansa, a gurguje suka yi sallama da Haj. Rumanatu ta wuce, bayan ta tabbatar mata cewa kwarai ta fahimce ta, zata yi iya yinta wajen lallashin Jamilu ya hakura, ko don kwanciyar hankalin Inna da zaman lafiyar su da Babansa dan jidali (Zakari). Sarham ya zauna a falon Inna yana jiran ta har ta shigo ta zauna akujerar dake fuskantar sa, suka gaisa, sai ya koma cikin kujera ya kishingida yayi shiru, har da dan juyawa ya kalli taga yaga ko Hauwa taji kunyar idonsa na abinda ya tarar tana yi (soyayya) tayi maza ta baro saurayin ta shigo gida ko a’ah? Amma ina! Ko keyarta bai gani ba, tana can suna sallama da Jamilu kamar bazasu rabu ba, Sarham ya mike dogayen kafafunsa a kasa. Bai iya kara cewa komai ba don al’ajabi da mamakin Hauwa. Can jimawa sai ga Hauwa ta shigo, tana tafe abunta kanta tsaye, babu ko lalube irin na makafi, tsabar ta gane hanyar dakinta, tasa kai zata wuce dakinta taci uban tuntube da kafafun Sarham, saura kadan ta kifa ta ci da baka. Ko sannu bai mata ba balle yayi ‘apologizing’. Cikin fushi tace. “Inna wa ya saka min kafa zai kayar da ni haka?” Inna ta yi mata shiru, kafin tace “daga ina kike?” tace “Yaya Jamilu ne ya kira ni soro”. Haba! Sai Inna ta balle da fada kamar ta rufe ta da duka, cewa take “da iznina kika fita zance gun Jamilu? Kece da zuwa zance Hauwa da wane idon zaki ga saurayin?” Saida Dr. Sarham yace “ya isa Inna, kinsan kinada matsalar zuciya, kada ki dinga bata ranki irin haka kan kananan abubuwa har ya tabo zuciyar ki”. Hauwa ta wuce dakin ta a sanyaye, bayan ta gaishe shi. Dr. Sarham yaki ko amsawa balle ya nuna ya san tana gaishe shi, har ta wuce tana mamakin me ta yi wa Dr. Sarham yau? Gashi dai yau bai kira sunanta da yake mararin kira na MAIJIDDAH cikin farin-ciki, yalwar fuska da far’ar nan tasa ba, bai kuma amsa gaisuwar ta da kulawa da (attention) kamar yadda ya saba ba. to me ta yiwa Likitan Inna? Ji yayi gabadaya yau ya kasa zama ya dade a gidan yadda ya saba, ya kuma kasa hira da Inna yadda suka saba, ita kadai take ta babatunta, daga karshe da Inna taga shirunsa yayi yawa sai ta dago ta dubeshi tace, “ko lafiya kake kuwa likita? Na ganka ba’a yadda na saba ganinka ba”. Sai kawai ya mike yana cewa “bari in karasa gida Inna, kaina ke min ciwo, yanata sarawa, idan na ji sauki zuwa gobe ko jibi in sha Allah zan shigo”. Inna tace “ni ai ban sani ba, gashi har nayi maka tuwon Acca kuwa, da miyar da kake so ta zogale” Sarham ya juya a lokacin yana saka takalman sa a bakin kofar falon, yace “ba komai Inna, some other time, zan ci”. Suka yi sallama dukkansu jiki babu kwari ya juya ya tafi. Ko sallama bai yiwa Hauwa ba. Yana tuki yana hada gumi kashirban, duk da sanyin AC din motar sa. Abun ya daure masa kai matuka. Ya kuma sakashi a damuwar da ya kasa sanin ma’anarta. Yana isa gida yaji ana murnar zuwan Sumayyah, wadda ta zo hutun karshen shekara da barkar haihuwar Waheedah. Kamar bai ga Sumayyah ba, bayan kuma har ido sun hada a falon, ya dauke kai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa bayan yace musu cikin jam’u “sannun ku da gida”. Mama ta bi shi da kallo, Sumayyah kuma ta ce. “Bhaiya lafiya kalau yake? Kaamr bai ganni ba Mama?” Mama ta ce “oho muku, kun fi kusa”. Surayyah ta ce “nafi tunanin wani ne ya bato masa rai daga waje, baki ga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ba?” Sumayyah sai ta mike ta bi bayan sa zuwa dakin nasa. Sallama tayi daga bakin kofa, sai da ya bata iznin shiga ta shiga dakin ta same shi zaune akan ‘study chair’ ya rafka uban tagumi, ta ce. “Bhaiya baka ganni bane ka wuce bamu ko gaisa ba?” Ya dago ya dubeta da jan ido, a lokacin taga idanuwansa sun kada, yace “a’ah Summy ce yau a gari? Saukar yaushe?” Tace tun dazu na sauka, ta gabana fa ka wuce, har ido mun hada, ka san mun yi hutu shine fa nace bari kawai in taho ganin Hauwa’u”. Ta zauna a kujerar ‘sofa’ kwaya daya dake dakin, ta ce “Bhaiya duk ka birkice, you are upset, anya lafiya kake kuwa? Na ganka ‘moody’ tunda ka shigo”. Yace “Sumayyah, bansan yadda zaki fassara abinda ya sani a damuwar ba idan na fada miki, ba wani abu bane serious I don’t know why I made it serious, abun ne ya bani mamaki, ya kuma bata min rai, wai Hauwar nan da kika sani ko ido bata da shi, amma ta iya tsayawa zance da saurayi a soro??? Ni ban taba ganin abinda ya bani mamaki ya rikitani irin wannan ganin dana yi ba”. Sumayyah tana sane tace “Hauwa wacce? Baby Hauwan mu?” Ya harareta, “ke bana son sakarcin banza. Hauwa ‘yar Inna mana, kanwata ta kofar Na’isa” Sumayyah ta wani ce “au ho! Ka ce min kawai Hauwar Inna, HAUWA-KULU ‘yar cikin BADALA!”. Sai ta hau tuntsira dariya tace “Bhaiya, yanzu ganin Hauwa da saurayi shine abinda ya birkita ka haka?” Sarham ya harareta yace “Sumayyah yaya ina miki magana ‘serious’ za kina dariyar rainin wayo, Hauwa fa, wadda ko ido bata da shi, ina zata kai wani namiji da sunan soyayya? Ganin ta nayi da wani cousin dinta suna zance fa, zance na saurayi da budurwa! Wai sunan sa Jamilu, dan kanin Babanta ne”. Ai kuwa Sumayyah ta kara tuntsirewa da dariya sai da tayi mai isarta, shi kuma ya shaka sosai, saida dariyar ta lafa mata ta ce. “Bhaiya makaho ba mutum bane? Ko kuwa makaho bai san SO da mai son sa ba? Don tana makauniya shikenan sai akace bazata yi aure ko soyayya ta ji dadin rayuwar ta kamar kowanne dan adam ba? Ko in bata saurari masu son ta ba kai din auren ta zaka yi? Yau nake ganin ikon Allah, yau ina ganin abinda ya gagari Kakata Kulu, kai ka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36