Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ko kiftawa haka babu kakkautawa tsakanin SARHAM DA MADINAH. Suka yi wa juna kiriii da ido. Kallon da ya dawo masa da duk abinda ya faru cikin shekarun soyayyar kurciyar su kan idon sa, koko ince, kan idon kowannen su, komai da ya gabata (in the past) ya zo yana gilmawa a idanun kowannen su, tamkar yadda sinasinai ke wulgawa a majigi, suna tariyo kan su, suka kuma shiga warware tsohon kullin dake zuciyar Sarham akan Madina, tamkar ana tariyo tsohon kaset na faifan bidiyo. A hakikanin gaskiya Sarham na kullace da Madinah kullata mai yawa, wadda ta janyo ya maida kansa ba namiji ba, ta hanyar daina sha’awar soyayya da sha’anin mata gabadayansu. Madinah tasa ya hada su itada sauran matan duniya yayi musu kudin goro da cewa dukkansu maciya amanar kauna ne, kuma basu san darajar soyayya ba, mata irin Madinah in ka bari ka fada komarsu zasu iya kashe ka har lahira akan soyayya. Yana tuhumarta ne da rashin alkawari da cin amanar kaunar da suka yi wa juna. Son data ke ikirarin tana yi masa yayi ittifakin ko kusa bai kai rabin nasa ba, shiyasa ta iya bari har aka raba su cikin matukar sauki haka, kamar kwace goriba a hannun kuturu. Abu daya ya sani kuma yake da tabbacin sa; Madinah Attahiru, bata taba raina shi ba, wai don shekaru biyu ko uku kawai ya bata a haife, Madinah bata taba raina arzikin mahaifin sa ba, wai don bai tara dukiya kamar nata mahaifin ba, baya ga kasancewar sa malamin makaranta/malamin jami’a. Yana son Madinah har gobe, domin ta hada duk wasu halaye na kwarai da nagarta da kyawun sura dake sawa a so mace, a yi mata So na musamman. Duk wasu ‘attributes’ da yake so a matar aurensa Madinah ce ta hadasu ita kadai ranta. Ya ci buri mai yawa a kan Madinah Attahiru, haka ya sha wahala lokacin da ya rasa ta farat daya. Haduwar su ba zato a yanzu, karo na biyu cikin shekarun girmansu, a lokacin da suke da cikakken hankalin su bata nufin komai sai fami a kan gyambon da riga ya warke. Kafin wannan lokacin sun yi alkawarirrika masu dimbin yawa shi da ita, kai har yawan adadin ‘ya’yan da suke burin haifa ra’ayin su ya zo daya, wato ba masu yawa ba, shi da Madinah kamar Lailah da Majnoun ne. Daga cikin manyan alkawuran su na can baya, har da na yin aure daga zarar sun kammala MBBS, koda basu samu ayyukan yi ba a Jeddah, sun ajiye a ransu zasu yi ko ayyukan philanthropy ne a private clinics na Jeddah don rufa asirin juna indai zasu rayu tare. Rana daya Madinah bai san ya aka yi ba, bai san me ya faru ba Madinah ta yarda mahaifin ta ya ci zarafin sa, ya kuma canza mata makaranta, duk dai don ya raba su, ya rasa mai yasa Baban Madinah ya ki jinin sa ya kuma raina arzikin su shida iyayensa har haka, tunda daidai gwargwado iyayensa nada abin yin su, da rufin asirin su basa nema a hannun kowa, ko da yake ya taba gaya masa fuska da fuska; “me na sama ya ci bare ya baiwa na kasa? Kuma yayi yarinta da auren ‘yarsa a lokacin” Shine kawai hujjarsa. Babban laifin da Madinah ta yi masa shine, bayan an canza mata makarantar, bai kara ji daga gareta ba, Madinah bata kara waiwayarsa ba, bata kara neman sa ba, koda da gaisuwar zumunci ne. Ai yasan Madinah nada email adireshinsa, da adireshin sa na gidan wasika, da lambar talfon din gidan su, amma ko sau daya, bata taba tunanin gwada neman sa ba, wanda ke nufin ta datse duk wata alaqar soyayya da sanayya dake tsakanin su. Koda ba don maganar alkawarin aurensu ba, ai ta nemi inda yake ta ji yana raye ko ya zarce ta dalilin kisan gillar soyayar da suka taru suka yi masa itada mahaifin ta, tunda dai ta kwana da sanin irin son da yake mata, ba irin wanda zai gushe farad daya bane. Wannan shine babban laifin da Madina tayi masa da ba zai yafe shi ba wato kin neman sa ko sau daya cikin shekaru bakwai da rabuwarsu, tun bayan komawar ta Yamboa inda a can tayi nata consultancy din, tsayin shekaru biyar, da komawar sa shima zuwa gida Najeriya na dan wani lokaci, inda daga baya ya dawo shima yayi consultancy dinsa ya sake komawa gida. Wanda ya yi shi ne da kyar da sudin ludayi shikadai a [KAU] a dalilin rashin Madinah tare da shi. Saboda tunda suka fara MBBS suke tare, har zuwa karshen sa. Karatun dukkansa, da aikin gida (assignment) da halartar lacca duk tare suke yin komai. A lokutan jarrabawa kuwa duk zaka same su tare a library, sun dukufa basa komai sai fatan isa ga ‘goal’ din rayuwarsu. Don haka shekaru goma kenan ya kwashe a cikin hidimar dakon son Madinah Sorondinki, idan har lissafin sa daidai ne; yayi shekaru biyar tare da ita cikin fafutukar hada MBBS, shekaru biyar kuma cikin jinyar soyayyar ta, lokacin da yake consultancy, tun bai san so ba akan Madina ya koye shi, wato tun farkon tashen balagar sa da soyayyar Madinah ya budi idanu. Wannan shine tarihin soyayyar su shi da Madinah wanda ya tuna a wannan ‘yan dakikan da suke kallon debe tsammani shi da ita. **** **** **** Da tunanin sa ya zo nan, sai ya dauke kai daga kallon kudar da suke yi wa juna, ya juya da zummar cigaba da tafiya ya bar ta a wurin, ba tare da ya kara tankawa ba. Madinah bata yi fushi ba, ta hakurkurtar da ranta da cewa fushin fari ba nata bane, Allah na nufin su da wani al’aamri maigirma da ya sake hada su (at appropriate time), ta sake biyo bayan sa jiki babu karsashi, yana saka kafa tana mayas da tata duk inda ya cire tasa, cewa tayi cikin muryar dake raurawa. “Sarham, yaya bayan rabo?” Cikin dakiya da tsare gida yace “bayan rabo kuma? Sai tarin alkhairi” “Kamar baka gane ni ba?” Madina ta fada kamar zata fashe da kuka wannan karon, idanun ta na kallon kasa, sun kasa rike hawayen yanzu, suna cigaba da tafiya zuwa dakin karatu, hawaye na tsirgo mata. Sarham yace. “Madinah kenan, ni kuwa na gane ki, ko ba Madinah Attahiru diyar masu Bankin Musulunci na Duniya bace? Idan na gane ki sai me hakan zai kare ni da shi, ni Sarham dan yaku-bayi?” Madinah tana hawaye tace “zaka iya fadin komai a kaina ba tare da na ga laifin ka ba Sarhm, laifi kan laifi na san na yi maka amma ina da DALILI na. Abu daya nake so ka gane yanzu, Daddyna daka sani a da can, to bashi bane yanzu. Wannan sabon Attahiru SoronDinki ne, wanda duniya ta biyar dashi, yanzu ya gane cewa rayuwar kanta da dan adam kansa komai mukami da mulkin sa, da dukiyar da yake tinkaho duka ba a bakin komai suke ba. To cut it short, Daddyna ya dade yana neman ka ido rufe domin ya nemi afuwar ka, ya kuma baka damar da ya dade yana hana ka”. Murmushin da Dr. Sarham Shanono yayi irin wanda yafi kama

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});