Chapter 2
Chapter 2
ta dauraye ta kife a kwando. Kafin sati ya zagayo sun kware da aikin abincin Haj. Ladi, sun saba da sauran ma’aikatan Hajiya Ladi biyu Zulai da Amuna. Hajiya Ladi na da ciwon Asma duk ranar da ta motsa mata bata iya tabuka komai, sai kwanciya sai tari, sai ta danka komai a hannun Inna, ganin ita babba ce ta girmi su Amuna kuma ta fi su hankali da kula, wannan ya fusata Zulai ta bar aikin, don a ganin ta an fifita bakin zuwa a kanta. Ya zama saura Amuna da Hauwa kadai ke yin sauran ayyukan, har aikin da baka tsammanin mara ido zai iya Hauwa ta iya, su yankan alayyahu da yankan salak, kuma ba tare data yanke hannun ta ba, haka duk wani aiki da za’a iya yi daga zaune, ita Inna ke baiwa tayi. **** **** **** Ciwon asma mai tsanani ya kwantar da Hajiya Ladi sosai, baiwar Allahnnan sai ta soma tsoron kada ta mutu ba’a san kowa nata ba, yanzu kam tayi nadamar rayuwarta da kuruciyarta data karar a Kano-to-Jeddah, harta soma tunanin iyayenta ko suna raye yanzu? Haj Ladi ta soma istigfari daga kwance, rannan cikin dare ta tashi, ta kuma tashi Innar Hauwa, tana kuka ta soma gaya wa Inna ita asalinta. Tace ita ‘yar kauyen Billiri ce, Billiri ta Gombe, ita ‘yar mai garin Billiri na lokacin ce, tace abinda ya fiddo ta daga gida auren dole ne suka samu uwar daki ta haure da su Makkah suka jima cikin rayuwa ta Kano-Jidda, daga baya aka kamo su aka watso Najeriya, shine fa ta kama sana’a don tana tsoron karuwanci a Kano, sabida shari’ar musulunci da aka kafa lokacin, har yau bata iya ta koma gida ba. Tace “idan ta Allah ta kasance a kaina, na bar miki shagon nan ki cigaba da hayar sa saboda rikon amanar ki, bamu jima tare ba, amma na yarda da halayen ki na kwarai, inaso ki cigaba da sana’a ta amma ki tattara komai nawa ki kaiwa mahaifi na, ki roka min gafarar sa, zan kara jan hankalin ki kan ki kula da mutuncin makauniyar ‘yar ki a rayuwar tashar nan, don akwai bata gari, gashi ta cika ido ta kai munzali, Allah ya taya ki kula da ita. Jikin Inna yayi sanyi ta ce “Hajiya Ladi tafi da kan ki nemi gafarar mahaifin ki, tunda da sauran karfin ki, ciwo ba mutuwa bane, iyaye sun wuce komai kuma ba zaki taba samun kwanciyar hankali ba in baki samu albarkar su ba. lokaci bai kure miki ba Hajiya Ladi”. Inna da Hajiya Ladi sun yi wannan maganar da kwanaki biyu Inna ta wayi gari da asubah don yin sallah sai ta fahimci Haj. Ladi bata tashi sallahr asubah kamar yadda suke yi kullum ba, tun tana tunanin jikin ne ya motsa mata ta makara har garin Allah ya waye Haj. Ladi bata tashi ba, sai ta matso ta duba ta, anan ta fahimci Hajiya Ladi, babu. Wato rai yayi halin sa. **** **** **** Inna ta tsaya tsayin daka aka kai gawar Hajiya Ladi gidan mahaifin ta wato gidan Maigarin Billiri, ta kuma isar da wasiyyar Hajiyar ta hanyar damka masa dukkan kudaden ta na cikin lalitar ta, ya sakawa Inna albarka yafi cikin kwando, ya tambayeta ko ita ‘yar ina ce? Don bata yi masa kama da ‘yan Kano Jiddan ba ita, Inna ta gaya masa daga cikin Badalar Kano suka fito, neman abin rufin asirin rayuwa, sakamakon batan maigidan ta, shine suka hadu da Haj. Ladi gun sana’arta, ta kuma taimaka musu a lokacin da basu da mataimaki sai Allah, ta gaya masa sun yi zaman amana tare. Ta kwashe duk irin taimakon da Haj. Ladi tayi musu ta fada masa, shi kuma ya ce albarkacin ta da mutuncin ta ya yafe wa Ladi duniya da lahira. Zai taya ta rokkon gafarar Ubangiji. Ta fada masa Hajiya Ladi ta bar mata shagon abincinta ta ce ta kama ta cigaba da yi, tana da jari, don haka zasu koma Kano, yayi mata fatan alkhairi da godiya, bayan sadakar ukun Hajiya Ladi suka koma gidan da take haya inda suke zaune, kasancewar kudin shekara data biya bai kai ko rabi ba. Inna ta fiddo ajiyarta ta kudin da ta ke ta ajiye da su tayi cefanen abinci yadda suka saba lokacin Haj. Ladi, daga ranar ta cigaba da sayar da abinci, ba maraba da Haj. Ladi na raye. Ciniki sosai suke yi da tsofaffin kwastomomin Haj. Ladi, a kullum ranar Allah sai ta dafa shinkafa tiya uku, suka tara kudi masu dan yawa, daga nan Hauwa ta kawo shawarar su canza gida mai dan kyau, abinda suka tara zai ishe su kama gidan haya tunda kudin Haj. Ladi ya kare, Hauwa tace su kama gida a nan cikin Kurna ko dai wani waje kusa da tashar kukan. Hakan kuwa aka yi. Inna ta kama dan mitsitsin gida mai tsafta fiyeda na Haj. Ladi, mai dakuna biyu da bayi da madafi a wani lungu cikin unguwar Kurna. Sana’ar abincin Inna na kara bunkasa, don duk tashar kuka babu mai abinci mai kyau kamar nasu, har ta kai Inna ta dauki ma’aikata biyu a karkashin ta da suke tafiya tun asubah su dora abinci kafin ta iso, Saude da Hajara zawarawa ne, ita kuma sai gari ya fara haske tayi sallar walha take tadda su, galiban zata tarar har sun dafa sun kwashe, sai ta zauna ta fara sayarwa da kanta. Basu jima a Kurna ba Hauwa ganin hankalin su ya kwanta, kuma samun su ya ninka na baya ta tada kayar bayan komawa makarantar su, ga shekarar na neman wuce ta, za’a zana qualifayin, tunda dai yanzu suna samun kudi daidai gwargwado Inna bazata kasa daukar nauyin zuwan ta makaranta ba, dama jakar makarantar ta da komai na makarantar ta na nan har lokacin bata rabu da goyon ta ba, hatta uniform da [photochromic Glass] dinta da takalminta suna nan cikin jakar. Inna ta ce Hauwa daga nan Kurna zuwa makarantar ku akwai nisa fa, kuma bazan iya kai ki kullum da kaina in dawo dake ba, da girkin abinci da muka dogara da shi zan ji ko da kai ki makaranta da dauko ki?” Hauwa ta ce “Inna me zai hana mu samu mai Achaba wanda ya kasance dan unguwar nan da aka san gidan su da komai nasa, ku tsadance, kullum ya kaini ya dauko ni, in yaso a dinga biyan sa duk karshen wata”. Shawarar Kulu ta samu karbuwa gun Inna, dama tasan dai Hauwa-Kulunta ba daga nan ba wajen kaifin basira. Hakan kuwa akayi. Hauwa ta samu komawa makarantar su special school ta Kano a ranar wata litinin, daga malamanta har dalibai ‘yan uwan ta sun yi farin ciki da dawowar Hauwa Bilyaminu, bayan kwashe watanni shidda rabon ta da makaranta. Amma duk da haka saboda kokarin Hauwa malaman su basu yi mata rifitin ba, sun tabbatar bada jimawa ba zata kamo duk abinda ya tsere mata. Wani kabila dan bautar kasa mai suna Teacher Amos Hedimasta yasa yake yi mata lesson fisabilillah, saboda kokarin ta, kullum na awa daya bayan tashi daga makaranta. Wannan ya taimaka mata kwarai tayi saurin kamo ‘yan ajin nasu, ya zama da an fara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36