Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana saka kayan barci zata kwanta kiran sa ya shigo mata, sai da ta ja aji, don taji haushin kiran data yi masa bai dag aba kuma bai biyo bayan kiran ba, kafin ta dauka da kyakkyawar sallama a bakin ta, maimakon ta ce tayi fushi, saboda bai zo inda take ba tun saukar ta a Kano, ko irin kananan korafin nan na amare da ke cikin lokacin da ake mararinsu, ina! Madinah nata salon daban ne, da wuya kaga bacin ranta akan abu, komai tana kokarin maida shi ba komai ba a rayuwarta (banda kishin Sarham), don ko shi Sarham zai rantse bai san me yake bata ran Madinah ba, sai ta karya murya cikin rangwadarta da zakin muryarta tace, “daga jin muryar ka mura kake, ina fatan angon Munawwarah yaci abincin dare?” Sarham yayi wata wawuyar ajiyar zuciya, tuni ya manta da kishin da yaci alwashin gasata akansa da zarar ta shigo gidansa, wato fushin aurenta da AVM Alkali, ya samu kansa da cewa “kayya! Anyway, kin zo lafiya Madinahtul-Munawwarah, ya gajiya ya aka ji da zafin garin mu?” Madinah tace “garin ku kai kadai? Ai ba’a canzawa tuwo suna. Zafi kuwa ai yana Saudi Arabia”, yace “kiyi min alfarma mu Arabian Bride, na san ke dinnan ma’abociyar tsinkaye, fahimta, da yi min uzuri ce, bazan iya shiga dakin Sumayyah inda kike ba kusa da dakin mahaifiyata ne, ba zan iya tsallake dakin Mama a gidannan in dinga zuwa inda kike ba, amma already nayi kokari nayi mana booking na komawa Jidda, don ni garin Kano ya fita kaina, zamu tashi rana ita yau in sha Allah muje mu ci duniyar mu da tsinke. Na yanke shawarar karbar aikin nan na Saudi-German”. Farin ciki mai yawa ya cika fuskar Madinah da zuciyarta, don dama tana cikin tunanin yadda zata iya rayuwa a garin Kano, ta shiga damuwa akan yadda zata iya rayuwa a Nigeria ma in general, tana dai daurewa ne albarkacin soyayya da yadda kowa nata ke lallashin ta, yayyenta kuma suke gaya mata aure babu inda baya kai mutum har bukka a jeji, amma hakika tafi son cigaba da rayuwa a Jeddah. A can aka haifeta acan ta rayu, acan ta girma. Abinda ta sani ta kuma yarda da shi kawai shine; ko a cikin ruga zata iya rayuwa in dai da Sarham Abbas ne, kuma in dai zasu kasance tare karkashin alfarmar aure da ni’imarsa itada shi har karshen rayuwar su. Sarham ya katse mata tunani, “kin amince ko?” Da sauri Madinah tace “haba-haba ai nima zan fi son hakan, da kunya kam mu kebe ko na minti biyu ne alhalin Mama da Abba suna cikin gidan, Allah ya kaimu lafiya, ni da ka kara mana wani satin ma a kan dayan ya zama munyi biyu tareda su kafin mu koma”. Yace “no, zamu tafi rana ita yau in sha Allah bana son zaman garin ne”. Ya tambayi Madinah ko me take yi yanzu? Ta ce ta yi wanka ne zata kwanta, ta gaji sosai, tace tun saukarsu a Kano bata huta ba. Sarham ya ce, “ai kuwa baki ga ta barci ba, kamar yadda nima ban ganshi ba. On this special day, ki tashi ki dauro alwallah ki yi sallah raka’a biyu nima zan yi yanzu, mu godewa Allah da ya cika mana burin mu da cikar alkawuran da muka yi wa juna yau shekaru goma! Kada ki manta a cikin sujjadar ki ta karshe ki roka mana ‘long life, prosperity, blessed children, unending love, and infinite peace. Madinah ina fatan ki zamo min ‘shelter’ kamar yadda birnin Madinah ya zamowa Annabin mu Shelter, refuge, security, safety and peace!”. Madinah ta lumshe idanunta cikin farin cikin da bazai misaltu ba, tace “kaima ina rokon ka roka min aljannah, don Hajjah Ramlah ta gaya min aljannah ta yanzu ta tashi daga dugadugan su ta dawo bisa dugadugan ka. Ka roka min ‘ya’ya masu yawa tare da kai kuma masu albarka, ka roka min Allah ya mallakamin zuciyar Sarham dina, nikadai raina bakidayan ta, don itace kadai ‘weakness’ dina a duniya (zuciyarsa)”. Finally, daga yau dai, sunansu ya tashi da ‘honorifics’ tunda ya koma Mr&Mrs. Dr. Shanono. Bayan tarihin fafutukar soyayyar shekaru goma!!! **** ***** **** A kwanaki bakwai din da Madinah tayi a gidansu Sarham, ta saba da kowa, kuma ta samu karbuwa ba laifi a wurin iyayen sa musamman Abba Prof. da yake ganin girman Kakan ta mai rasuwa Alkalin Alkalai, duk da ba wai sanayya ce a tsakanin su ba, amma yayi masa farin sani a matsayin daya daga cikin iyayen Kano. Ta fannin Mama kuma, ta zauna ne daga gefe tana laqantar Madinah a ma’auni na adalci da son sanin hakikanin halayen ta, inda a dan zaman su tare ta fahimci Madinah wayayyace, Madinah mai ilmi ce, bata da matsala sai ta rashin kawaici a kan Sarham, in bata gan shi ba sai ta ishi kannen sa da tambayar ina yake, wanda ke nuna zata yi kishi akan sa sosai, idan ya fita bazata nutsu ba sai ta ji shigowar sa gidan, tana da bala’in jan aji amma akan Sarham babu ajin ko kadan, don bata iya boye son da take masa a gaban iyayen sa da kannen sa. Gata da halaye na kowa tasa ta fishshe shi, wato halayen nasara, kai bazaka ce girman kasar larabawa bace, amma kuma duk da haka tana girmama su, musamman su iyayen sa, ta fahimci Madinah ta san abinda take yi yadda ya kamata, tunda duk rashin kawaicinta data fahimta, a duka kwanakin nan bakwai data yi tare dasu, bata tsallake su ta kebe da Sarham ba, ko ta bi shi inda dakinsa yake, ita da shi sai ko a waya, ko in ya shigo ya taddasu duka a falo, sai ya zauna ayi hirar tare da shi, amma baya sakewa musamman in Mama na wajen, tana kallon Madinah na kashe shi da murmushi. Shi da kan sa Sarham ya fahimci wani abu, wato tun bayan zuwan Madinah, mu’amalar sa da Sumayyah ta ja baya, Sumayyah ta daina shiga sha’anin sa sam, ko wuri ya shigo tana dariya sai ta daina, ta yi fuska. Ta daina kai masa abinci ko gyaran dakin sa wanda aikinta ne. A’ah, tun baya damuwa har ya fara tunanin laifin me yayi mata don wannan ba halin ta bane, me yasa ta daina ajiye masa abinci ko kiransa yazo ya ci, da gyara masa daki alhalin ta san ba wai Madinah ta tare bane, da zata cigaba da yin wadannan hidimomin da tazo ta tarar tana yi masa. Yau ya fita can karshen layin su yana wata irin romantic waya da Madinah, don hakurinsa kusan ya fara karewa da takunkumin da ya sanya musu, haka suke yi yanzu kullum da yamma in jama’ar gidan basa nan ko suna wasu sabgogin a kitchen, ko can dare in kowa ya kwanta, sai ga Sumayyah ta karyo kwana tana tafe cikin nutsuwa, ta zo har inda yake ta gifta shi bata ce masa ko sannu ba, har ta zarta shi kadan ya kashe wayar ya saka a aljihu, ya ce, “Sumayyah!”. Sumayyah ta dan dakata amma bata juyo ba, ta daure fuska sosai, ya ce “ko ba da Sumayyah nake magana bane?” Ta

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});