Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yasa ayi na gidan su Hauwa ya kammala, gini ya fito sosai na zamani, amma ba’ayi fenti ba tukunna. A zaure ya tadda Malam Isa yana shirya itacensa, ya yi masa sallama, tun daga nesa da Mal. Isa ya hango shi sai ya saki hamdala, Sarham na isowa tun kafin su gaisa yace “Dan nan kana lafiya? Ina ka shiga shekara guda da watanni ina neman ka? Tuntuni nake ta jiran zuwan ka, gashi ban san gidan ku ba, aikin gini tuni an kammala, wayar da ka bani kuma na kasa magana da ita tun lokacin da ta fada ruwan wanka na ta lalace, na sunkuya sai ta fado daga aljihuna ta shige bokitin ruwan wanka, shirun ka yayi yawa baka leko ni ba, in ce ko dai lafiya? Kusan shekara da rabi kenan ban ji daga gareka ba. Tun bayan tafiyar ka da kadan nake ta son in yi magana da kai abu ya faskara, in labarta maka abinda ya faru. Wato cikin ikon Allah kwanaki Mai kosai (matar sa) ta je tashar Kano line zata hau motar Zaria ta ce min ta ga wata mata kamar Innar Hauwa tana sayar da abinci a tashar, amma bata yi mata magana ba ta fasa tafiya Zaria tazo ta gaya min, don ta san irin neman da mukeyi mata. A take na bar abinda nake yi na bita muka je amma bamu same ta ba, sai wasu mata guda biyu a wajen dake yi mata aiki, muka tambaye su ko anan Innar Hauwa take, tana da ‘ya makauniya, suka tabbatar mana anan take sana’ar ta saidai ba kullum take zuwa ba yanzu, don bata da lafiya, su suke rika mata aikin yanzu, amma tabbas bamu ga Hauwa a wajen ba. Wallahi tun lokacin nake so in gaya maka na rasa hanyar isa gare ka, ni kuma ban kara komawa tashar ba har yau, don a washegarin ranar Sunusi dan waje na ya zo ya tafi damu Ikko, can inda yake sana’ar sa, mun jima bamu dawo ba sai jiyan nan muka dawo nida Maikosai”. Sarham bai cika katse mutum kafin ya kai aya ba, amma hakika yau ya gundura da dogon bayanin Malam Isa, kawai ya ce masa ya ga Innar Hauwa mana ‘short and simple!’ Mikewa tsaye yayi jikin sa yana dan tsuma, yace. “Sako takalmanka Malam Isa mu je ka raka ni inda ka gan su suna sayar da abinci din”. Malam Isa ya ce” ai ka bari ka fara duba ginin daka bar min amanar aikin sa ko? Kafin mu je neman nasu, tunda takamaimai bamu sani ba ko har yanzu suna can” Sarham ya kufula, kamar ya kaiwa Malam Isa naushi, don ji yake kamar yayi fiffike ya tafi shikadai. Malam Isa ya ce “to tunda naga ranka ya baci, bari to in kira Halilu ya zo ya zauna min akan itacen nan, in yaso in muka yi la’asar sai muyi maza mu tafi”. Kawai sai Sarham ya samu kansa da ce masa “ai nayi sallah kafin na zo don Allah Malam Isa, ka daina ja min rai, bani da hakuri wani lokacin kamar zawayi nake”. Malam Isa yayi dariya yace “ai wallahi sai ka jira ni na yi tawa sallahr, na kuma kora dan farau-farau a cikina, baka ji shi ba kamar bakin akuya tun dazu sai kururuwa yake”. Sarham ya koma kasa ya zauna, dabas! Kamar kayan wanki, dole ya jira Malam Isa yayi alwallah a gefe ya hau buzunsa ya tada sallah, ya gama ya jawo kwanon sha a rufe ya sha farau-farau din sa ya koshi, sannan ya dubi Sarham wanda ya kai kololuwa wajen hadiye fushi, Malam Isa yayi dariya yace “irin wannan zama a kasa haka duk ka bata farar shaddar ka, wai ni ko son Kulu kake yi ne, don itama haka take da kyau tubarakallah kamar ka, koda idanun suka makance sai suka kara zame mata gwanin kyau” Sarham bai tanka ba don bacin ran bata masa lokaci da yake yi, yace “in ka gama muje ko Malam Isa”. Yayi gaba ya bar shi yana masa dariyar shegantaka wai matuka zai dace da Kulu, don idan ta yi fushi haka fuskarta take komawa kamar balam-balam yadda ya koma dinnan”. Sarham yayi masa banza. Ya budewa Malam Isa gaban mota ya shiga ya rufe ya zagaya shima ya shiga, Sarham ya wani irin juya sityarin a guje da hannu daya saura kadan hular Malam Isa ta fado, da haka ya bar kofar Na’isa, suka hau titi sambal. Malam Isa da yaji sanyin AC ta ratsa shi sai ya hau sakin zance ba kai ba gindi, ya ce “na so hada Kulu da Sunusi, tun tana yarinya, na gayawa Malam Bilyaminu kuduri na, sai cewa yayi “shi yafi so ‘yar sa Kulu ta je makaranta, baya son auren wurin nan da muke yi wa yara, ka ga yanzu da ya barta ta auri Sunusi, da ta tara yara sun kai biyar, don bana tantama Innar ta ma irin sa ce shiyasa suke zaune lafiya baka taba jin kansu, su dai makaranta-makaranta kamar goyon Mungu Park, don har bayan data makance wallahi mutanen nan basu raba ta da boko ba, haka muka ga sun samar mata dan jagora kullum sai ta je, ban taba ganin masifar son boko irin na Innar Kulu ba, bayan ita ko a zaure bata taba zama da sunan karatun bokon ba”. Sarham ya juya kan mota cikin kwarewar tuki suka shiga tashar Kano line, ko tanka masa bai yi ba yana mamakin surutu maras ma’ana irin na Malam Isa, fadi ba’a tambaye ka ba, da alama bashi da matsala a rayuwarsa sai ta saida itacen sa. Malam isa ya wuce gaba kuma har zuwa lokacin bakin sa bai yi shiru ba, yana gaya masa shi ya san dama Innar Hauwa bazata zauna babu sana’a ba, musamman ta abinci, don aljanunta na girki da tsaftane. In ta fara girki duk gidan sa sai miyau ya tsinkewa kowa, saboda kamshin girkin ta, yanzu ma ashe shiyasa ta zabi sana’ar abinci, Malam Isa ya kara da cewa Sarham, “to Allah yasa ba’a tashar suke kwana ba, ko don ‘yar makauniyar nan Hauwa-Kulu, kada mazan tasha su dinga yi mata dan kira”. “A’uzubillah!” Sarham ya fada a zuciyar sa, lokacin sun kawo kofar rumfar abincin Inna mata biyu da dattijuwa daya suna ta kula da kwastomomi daya na zuba abincin in anzo saya, sukayi musu sallama, suka amsa suna tambayar su “me za’a zuba musu?” Kai tsaye Malam Isa ya ce nawa kwanon shinkafa da wake da miya da nama? Sarham yayi masa kallon takaici ya ce “Malam Isa abinda ya kawo mu kenan?” ya ce “au, yi hakuri na manta ne, ‘yammata Innar Hauwa-Kulu muke nema”. Dattijuwar mai zuzzuba abinci ce ta basu amsa. “Ayyah ai Innar Hauwa jiki ya ki dadi, yau wata guda kenan bata zo shagon nan ba, na ji ance ma bata gari, wani makwabcin su ya kai ta gidan mai maganin gargajiya na ‘ciwon zuciya’, a can wani kauye wai Albasu, don Innar Hauwa sam-sam ta ki zaman asibiti. Allah ne yayi Innar Hauwa na da nisan kwana da yanzu wani zancen ake akan jinyar ta ba wannan ba”. Sarham yace cikin yanayina gigicewa “na

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});