Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wanda na sani ce da gaske? Ina nufin na ISDB? In haka ne kenan jikar Alkalin Alkalai Habibu SoronDinki kake nema kenan fa?” Sarham ya dan samu kwarin guiwa da hope, domin a muryar Abba kawai ya ji ‘excitement’ na sanin iyayen Madinah da yayi, kamar zai yi na’am da maganar shi kam. Yace, “sune Abba, his last daughter Dr, Madinah Attahiru”. Da rashin karsashi a muryar sa ya baiwa Abba tarihin su Madinah da iyayaenta kamar yadda ya ji daga bakinta, da kuma na rayuwar su a Jeddah itada mahaifanta da ‘yan uwanta maza, inda a can aka haife su itada wasu daga cikin yayyen nata, da yadda mahaifin ta ya raba su a baya, yanzu kuma su da kan su suka neme shi ba shi ya nemi Madinah ba ta dawo masa ba, har pretending din da yayi tayi mata don kada ya koma mata ya gaya musu, da kiran sa gidan su da Daddyn nata yayi, domin ya bashi hakuri da uzurin sa na hana shi auren Madinah. Amma abin mamaki duk da wannan labarin da Sarham ya bayar Mama taki saukowa ta amshi zancen Madinah da hannu bibbiyu, musamman da taji wai har aure an daurawa Madinah bata tare ba mijin ya rasu, sai ta kara ninka ‘opposition’ din ta da zancen, inda tace cikin mamaki, “Sarham! Kai kuma inda Allah yayi da kai kenan saboda soyayyah? Bazawara/widow zaka dauka kana saurayi wanda bai taba aure ba? Bazawara fa kaikuma saurayi? Ni ban yarda wai bata je gidan mijin ba, sun dai rufa ka ne don su sayo mata matsayin budurwa, shiyasa ko lefe aka ce ka bari, kai kuwa saboda Allah me Madinar nan ke da shi da sauran mata da kake gudu suna rububin ka basu dashi?” Abba yace “Maimuna har gobe baki san SO ba na ga alama, kyale rai da abunda ya afu ga so, aure kuma ai ba kaskanci bane daraja ne, haka mutuwar miji baya nufin darajarta ta ragu, ni ban ga laifi anan ba don yarinya ta taba aure, shin Manzon mu ba da bazawarar ya fara ba? Yarinyar nan ‘yar manyan mutane ce kuma ‘yar babban mutum, sama da abunda yafi haka zasu iya cewa kafin su bada auren ‘yar su, aka ce tuwon girma… miyar sa nama Maimuna, ko yanzun ba don ta rasa miji bane yasa suka bashi, a’ah, ya ci darajar soyayyah ne kawai Allah kuma ya tsaga cewa ita din rabon sa ce”. Mama tayi shiru amma ta ki gamsuwa, ta ce “ni kawai ko ‘yar shugaban kasa ce bai dame ni ba, tunda suka raina arzikin mu tun farko nima na raina mutuncin su, saboda basu yi amfani da ilmin su ba anan don wallahi ba yabon kai ba, Sarham dina ya wuce raini, tunda Allah ya bashi addini, nasaba, ilmi da basira to ya gama bashi duk wani arziki na duniya koda kuwa a kan jaki yake yawo”. Duk aka yi wa Mama dariya Abba yace “Maimunatu Dan farin? Kike wannan zakewar a kan sa babu fulatanci? Ina fulatancinki ya tafi ne?” Ta yi fuska sosai ta ci laya tace “ko rabin farko ne shi ba Dan fari ba, ina son abuna yadda suke so ‘yar su koma fiye, sun dauko sudin kwano sun bashi, ina dalili da gatan sa shima da komai?” Abba yana danne dariyarsa yace. “Barr. Maimunatu to yaya zaki yi? Tunda shi ya ji ya gani yana son leftover din nasa a haka?” Sarham dai bai ce komai ba kansa na kasa, kamar yace da kasar ta tsage ya shige, amma ya ji ciwon kalmar nan ta an bar masa sudin kwano, ta kara rura wutar kishin sa akan auren Madina da AVM Alkali. Duk ya daina dokin auren ma, Madinar ta kara bashi haushi, amma baya jin ruwa da iska zai fasa karbar auren Madinah ko da ta haihu goma da AVM wanda ke nufin so na hakika yake yiwa Madinah. Abba da Hajiya Kulu, suka yanke shawarar wadanda za’a tura Sorondinki daga waliyyan Sarham don gabatar da zancen aure don itama Haj. Kulu tayi na’am da zancen dari bisa dari don kuwa ta san Kakan Madinah farin sani marigayi Alkalin Alkalai wanda tace zuri’arsa ne kaf suka samar da Sorondinki. A daren Abba Prof. kwana yayi yana lallashin Mama cikin dabara da soyayya irin ta manya akan maganar auren Sarham, yace mata abu daya zata duba kawai; son da Sarham yake wa Madinah, in ta duba wannan to sai ta sakawa ranta salama. Domin shi ya lura son da Sarham yakewa Madinah mai yawa ne, tunda har ya iya kwashe shekarun nan babu aure saboda rashin ta, kuma jin ta auri wani kafun shi, bai say a ce ya fasa ba. Ita kuma Mama irin iyayen nan ne masu kishin ‘yayan su, wannan son da ake fadi yana wa Madina shi yafi komai bata mata rai, don a tsarin ta sam bata son Sarham ya auri macen da son da yake mata ya zarta wanda take masa, ko wadda zata zo ta canza masa behaviours da alaqarsa dasu. A ganin ta son da yakewa Madinah yayi yawa har ya zarta nata son, ba don haka ba ai da bata yarda ta auri wani kafin shi ba, tana tsoron kada Madinah tayi amfani da hakan ta bautar mata da shi, ko ta wahalar mata da shi tunda ta zame masa rayuwa dungurungum. Duk da ta san Sarham jarumi ne akan komai nasa ko a cikin maza, kuma tsayayyen namiji ne tun yana yaro akan ra’ayinsa, amma tana tsoron wannnan matsiyacin son da yake yi wa Madinah Attahiru. Haka Abba Prof. ya samu ya lallaba ‘yan kayan sa, don shikadai yasan abinda yake zuciyar Mama, ya nuna mata in bata cire kishin matar Sarham daga ranta ba zata zubar da girmanta, kuma zata sha wahala don matsayin kowaccen su daban a wajensa, ya roketa kada ta zama fitinannun iyayen mijin zamani masu tsanar surukansu babu gaira babu dalili kawai don yaransu na son su, tunda itama ba haka Hajiyar Gadonkaya tayi treating dinta ba duk da ta san son da Abban yayi matukar yi mata, da haka ya samu ya lallabata har dai ya samu lagonta ta amince aje akai kudin auren, ta kuma sakawa al’amarin albarka. Washegari waliyyan Sarham suka tafi SoronDinki. Suka dawo da albishir mai dadi na cewa Baffanta yace Juma’ar nan za’a je a daura auren a babban masallacin juma’ah na Kano, su sun shirya tuntuni, su suke jira dama. Suka kuma fadi irin karbar mutunci da saukar girma da aka yi musu, wannan ya kara sauko da zuciyar Mama. Iyayen Sarham sun gabatar da komai na auren har sadaki ga kanin Baban Madinah tun kafin juma’ar ta zo, kuma Baban Madina yana ta kara jaddadawa kanin shi ta waya ya gaya musu shi baya karbar lefe, sadaki da kudin aure kawai yake amsa. Wannan ma ya kara sanyayawa Mama. Juma’ah na zagayowa aka daura auren. **** **** **** Tun dawowar sa Najeriya Sarham bai samu nutsuwa ba ko ta kwabo, sai yau da aka daura auren sa da Dr. Madinah Attahiru bayan saukowa daga juma’ah, mahaifin ta da duka ‘yan uwanta maza hudu sun samu sun halarci dauren auren, Madinah ‘yar dangi ce

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});