Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

other stuffs kawai nake karawa da su duk wata, saboda Mama bata yarda ta saya min irin wadanda nake so.” Idon Sumayyah har rawa yake don bacin rai, da tsoro da mamakin abinda ‘yar uwarta ta aikata, har ta fara hango irin hukuncin da Bhaiya zai mata, ta fara hango shi ya dauke Surayyah da mari kodayae Bhaiya baya duka baya zagi, amma fa bai iya fushi bay a kuma kware da (silent punishment), fatar bakinta ma rawa take yi, ta kasa murnar dawowar tasa ma don haushi da mamakin Yayar ta Surayyah, da kyar Sumayyah tace, “kin ci amana amma, Yaya Surayyah kin ci amanar Bhaiya, na rantse da Allah babu ruwa na, count me out of your dirty game”. Daga haka Sumayyah ta fice da gudu tana “Oyoyo! Bhaiya, Mama Bhaiya ya shammace mu”. Sai ga Mama ta fito daga dakin ta itama kan ta ko kallabi babu, tace “really?” Surayyah kuwa bayan gida ta shige ta boye kanta, jikin ta ba inda baya rawa. Sumayyah ta kusa kai Sarham kasa sakamakon tsallen da tayi ta shako shi da sunan murna. Haba! Sarham sai ya balle da fada blah! Blah! “Sumayyah meye haka? Baki san kin girma bane? Ko an ce miki da da yanzu ma daya ne? Bana son irin wannan haukan welcome din, an wuce wajen, kada ki kara”. Mama ta iso falon tana cewa “kai mai hali dai baya fasa halin sa, kai kuma daga zuwa sai fada kamar tsiduhu? Shekara uku ba kwana uku ba basu saka ka a idon su ba, ba dole su yi murnar ganin ka bagatatan yau ba?”. Sarham ya mike ya isa gareta ya kama hannayen Mama ya rike cikin tafukan sa, yana murmushin farin ciki ya kai su ga fuskar sa kan sajen sa, wanda a baya kafin ya tafi bashi da shi yace “My Mommah, I missed you badly kin sani. Amma autar ki bata san ta girma ba, kullum tana nan jiya I yau shiyasa bazan daina fada ba”. Kafin kace meye wannan gida ya kacame da murnar dawowar Dr. Sarham. Da Abba Prof. ya dawo murnar tafi armashi, a ranar har dare suka raba a falo suna hirar yaushe gamo, amma an nemi Surayyah an rasa a falon, tunda ta zo ta yi masa sannu da zuwa ta gudu gidan Kakar su Haj. Kulu a gadon kaya, don tayi-tayi Sumayyah ta karbi ‘yan kudin da ke hannun ta ta kai Kofar Na’isa, ta roke ta kan ta rufa mata asiri tayi maza ta kai musu tun kafin Yaya Doctor ya huta ya waiwayi zancen, wadanda ko kwatan abinda ta kashe daga abinda yake aikowa din basu kai ba. Sumayyah ta ki amsa, ta kuma ce in ta takura mata ta cigaba da saka sunanta cikin laifi nan wallahi zata tona ta, “kawai ki yi harkar ki Yaya Surayyah ki rabu da ni, ni ba maciyiya amana bace kuma ba’a shirya rashin gaskiya da ni”. Duk da ta san Sumayyah ta gaya mata bakar magana sosai amma ta kasa cewa komai wannan karon, girma da mutunci ai madara ne, kuma mutum shi yake rike kayan sa, ta yarda ita ta zubar da girman ta har Sumayyah kanwar bayan ta yau ta nemi zagin ta (in disguise). Don haka Surayyah ta ga gara ta gudu gidan Hajiya, inda ba abinda Sarham ya isa yayi mata in dai a gaban Hajiya ne koda ta bare da ita. Washegari walima sosai Mama ta hada musu a babban falon ta, ta murnar dawowar Sarham da kammala zurfafa karatunsa, wato kwas din da ya je yi na tsayin shekaru uku a (KAU, Jeddah) ta kasar Saudi Arabia, don haka aka tura direban zuwa Abba Gadon kaya don ya dauko Hajiyar Gadonkaya. Jin maganar zuwan direba daukan su daga bakin Maigadi yasa Surayyah duk ta damu, lokacin da da aka ce su fito a tafi gidan Abba, Hajiya tace ta shirya su tafi gidan nasu tare, ta yaya ana can ana murnar zuwan dan uwanta da taya shi murnar zama babban likita zata taho ta zauna ita kadai anan kamar mujiya a cikin ‘yan uwanta? Tace lallai ta shirya su wuce, bazata bar ta ita kadai a gidanta ba. Da Surayyah ta ga ba sarki sai Allah sai ta fadawa Haj. Gaskiya cikin damuwa, cewa laifi tayi masa fa, bata so ya kure ta, don zai iya dukan ta, Hajiya kuwa ta saka ta a gaba tace sai sun tafi taren, mai dukan mata ita sai ruwan sama. Mama da hannun ta tayi girke-girken walimar nan, don haka sun kwashi gara mai dadi sosai. Sarham yayi wa girkin Maman sa cin yaushe rabo! Da sweet cook din Mama!? Ba abinda bai ci ya hantse a wajen ba. Da yake magananne ne har gobe tunda ya fara cin abincin nan bai yi shiru ba, yana yi ne yana zuba santi, saida Hajiya Kulu ta saka masa filon kujera a kuturin sa, tace, “gara a saka maka waigi haka likita Sarhamu, Allah yasa dai matar duk da zaka aura mai iya girki ce. Shin ma ina aka kwana kan maganar aure? Wannan karon kam zan bada cigiyar mata har a masallatai idan bakin jini ne ya hana ka samun mata”. Daga Abba har Mama duk suka bi shi da ido kamar Hajiya ta ci musu albasa ne ta fadi abinda ke ci musu rai, suka dakata da cin abincin suma suna jiran amsar sa da zai fada, da alama dukkannin su suna da wannnan damuwar tuntuni kawai Hajiya ta riga su furtawa ne. Ai yau Sarham da karfin guiwar sa ya ce “ki kwantar da hankalin ki Hajiya, ba sai kin kai tallata a masallaci ba, an riga an bani mata cikin daraja da kima kuma wadda nake so tuntuni, ku ake jira ku je tambaya da sanya lokaci”. Mama da Abba har suna hada baki wajen tambayar sa. “Daga ina ka samo matar kuma ‘yar waye a Kano a ina suke? Tun yaushe kuke tare bamu da labari?” Yace “Mama zaki iya tuna yarinyar dana ke tare da ita tun zuwana karatu MBBS na farko? Ina nufin MADINAH. Ke ai kin jima da sanin labarin ta, wadda a baya mahaifin ta yace bazai bani ba, to ita din ce dai muka sake haduwa a wannan karon muka sulhunta, mahaifin ta kuma ya bani auren ta already ku kadai yake jira, ‘yar gidan Attahiru Habibu SoronDinki ce”. Mama da yake ta san zancen Madinah tuntuni nan da nan ta ci magani, fuska a gintse tace “shima ai ya sani” (tana nufin Abba Prof.) ta kara da cewa “ko ba yarinyar da ka kusa kashe kanka a kanta ba, saboda uban ta ya wulakanta ka? Yarinyar da ka zauna shekara bakwai cikin tuzuranci babu aure saboda an hana ka ita, sakamakon cewa sun raina arzikin mu da mutuncinmu? Itace ko ba ita bace?” Sarham yayi shiru, gaban sa da zuciyar sa na wani irin faduwa, tsoron sa Allah tsoron sa kada Mama tayi (opposing) maganar Madinah, shi kam da ya shiga uku, don in har ba Madinah ya aura ba, babu shi babu aure a duniya (ya fada a zuciyarsa). Abba ya ce “Lelen Abba rabu da Mama, yi min cikakken banyani, diyar Attahiru Sorondinki

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});