Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dafe dahir har da ‘yar ka tubarkallah, shine ita zaka yi mata fatan ta tsufa a dakin uwar ta, alhalin kai ba son ta kake yi ba, wannan fa shi ake kira karfin hali barawo da sallama ko in ce, Bhaiya na, da tsabar son kai tsagwaro. Wani hali da ban san shi da shi ba. Ni wallahi gani nake ma babu wanda ya dace da ya aureta kamar dan uwan nata, tunda jinin su daya, ya san darajar ta, zai yi hakuri da nakasar ta, ya riketa da daraja a gidan aure, don kai kam Bhaiya, baka da alqiblah. Ayi magana cibi ya zama kari!”. Ta sake tuntsirewa da dariya ta ce “sai amara kirazan biki, mu ne manyan kawayen amarya Hauwa’u, a bikin ta da Yayanmu Jamilu”. Sumayyah har da dan gudu-gudunta ta bar dakin, tana cigaba da tillika dariyar shegantaka. Don ta san ta gama kunna shi in ta kara minti uku a gabansa zai iya losing control kai mata duka. Don tana ganin yadda yake girma idanunsa tunda ta soma shegantakarta. Maganganun ta dinnan, suka taru suka zamewa Dr. Sarham “a warm food for thought!” A tsayin wannan daren bakidayansa kona rabin away a kasa runtsawa. Sarham sai faman juyi yake a kan gadonsa, daga wannan gefen zuwa wancan, yana tauna maganganun Sumayyah a kwakwalwarsa, yana kuma fassarasu a zuciyarsa cikinma’auni na hankali da tunaninsa. Daren da yazo masa da tarin ‘alterations’ koko ‘revolutions’ wadanda a can baya bai taba hango yiwuwar makamantansu ba. Ko na minti daya ya kasa rintsawa. Idan ya tuna maganganun Sumayyah. A ganin sa Sumayyah maganganu ta gasa masa masu zafi ta cikin ruwan sanyi, koko yace jirwaye tayi masa mai kama da wanka, don dama tana kullace da shi akan abinda yayi mata, don kawai ta tambaye shi ko son Hauwa yake yi shekarun baya, bazata manta ba yayi mata wulakancin da bata zata ba, kiris ya rage ya doketa. A nata bangaren Sumayyah, ta dade tana kiwon mu’amalar sa da su Hauwa ta rasa alkiblarsa, musamman in ta tuna abinda yayi mata daga ta tambaye shi ko son Hauwa yake? Ta tuna a ranar dukanta ne kawai bai yi ba, shine abinda take nufi da “ayi magana cibi ya zama kari”. Da gasken gaske ya kasa barci a daren, sai faman tauna maganganun Sumayyah wadanda ya kira jirwaye mai kama da wanka. Washegari ya samu kansa da kasa zuwa gidan Inna, saboda har zuwa lokacin ransa a bace yake, haka a sauran kwanaki ukun da suka biyo baya ko hanyar kofar Na’isa bai kalla ba, yana like wajen su Waheedah, kamar ya maidasu ciki, don a can yake samun sanyin ran sa, daga zafafan maganganun Sumayyah da haushin Hauwa (a ganin sa bakaken maganganu ne Summy ta gasa masa son ran ta), da suka dade suna dafa shi kamar dafaffiyar masara, kuma ya kasa cewa Sumayyah komai a kai again bayan kuma ita kadai ce zai iya zancennan da ita. Madinah ta samu lokacin sa sosai a wannan satin, don yanzu kullum yana wuni tare da su baya zirga-zirgar gidansu Inna. Inna na talgen tuwo a yammacin yau da Sarham ya kwashe kwanaki bakwai bai zo gidan su ba, sai ya fado mata a rai, ta dubi Hauwa dake wankin sittirun ta a bakin famfo tace. “Kuluwa!” Hauwa ta tsuke baki ta kuma tsuke fuska bata amsa ba, ai ta san in ta ce mata Kuluwa bazata amsa ba, sai ta ce “ni kuwa kin lura da abinda na lura da shi?” Hauwa tace “me?” “Likita Sarhamu, yau kwana bakwai bai zo gidannan ba, tun ranar da ya zo yace min kansa na ciwo, yanzu haka jikin ne ya matsa masa tunda har kika ga yayi wannan dadewar bai zo ba”. Hauwa ta yi shiru bata ce komai ba, ta cigaba da wankin ta, ashe ba ita kadai ta lura da rashin zuwan nasa ba. Inna ta sake cewa. “kin ga da ace na san gidan su sai in je in duba shi”. A nan ne Hauwa ta bata amsa, “kai su Inna akwai wuce gona da iri”. “Ba wuce gona da iri bane Hauwa-Kulu, baki ji fadar bahaushe ba? Yace KA GAIDA MAI GAISHEKA KO DA BAZAI AMSA BA!” Wannnan magana ta karshe da Inna ta yi, ta yi ta ne a kunnen dan halak din wato (Sarham), don a lokacin ya iso tsakar gidan da kasaitattar sallama a bakin sa. Nan da nan Inna ta bar abinda take yi a madafin ta fito, ta washe baki tana amsawa, “maraba da Da na Sarhamu, likita Sarhamu na ne tafe? Dan halak yanzu nake zancen ka, sai gaka”. Sarham ya tsugunna a kofar kitchen din yana gaida Inna, Inna ta koma ta kashe wutar tuwon, ta taso suka shiga falon ta tare, suka kara gaisawa, Inna sai taga duk ya rame mata, tace “Likita jikin ne ya boye ka ne?” Ya ce “a’ah Inna lafiya ta kalau, kwana biyunnan dai ban cika fitowa ba, ina can wajen su Hauwa’u karama kullum”. Hauwa ta shigo da sallama tana dan dafa bango, ta isa kofar dakin ta sannan ta juyo saitin da ta ke jin tashin tattausar muryar Sarham, ta ce cikin girmamawa “Dr. barka da zuwa, ina wuni?” Ya dago kai ya kalle ta kadan, kayan jikin ta sun dan jike sun manne a fatar jikin ta, Hauwa yar shekara sha takwas ta gama samun duk wani dirin jikin da jikinta zai bayar, da kyakkyawar suffa na abinda ake nema a tare da budurwa ‘teenager’, nata har ya zarta yawan shekarun ta, don tsammani zakayi ta kai shekaru ashirin da daya. Tun asalinta Hauwa bata da rama haka take ‘yar duma-duma, lubu-lubu (luscious). Dr. Sarham ya yi wata ‘yar ajiyar zuciya ba tareda ya san ya yi ba, yana tuno kwailancin ta na shekaru biyar a baya, wai itace haka yau a gabansa, yace a hankali “lafiya kalau, ina Saurayin ki dan polo dan gayu?” ‘yar dariya Hauwa ta yi, ta shige dakin ta bata ce masa komai ba. Sai Inna ce tayi kwafa ta ce, “ai ka bar ni da Hauwa da Jamilu kawai, nice maganin su da rashin kangadonsu, da ni suke zancen wallahi, na sa uwarsa Rumanatu tayi musu iyaka, idan yaji toh, in bai ji ba na rantse zan iya kai shi kotu don alkali yayi musu iyaka. Na fada na kara ni fa bazan taba yi wa Hauwa wani aure ba, balle in bawa dan Zakari. Allah na tuba ko dan shugaban kasa ne ya zo neman auren Hauwa, wallahi bazani bayar ba, balle dan Zakari tsatson zalunci. A cikin burika na masu kyau a kan Hauwa, babu batun yi mata aure a ciki, babban burina shine ta yi karatunnan na zamani mai zurfi in dai makafi na iyawa kamar yadda ta fara, ta samu abunda ko bayan raina zata dogara da kan ta, kuma in karfina ya kare kada nata raunin ya bayyana dalilin rashin karfi na, ko in ta Allah ta kasance min hakan ya kassarata. Ni din nan nice karfin Hauwa, ni ce kuma idanun ta, bazan taba bari a wulakanta min ita da sunan aure ba, ko a ci mutuncin lalurar ta a dalilin aure, shi yasa na gwammace in adanata

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});