Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a jami’a, idan hakan mai yuwuwa ne. Zai nemi dai wanda zaiyi ‘coaching’ din sa akan ilmin ‘visual impaired’, ba zai koma Jeddah ba sai ya tabbatar rayuwar su bata da matsala ta zama ‘stable’ kuma Hauwa na kan turba ta tafiya zuzzurfan ilmi. Wanda shine kadai zai zame mata gata a dukkan rayuwar ta, a matsayin ta na mai nakasar da ake kira mutuwar tsaye. To amma me? Sai zuwa yake yana dawowa a inda ya san lokon gidan su Inna yake situating, amma baya ganin gidajen da ya sani a wurin sai fili fetal. Da aka zagaye da langa-langa. Ya ilahi! Ko dai yayi batan kai ne? Ko makuwa yayi? ko kuma ya manta hanya ne? To amma da mamaki ai ace ya mance hanyar gidan su Hauwa, ko shekaru goma yayi baya nan ba uku ba, in dai ba juyewar kwakwalwa ya samu ba ko shafewar tunani wato ‘amnesia’. Kuma dai ga Kofar Na’isan nan dai tana nan bata je koina ba. Da ya gaji da zuwa da dawowa wato ya gaji da safah da Marwah a cikin mota sai ya fito yayi ta zagaye wajen da kafafun sa, amma ya kasa ganin gidan Malam Bilyaminu, ya kuma tabbatar anan gidan yake, sai ma yaga ‘pure water’ na leda ake bugawa a filin wajen. Kamar an maida wajen kamfanin ruwa leda. Ya tambayi wani saurayi cikin masu buga ruwan ledan don Allah ko inane gidan Malam Bilyaminu dan Kofar Na’isa? Ya ce da saurayin “kamar na maku, don na jima bana nan”. Saurayin yace shima bako ne a unguwar, amma bari ya hada shi da Malam Isa mai faskare shi da ya dade a unguwar. Gidan malam Isa ne kawai ba’a rushe ba cikin gidajen wurin don gidan yayi gefe sosai, saurayin ya raka Sarham suka samu Malam Isa a zauren gidan sa yana aikin itacen sayarwar sa, ya yiwa Malam Isa bayanin wanda Sarham ake nema ko ya san shi? Wai gidan Malam Bilyaminu. Malam Isa ya bar abinda yake yi ya juyo ga Sarham sukayi musabiha, sai ya bashi wajen zama kan buzun sallahr sa yace ya zauna, da ya tambaye shi ko wa yake nema a gidan Malam Bilyaminu? Sarham yace. “Innar Hauwa”. Sai Malam Isa ya tambayi Sarham “kana da alaqa da Innar Hauwa ne?” Sarham yayi dan jim! Kafin yace “eh, amma na dade bana kasar, ina fatan ba wani abu ne ya faru da su ba?” Malam Isa ya nisa yace, “eh toh, samari, ai Innar Hauwa ta gamu da sharrin wani azzalumin kanin miji, ya sayar da gidansu, rana daya muka ga an zo ana rushe gidan, aka maida wurin wajen hayar neman kudi kala-kala, na so ta zauna mu je kotu a kwato musu hakkin su ni da sauran makwabtan su, kasancewar a gaban mu Zakari ya sayarwa da dan uwan sa gidannan aka raba rigima tun a lokacin a gaban marigayi mai unguwa, amma matar nan ta ki tsayawa, ta gudu daga gidannan bamu sani ba, yau kusan shekara uku zancen nan da nake maka, bamu kara jin duriyar su ba ita da ‘yar ta Hauwa-Kulu”. Sarham ya ji idon sa har rawa yake banda fatar idon dake raurawa itama, da kyar ya iya yace wanene kanin mijin nata? Ya ce. “Zakari sunan sa, don kawai dan sa ya zo yace zai auri Hauwa-Kulu, shine ya sayar da gidan don ya kore su ko ince yasa aka rushe shi, to ya ci galaba kam don daga ranar da aka zo aka rushe gidan su basu kara waiwayar kofar Na’isa ba, kuma ba wanda ya kara jin duriyar su, ina tabbatar maka bazasu zauna a Kano ba yadda suka fita a tagayyare, wutsiya zage, kuma cikin mummunan bacin rai. Jifa aka dingayi da komai nasu. Tausayi yasa na tattara tumakin ta da akuyoyin ta na kado su gida na, na hada na nawa na cigaba da kiwata mata, muje in nuna maka su cikin shekaru uku gasunan suna ta hayayyafa ban san ya zan yi da su ba”. Sarham ya rasa a halin da yake ciki tsakanin tashin hankali da gigicewa, yace da Malam Isa “basu da wasu ‘yan uwa da zasu iya zuwa wajen su?” Malam Isa yace “eh, toh, ai dukkan su ‘yan cikin Badalar nan ne a sanin da muka yi musu, in ma suna da su, to mu bamu san su ba, basu da wasu ‘yan uwa da bamu sani ba, dangi kam sun kare ai, kuma bana jin a zuciya irin ta Innar Hauwa zata yarda ta rabi wani nata in ma tana da shi. Tun tali-tali tanada wani irin hali, tafi gane rayuwa ta tsayuwa akan kafafun ta fiyeda ta rabu da wani ya taimaka mata, har kuwa bayan batan mijinta, bata taba neman taimakon kowa ba”. Sarham yace “shin a ina wannan Zakari din yake?” Zai so kwarai yayi ido hudu da wannan Zakarin, don kwatarwa su Inna hakkin su, zai so kwarai yayi shari’ah da shi, daganan har kotun daga ke sai Allah ya isa! Domin ya kwatowa Inna hakkin ta, a daure shi har sai igiya ta yi rara, amma Malam Isa ya gyara murya ya kuma gyara zama, yace masa “ka manta da Zakari kawai, ka nemo su Hauwa din shine mafi a’ala, ganin Zakari bazai kare ka da komai ba sai karin bacin rai, don zai iya yi maka mummunan bita da kulli, idan ya gano su Safiya suna da wani gatan bayan shi a duniya. Ai sanin cewa basu da kowa da zai tsaya musu ne yasa yayi musu haka!”. Sarham yayi shiru, can yace Baba ina so in sake saye filin wajen ne, ina nufin filin gidan nasu daga hannun wadanda suka saya”. Malam Isa yace, ai hakkin mallakar filin ya bar hannun Zakari tuntuni, wannan mai kamfanin ruwan shi ke da wajen yanzu, kana iya tuntubarsa ko zai sayar maka, amma lallai sai ka nunnunka masa kudi”. Tare suka je har gidan mai kamfanin ruwan ledan da ya kafa rumfa a filin gidansu Hauwa yana sana’ar ruwa, suka gaisa, Sarham yana hadiye hawayen sa yace, so yake ya sayar masa da filin wajen, inyaso ya yanka masa kudin ko nawa ne zai biya shi, ya bashi takardun mallakar kangonnan. Hakan kuwa aka yi, da mutumin ya ga kudi ya amince, ya yanka kudin da yaga dama Sarham ba musu yace gobe zai kawo masa su (in cash) ya karbi takardun wurin bisa idanun shaidu kwarara da sabon mai unguwa. Bayan ya bar Kofar Na’isa kasa komawa gida yayi, ya kuma kasa tuka motar, ya koma gefen titi ya kashe motar ya kifa kansa a kan sityarin, yana tuno fuskar HAUWA-KULU da kyawawan manyan idanun ta da ya nakasta mata su bisa kuskure, da kuma murmushin Innar ta. Daga baya ya ja motar ba tareda ya san wurin zuwa ba, haka yayi ta yawo kwararo-kwararo titi-titi a cikin BADALOLIN KANO, ya taho tun daga Kofar Na’isa, ya isa Kofar Gadon kaya, ya bi ta kofar Dukawuya, ya bulla ta kofar Kabuga, daga can ya karya kan motar yayi kofar Kansakali, ya taho har Kofar Ruwa, bai ga ko mai kama da Inna ko diyarta Hauwa ba, ya dawo baya ta cikin gari ya bulla ta Sabuwar

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});