Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da mara lafiya a asibiti ne. Mama tayi wani dan tunani sai ta ce “in kika bibiya bazai wuce mutanen sa na Badala ya gano ba. sune kadai zai dauka da muhimmanci irin haka ya kasa nutsuwa in suna cikin matsala”. Surayyah ta ce cikin mamaki “ba sun bar Kano ba? Ba sun bace masa ba tuntuni?” Mama tayi dariya tace “ko a ina suke in dai a fadin Najeriya ne na tabbatar miki sai Sarham ya nemo su, ki bar Sarham akan abinda yasa kan sa, ko yake kuma kauna da son taimakawa da zuciya daya”. Surayyah ta kwana abun yana bata mata rai, na yadda ta zage ta shirya masa abincin nan da kyau, don ita bata son zancen su ma, yadda aka sakata girkin wahalar wasu kauyawa wai su su Innar Hauwa, tarkacen BADALA, don haka washegari da ya saka ta girkin again tayi maza ta ce kanta na ciwo bazata iya ba, dole sai Nancy sabuwar mai aikin Mama ya saka tayi masa ‘potatoe porridge’ da yaji ganyen alayyahu. Da dafaffen kwai. Ita Hauwan ma da ake kaiwa garar abincin mai dan gina jiki, don a samu ta murmure ta tada komada daga muguwar ramar data yi da mokadewar da kashin wuyan ta yayi a Albasu, sam bata iya ci, bakin ta ya kasa karbar dandanon abincin don bata saba da cin mai lafiya da dadin dandano irin sa ba. Ruwan bunu (lipton) ko na Milo kawai take iya zubawa a cikin ta ya zauna da dadin rai, ta zama kamar ka bushe ta ta fadi don kamar ma bata da lafiya, nan kuwa yunwa ce kawai ta zaman Albasu ta zauna a jikinta tayi mata illah. Abu daya ke faranta mata in ta tuna Inna na bisa karkashin kyakkyawar kulawar asibiti yanzu, kuma ana tabbatar mata da tana jin sauki kasancewar idonta a rufe yake kuma kullum ana mata karin ruwa kafin ranar da za’a yi mata aiki tazo. Sarham ya biya komai ranar aikin, ya kuma saka hannu aka yiwa Inna aikin zuciya. Aka yi lafiya cikin nasara ba kamar yadda Inna ke tsoro ba. A lokacin ne ya samu ya koma cikin hayyacin sa tun daga ranar da ya dauko su Inna sai yau ya samu nutsuwa, bayan an gama aikin an kai ta dakin hutu, inda Hauwa ta cigaba da jiran farfadowar ta. Sai ranar ya samu ya leka su Baby Hauwa. Madinah bata iya fushi da Sarham ba, ko me yayi mata kuwa, komai girman laifin, amma yau a kwayar idonta ya gane tayi fushin, musamman da yaga tana ‘avoiding eye contact’ da shi, ya san tayi fushi mai ban mamaki ko bata furta ba. Ya sa hannu ya dauki Hauwa cikin dan kyakkyawan gadon ta tana barci, ya zauna dab da Madinah yace “Likita matar Likita barka da yau, ya kuka kwana? Ya kukan daren uwar bil’adama?” Madina ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, sai yace “ba sai an gaya min ba, na san nayi laifi wa GIWAR SARHAM, kuma na karbe shi tun ba’a bani ba (laifin), tun kwanaki uku baya ma fa ya kamata ace na koma Jeddah, amma inada uzurin da ya rike ni mai muhimmanci, kiyi hakuri kin ji Madindin din Sarham! Madinatul-Munawwarah my shelter, my eternal happiness, my home peace, my safety and my security, in sha Allahu nama fasa komawa, sai kin gama wankan jegon ki sai mu koma tare, zan yi amfani da lokacin (as annual leave) dina”. Amma har ga Allah ya fasa komawa ne saboda lafiyar Inna, yana kuma son daukan ‘measures’ din da ya dace akan rayuwar su Inna kafin ya koma Jeddah. Madinah da bata iya dogon fushi da Sarham ba jimawa ta yarda da uzurin sa ta kuma saki rai suka shiga hirar arziki da hirar soyayyar su da bata kodewa, suna yi suna kallon kyakkyawar fuskar ‘yar su Hauwa (Waheedah) wadda suka saka a tsakiyar su tana barci da sauke numfashi cikin koshin lafiya. A lokacin Madinah da Sarham suka hau musu akan wanda Hauwa tafi kama dashi, shi yace da shi take kama completely, ita tace kalar su da gashin su ne kawai iri daya amma fuskar da yatsun, duk nata ne. Madinah a idon sa kadai ta fahimci ya jima bai ci abinci ba, amma da yake a dabi’ar shi baya dorawa matar sa nauyin ta tashi tayi masa girki a duk sanda yake so, sai bai mata complain ba, ita da kanta da yake ta san kan kayanta, ta gane sosai yake cikin gajiya da yunwa, don tun haduwar sa dasu Inna bai samu nutsuwar cin kyakkyawan abinci ba sam, don haka ta tashi ta hado masa abinci mai rai da motsi, sai da yaci ya koshi suka gaisa da Kakarta Haj. Lailah, wadda ke falo, sannan yayi musu sallama ya wuce asibiti don ya tadda su Hauwa ya ga farfadowar Inna, don haka daga nan Soron dinki can ya nufa. Saida ya tsaya a hanya ya yi musu sayayya sosai kamar yadda ya saba duk da ya lura Hauwa bata iya ci, yau sai ya saya mata fresh milk da yawa (unsweetened) kafin ya wuce aibitin. Da sallama ya murda kofar ya shiga dakin, bayan Inna tayi masa iznin shigowa, amma Hauwa a ciki ta amsa masa kamar yadda ta saba amsa sallamarsa tun fil azal, ya tadda su tare da Malam Isa ya zo dubata shi da dan gidan Inna wato Saleleh. Malam Isa har gidan su Salele ya je ya gaya musu an ga Innar Hauwa, shine fa Salele ya biyo shi. Inna ta dubi Sarham tana daga zaune jikin filo. Ba don ba karamin sani tayi masa ba da bata gane shi ba, don ya canza gabadaya daga yadda ta san shi, dan siririn saurayin likitan nan na Murtala, ya girma ya kara cika ido cikin shekaru kalilan, ilmi da kwarjinin addini sun kara bayyanar da cikar zatin sa. Tayi murmushi a hankali, ta ce. “Inda rai da rabo, likita Sarhamu! Ashe Allah yayi zamu gana?” Sarham ya ja kujera a gaban ta ya zauna, yana kallon Hauwa tana shafa hoda irin mai like da mudubinnan a jikinta, saura kadan ya fashe da dariya, kasa amsawa Inna maganar data yi yayi saboda dariya dake cinsa, ya nuna wa Inna ita da baki, itama tayi dariya, tace “kuma ayi magana cibi ya zama kari ba!”. Malam Isa ya juyo garesu yace “dariyar me kuke haka?” Inna tace “kai dai abar kaza cikin gashin ta, daga jiya zuwa yau na kirga shiga wankan ta ya kai goma! Wai biyan bashin wankan kwana bakwai da bata yi ba a kauyen Albasu take yi yanzu, tunda ta samu ruwan dumi da sabulu mai kamshi ai shikenan, har da yi wa Malam Sani Allah ya isa da yayi mata sanadin komawa zaman kauye”. Sarham yayi dariyarsa mai isarsa, har da sunkuyawa da rike ciki, sai lokacin Hauwa ta gane da ita suke. Ta dan dakata da shafa hodar, duk ta sha jinin jikinta, ga mudubin a hannun ta, kai sai ka rantse tana ganin fuskar ta cikin mudubin, jin sun kara ninka dariyar ta ji haushi, ta mike ta fita daga dakin sai Sarham ya mike ya bi bayan ta don ya bata hakuri.

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});