Chapter 78
Chapter 78
tayi abakin toilet ɗin batare da ta motsa ba,jahad dake zaune saman darduma,da alama ta kammala sallah,jikinta na a sanye da hijab Maroon colour,ta ɗaga hannayenta sama tana addu'a,tunkan ta kammala ta lura da halin da Sehrish ke ciki,tana shafa addu'ar da sauri ta miƙe ta tunkareta, "Sehrish!lafiya meya faru ne? A ɗan ruɗe ta tambayeta, Sehrish kuwa sam ta gaza buɗe bakinta tayi magana,saboda yanayin da ta shiga,gaba ɗaya jikinta yayi wani irin sanyi, Ruƙo hannunta jahad tayi tare da cewa"sehrish!wai lafiya?ki amsa mun mana"? Lumshe ido sehrish tayi a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya,daga bisani ta ɗan ware idanunta tana kallon fuskar jahad,dake tsaye agabanta, "Ko kin fama ciwonki ne"? Girgiza kai sehrish tayi alamar a'a,tukunna tace"Jahad,ina fitowa daga cikin toilet ɗinnan,naji gabana ya faɗi rass,kuma naji jikina gaba ɗaya yayi mun sanyi,bansan meya jawo hakan ba," "Ki cigaba da ambaton Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un acikin zuciyarki,In sha Allah babu abunda zai faru dake fa ce alkhairi,"ta ƙarasa maganar tare da janyo sehrish ɗin har izuwa gefen gadonsu ta zaunar da ita sannan tace"Ki kwantar da hankalinki,bari na ɗauko maki kayan da zaki sanya,". Amsa mata tayi da toh,kafin ta mayar da idanunta kan farin towel ɗin dake sanye ajikinta ta ƙura mashi ido tana kallonshi zuciyarta cike fal da fargaba,ita kanta batasan dalilin faruwar hakan ba, Jin an turo ƙopar ɗakinsu yasa tayi saurin ɗagowa don taga wanene,Hajiya azeema ce ta shigo hannunta ruƙe da shopping bag fara fuskar nan ɗauke da murmushi kamar wadda akayi ma albishir da gidan aljanna,murmushi sehrish ta saki da sauri ta miƙe tsaye tana gaisheta"Ina yini Aunty azeema," Bata amsa mata gaisuwar ba sae cewa tayi"me nake gani haka?Amarya sanye da towel,ko baki san cewa an ɗaura ba"? A ruɗe sehrish tace"Aunty azeema,bangane me kike nufi ba,naji kince an ɗaura"? dariya azeema tayi tare da cewa"su6ul da baka ne fa,Bansan ma na faɗa ba,inaso ince ko an ɗaura abincin lunch ne,ashe azmeen bata a cikin ɗakin nan," "Ina yini Aunty azeema,"jahad ce tayi maganar a yayin da take ƙarasowa wurinsu hannunta ruƙe da wasu riga da wando na turkey,da ta ɗaukko ma sehrish, "Lafiya lou jahad,in ce ko ke zaki sanya waɗannan kayan na hannunki," Girgiza kai jahad tayi tare da nuna sehrish tace"A'a bani zan sanya ba,Sehrish na ɗauko masu don ta sanya" Cike da Zolaya Aunty azeeema tace"kin ta6a ganin inda Amarya ta sanya waɗannan kayan a ranar ɗaurin aurenta"? Cike da mamaki suka haɗa baki wurin cewa"AMARYA KUMA!!"? da sauri Azeema tace"Kai,mantawa fa nakeyi,wani film na kalla yanzu,to yarinyar cikin film ɗince aka ɗaura ma aure,a yau juma'a batare da saninta ba,abunne ya tsayamun arai shiyasa nake ta sako zancen," Murmushi suka saki gaba ɗayansu,Jahad tace"Amma gaskiya na tausaya mata Aunty,meyasa za'ayi mata aure batare da saninta ba?To idan ita bata son Mijin da aka aura mata zata iya kashe kanta fa,'?yanayin yadda jahad tayi maganar fuskarta da alamun tausayi, Sehrish tace"Nima abunda nakeson cewa kenan,zai iya yiwuwa akwai wanda take so,hakan ba ƙaramin illa zaiyi mata ba," Murmushi hajiya azeema tayi tana kallonsu,har sai da suka kai ƙarshen maganar tasu,sannan tace"kun ce wani abu anan,amma idan mijin ya kasance kamar babban yayan ku fa?kuna tunanin akwai macen da zata iya rejecting ɗin aurenshi"? Kallon juna suka kuma yi,kafin jahad tace"Gaskiya zaiyi wuya Aunty azeema,ae babban yayanmu na daban ne shi ko acikin maza,zan iya cewa ma duk macen da ta mallake shi ba ƙaramar mai sa'a bace,ƴar baiwar ce,kuma ita jinin nasara ce,da ƙafar dama ta shigo duniya," Dariya sosai hajiya azeema tayi,jin yadda jahad ke zuzuta SGR, "Duk da ance abincin wani gubar wani,Zai iya yuwuwa ita yarinyar bata ra'ayin namiji irinsa,ba wai don bai kai ba...." Katseta hajiya azeema tayi da cewa"kamar ya kenan"? Sehrish taci gaba da cewa"yanzu kamar ace ita yarinyar,tafi son baƙin namiji dogo,sannan wanda baya tara sumar kai,kuma tafi son namiji mai yawan fara'a a fuskar shi,ko kuma ace ita yarinyar tafi son ta auri wanda bai ruƙe da muƙamin soja,Ya abun zai kasance?zatayi farin ciki idan ta samu kamar babban yayanmu,amma ta wani 6angaren baiyi dai dai da ra'ayinta ba," Tana kai ƙarshen maganar,Azeema tace"kamar ke kenan!kina nufin bakison namiji kamar babban yayan ku"? Tayi tambayar cike da fargabar amsar da Sehrish zata bata, Sunnar dakai ƙasa sehrish tayi tana wasa da yatsun hannunta,yayin da fuskarta ke ɗauke da ƙayataccen murmushi,wannan ya tabbatar mata da cewa Tana RA'AYINSA, Dariya hajiya azeema tayi tare da ɗago da shopping bag ɗin dake hannunta ta miƙe ma sehrish, "Wedding gown ce aciki,tare da takalmanta,Zuwa bayan la'asar,da zarar an kammala sallar,Zanzo in taimaka maki wurin sanya rigar,sannan da kaina zanyi maki kwalliya," A ruɗe sehrish ke kallonta don bata gane inda zancen nata ya dosa ba,ita kanta jahad abun ya ɗaure mata kai, Ganin yadda suka saki baki suna kallonta,yasa tayi saurin cewa"Oh,na manta ban sanar daku ba,Wani wasan kwaikwayone zamu yi yau acikin gidan nan don nishadi,that's why we choose you to be our bride in the drama," Wani irin farin cikine ya lullu6e sehrish,cike da zumuɗi ta kar6i bag ɗin,tana fadin"Amma abun zai ƙayatar sosai,dama inason inga na sanya wedding gown,Ashe da rabon yau in sanyata, Jahad tace"gaskiya abun zai bada citta,yau kam zamu sha hotuna," "Har ma video idan kunaso zaku iyayi,Ni bari na wuce kitchen wurin Azmee,". Tana ƙoƙarin fita,ta tuna da hosana da sauri ta juyo tare da kallonsu tace"Ya jikin hosana?naga sae bacci take tayi tunda nashigo,da alama jikin yayi sauƙi kenan"? Jahad tace"eh,taji sauƙi sosai," "To,ku ya jikin naku"? "Ae mu munji sauƙi,"suka haɗa baki wurin bata amsa, Jinjina kai tayi tare da kama hanyar fita tana cewa"Allah ya ƙaro sauƙi," Suka amsa mata da cewa"Ameen," A saman gado sehrish ta ajiye shopping bag ɗin,sannan ta kar6i kayan da jahad,ta ɗauko mata batare da 6ata lokaci ba ta zura riga da wandon ajikinta Red colour ne ba ƙaramin kyau suka yi mata ba,gaban dressing mirror taje wurin da ta ajiye ribbom ɗinta before ta shiga wanka ɗaukarsa tayi tare da zura shi acikin hannunta,sai da tafara tattara gashin kafin ta sanya ribbom ɗin ta ɗaure shi tamau, "Ko dai in tashi hosana,tayi wanka itama?kin ga ko sallah batayi ba,"acewar jahad, Sehrish tace"ko baki tasheta ba,Yunwa zata tayar da ita,kibarta kawai,kada ki tado mana jangwamgwam," "Baiwar Allah ni tausayi take bani,duk in na tuna yadda ta samu ciwon haukanta,sai inji idanuna sun cika tab da kwalla,"acewar jahad, Sehrish tace"Ni kaina ina tausaya mata sosai,Amma inaji araina cewa,Wata rana hosana zata dawo cikin hankalinta ne,sannu a hankali,Haka muke fata in sha Allah, Suna cikin magana,Jiniyar motocin dake shigowa cikin gidan ta karaɗe kunnuwansu,da ƙarar gaske har cikin dodon kunnuwansu, "Su babban yaya ne suka dawo daga sallar juma'a,bari in leƙa inga wankan daya ɗauka yau,!" Cike da farin ciki sehrish tayi maganar tare da juyawa ta nufi window,jahad ma tabi bayanta,janye labulan sukayi sannan ta zuge masu glass ɗin,Baza idanunsu sukayi suna kallon abunda ke wakana a farfajiyar gidan, Da gudun gaske motocinsu ke shararowa saman titin da zai kawo ka har wurin parking space na gidan,tun daga bakin gate titin ya fara, "Wlh abun kamar a shirin film" jahad ce tayi maganar,abun ba ƙaramin burgesu yayi ba, Lokacin da motocin suka ƙaraso ciki,a wani slow suka tsaya a jere,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243
- 244 Chapter 244
- 245 Chapter 245
- 246 Chapter 246
- 247 Chapter 247
- 248 Chapter 248
- 249 Chapter 249
- 250 Chapter 250
- 251 Chapter 251
- 252 Chapter 252
- 253 Chapter 253
- 254 Chapter 254
- 255 Chapter 255
- 256 Chapter 256
- 257 Chapter 257
- 258 Chapter 258