Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 119

Chapter 119

Abban Sojoji Takun Kaarshe 3 Complete Hausa Novel 1,351 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mashi da hankali yace"pls baba,dan Allah ka koma ka zauna muyi magana atsanake," Rai a6ace malam Nura yace"Idan maganar wannan fasiƙin mutumince ta kawoku to ku tattara kubarmin gidana!Banason ganinku,banason ganin duk wani abu daya shafe shi,ku fuce kawai tun kafin ranku ya 6aci a wurin nan "yana magana jikinshi na kerma saboda tsabar 6acin rai, Ganin yana ƙokarin korarsu yasa sehrish miƙewa tsaye cikin sanyin murya tace"Baban sadeeq,Ka manta da ƴan ukun zainabu abu da ta haifa"? Mayar da hankalinshi yayi sosai akanta yana kallonta, "Ni ɗaya ce daga cikinsu,nasan baka manta damu ba,Nice Sehrish ƴar uwarsu Jahad da Hosana" Cike da mamaki Malam nura ke kallonta,hannunshi na kerma ya nunata da ɗan yatsanshi daƙyar ya iya furta cewa"kek..ke..ƴar wurin zainabu abuce? Jinjina mashi kai tayi alamar eh,tace"Ni ce SEHRISH Baban sadeeq,su jahad ma suna nan araye," Wasu irin zafafan hawaye ne suka soma sauka akan fuskar malam nura,ruƙo hannunta yayi yana kallonta,la66ansa sae kerma sukeyi,yayi matuƙar mamaki ganin yarinyar,bai ta6a tsammanin cewa yaran zasu rayu ba,abun yayi matukar daure mashi kai, Cikin shessheƙar kuka yace"Allahu akhbar!Wai dagaske ƴa'ƴan abu suna araye a doron duniyar nan?Dagaske ne abunda idona suke gane mun kuma suke jiyomun!Ya Allah kasa ba mafarki nake yi ba,"kuka sosai ya fashe dashi,duk yabi ya ruɗe bawan Allah, Kama hanyar shiga cikin gidan yayi,yana kwaɗama maman sadeeq kira"Murja!!murjanatu!kina inane kizo dan Allah,Ki ganemun wannan abun al'ajabin,Yau gani ga jinin zainabu abu har cikin gidana,Abun da muka daɗe muna jira,yau Allah ya amsa addu'armu" Jin wannan maganar ta Baban sadeeq yasa Maman sadeeq ta miƙe zumbur daga zaunen da take saman sallaya,buguzun buguzun ta faɗo cikin zauren,turus ta tsaya abakin zauren tana ƙarewa Abusufyan da Sehrish Kallo, Malam nura yace"kin gani ko?Yaran nan sun rayu,Wahala batasa sun mutu ba,dama nasha faɗa maki cewa Allah yana tare dasu a duk inda suke,Allah shi zai kula da abunshi,Yau dai maganata ta tabbata,kalli ki gani wannan yarinyar ƴar wurin zainabu abu ce fa,Sehrish ce"yayi maganar yana nuna mata sehrish, Hannu murja tasa ta daki ƙirjinta tare da Ambaton sunan Sehrish da ƙarfin gaske, Da gudu sehrish ta ƙarasa wurinta suka rungume juna,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,kamar ransu zai fita, Tuni idanuwan Abusufyan sun cicciko da kwalla,shi kanshi baisan lokacin da hawaye suka wanke mashi fuskarshi ba, Gaba dayansu sun shiga cikin wani irin yanayi na ban tausayi,kowa da abunda yake tunawa acikin ranshi, Cikin shessheƙar kuka Maman Sadeeq ta dafa kafaɗun Sehrish tana faɗin"Ashe rai kanga rai!Rishi kece kika girma haka?lallai Allah Al musawwir ne,Kalli yadda rayuwa ta sauyaki,Ban manta lokacin da kuke rayuwa a wulakance ko takalma babu a kafafuwanki,Ya Allah na gode maka daka nuna mun wannan ranar,Yau gani ga ƴa'ƴan aminiyata zainabu abu,Wayyo Allah farin ciki,"zubewa ƙasa tayi ta fuskanci gabas tayi sujjada tana kuka tana godewa Allah,hakan ba ƙaramin ta6a masu zuciya yayi ba, Sun ɗauki tsawon lokaci suna wannan koke koken,kafin daga bisani komai ya lafa,Saman tabarmar suka koma suka zauna,cike da jimami,kowa yayi shiru na ɗan wani lokaci, Kafin Abusufyan ya soma magana"Baba waɗannan ƴaran ƴa'ƴana ne,bana sayyadi ba,Ya yaudaremu ne gaba ɗayanmu ya auri abu da cikina,batare da saninmu ba,Wannan shine silar duk wani abu daya faru a rayuwarsu...." Tunkan ya ƙarasa maganar Baban sadeeq yace"Dama najima ina zargin cewa,ƴan ukun nan bana shi bane ashe dagaske ne,Ya Allah kayi mana maganin Fasiƙin mutumin nan,Ka kawo mana ƙarshen shi,Mugu azzalumi ya jima yana cutar rayuwar yaran nan,In sha Allah ƙarshen shi bazaiyi kyau ba,"ranshi a 6ace yake yin maganar, "Sehrish ina Hosana take baiwar Allah"Maman sadeeq ce tayi maganar har lokacin hawaye ne ke shararowa akan fuskarta, "Duk suna nan lafiyarsu ƙalou muna atare dasu cikin danginmu," Murmushi Maman sadeeq ta saki tare da cewa"Allah sarki,rayuwa kenan," "Baba ko kuna da labarin Abu"?Abusufyan ya jefo masu tambayar, Gabansu ne ya faɗi atare suka kalli juna jin tambayar da Abusufyan yayi masu, Hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,tun daga kan irin kallon da yaga sunyi ma juna yasa shi shan jinin jikinshi,. Hankalin Sehrish a matuƙar tashe tace"Dan allah,ku faɗamana a ina Oummanmu take?nasan kuna da masaniya akai," Shiru sukayi batare da sun basu amsa ba,nan take Sehrish ta fashe da kuka tana cewa"dama nasani,zai yi wuya mu sameta araye,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un," Ƙiriss ya rage zuciyar Abusufyan ta buga,zumbur ya miƙe yana ƙoƙarin barin wurin,hannunshi dafe da saitin zuciyarshi, Muryar Baban sadeeq ce ta katse mashi hanzarinshi, "ABU TANA RAYE," jin wannan maganar yasa,Abusufyan komawa dirshan ya zauna,muryarshi har shaƙewa take yi wurin cewa"dagaske abuna tana araye?dan Allah ku faɗamin gaskiya,abu tana raye?tana ina?a ina zan ganta?" A natse baban sadeeq ya soma kora masu jawabi, "Tun bayan lokacin da Hosana tayi jinya a asibiti sakamakon Buguwar da kanta yayi harta samu ta6in hankali,nasan kunji labarin nan a wurinsu Sehrish,"ya ɗan dakata dayin maganar yana kallon fuskokinsu, "Hakane,munji komai a wurinsu,"a ƙagare Abusufyan yayi maganar,jikinshi sae tsuma yake yi,ita kanta sehrish ta ƙosa taji abunda zaice, "Tun bayan da aka kwantar da Hosana gadon asibiti,lokacin ana ƙoƙarin tattara kuɗin da za'ayi mata aiki,kwatsamm aka nemi mahaifiyarsu aka rasa ƙasa ko sama,tun bayan da ta sanar masu cewa zata je gida ta sanar da sayyadi halin da yarinyar take ciki don tunda aka kwantar da ita bai leko asibitin ba da tunanin ko asamu wani abu daga wurinshi,Don acika ayima yarinyar aiki,tunda ta haura ƙafa tabar asibitin bamu ƙara jin ɗuriyarta ba," Shiru ya ɗan yi yana sauke ajiyar zuciya kafin ya daura da cewa"A lokacin Hankalin mu ba ƙaramin tashi yayi ba,ga yarinya ba lafiya kwance gadon asibiti rai hannun Allah,Ga sauran ƴan uwanta dake a cikin ƙuncin rayuwa na rashin ganin mahaifiyarsu da basu yi ba har tsawon kwanaki,wannan yasa muka bazama neman abu acikin unguwar nan,Saƙo da lungu ba'a sameta ba,Gashi gidansu a garkame da kwaɗo,har muka fara tunanin cewa kodai Abu ta gudu ne tabar yaranta,wata'ƙil damuwace tayi mata yawa,shiyasa ta ta tafi tabarsu,Jinyar hosana ta koma hannun Maman sadeeq itace taci gaba da kula dasu a asibiti," Dakatawa ya ɗan yi da jawabin,na wani lokaci kafin yaci gaba da cewa"Ana haka,wata rana na dawo daga masallaci,ina ƙoƙarin shiga gidana,sae ga wani yaro nan,Umari ɗan wurin makwabcinmu ne shima,Yana tsaron shagon mahaifinshi abakin hanya,shi ya tare ni yayi mun sallama,Na juya na amsa mashi sallamar,yace mun malam inason magana dakai,game da Matar mutumin nan makwabcinka,Ya sayyadi,koda naji ya ambaci hakan sai na mayar da hankali sosai akanshi nace mashi"ina sauraronka,Anan ne yake sanar dani cewa,Ya gamu da abu akan hanya tana hauka babu takalma a kafafunta babu mayafi a jikinta,tana kuka tana sambatu tana fadin cewa Ya kashe mun babana,Ya rabani da mijina!kuma zai kashe mun ƴa'ƴana,'lokacin da Umari ya sanar dani wannan maganar hankalina ba ƙaramun tashi yayi ba,tun kafin ma ya ƙarasa maganar,jiki na rawa na hau babur ɗina na koma asibiti,a gaggauce na tattara yaran nan,nasa aka kaisu katsina wurin kishiyar babata,bakomai yasa nayi hakan ba,sai don gudun kada kalaman Zainabu abu su tabbata da gaske,Saboda a nazarin da nayi,wannan sambatun da akace tana yi yana da alaƙa da haukanta,Tabbas ya sayyadi shine yayi silar mutuwar mahaifinta,shiyasa har abun ya tsaya mata aranta,kuma ya ta6a mata zuciya har ta samu ta6in hankali,wannan dalilin yasa na ɗauke yaran gaba ɗaya na mayar dasu

Table of Contents

Chapters

258 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
  244. 244 Chapter 244
  245. 245 Chapter 245
  246. 246 Chapter 246
  247. 247 Chapter 247
  248. 248 Chapter 248
  249. 249 Chapter 249
  250. 250 Chapter 250
  251. 251 Chapter 251
  252. 252 Chapter 252
  253. 253 Chapter 253
  254. 254 Chapter 254
  255. 255 Chapter 255
  256. 256 Chapter 256
  257. 257 Chapter 257
  258. 258 Chapter 258
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});