Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Abban Sojoji Takun Kaarshe 3 Complete Hausa Novel 1,357 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da bubbuga ƙafafuwansu"jahad!hosana!ku tashi ana son ganinku," cikin bacci hosana ta buga tsoki tana fadin"dan Allah a ƙyale ni,kar a takuramin," Jahad kuwa tuni ta farka,tana faman mutsustsuka idanuwanta,wurga idanunta tayi kan sehrish tace"Wai lafiya"? "Wannan ce ke son magana daku,"tayi maganar tana nuna hafsat dake zaune, Juyawa jahad tayi tana kallonta,cike da mamaki ta ambaci sunanta"Aunty hafsat!" sunnar dakai ƙasa hafsat tayi,fuskarta dauke da matsananciyar damuwa,daƙyar ta iya amsa mata"Na'am jahad,"tashi zaune jahad tayi,suna fuskantar juna ta sake ambatar sunanta"Aunty hafsat," "Kinsanta ne"? Sehrish ce tayi tambayar,jahad tace"Niko na santa,itace ɗiyar wannan matar da nake faɗa maki wadda ta azabtar da rayuwarmu,kuma wannan itace ta ɗauke mu acikin motarta,ni da Hosana ta kai mu hannun wannan mugun mutumin wanda ya kai mu daji har yayi ƙoƙarin cutar da Hosana," Jin wannan maganar yasa ran sehrish ya 6aci,harara ta wurga ma hafsat tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace"Dan Allah malama tashi ki fita ki bamu wuri!bamu son ganinki!mugaye kawai Azzalumai,kun cutar da rayuwar ƴan uwana,saboda son zuciya irin naku,basuyi maku laifin komai ba,Amma kuka tsangwamesu,saboda kunga basu da gata,Insha Allah sai kunga sakayyar da Allah zaiyi masu,kuma sai kun ɗanɗana irin uƙubar da kukayi masu," Hawaye ne suka shiga zarya a fuskar hafsat,dama saida ranta ya bata cewar dakyar ne su yafe mata, Janye idanunta tayi daga kan sehrish ta mayar dasu kan Jahad,cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ku yafe mun Jahad,nasan mun cutar daku,amma inaso ku sani bada son raina ba,na kaiku wurin wannan mutumin,Mommy ce ta sanar dani cewa Gidan marayu za'a kaiku,shiyasa har na ɗauke ku,kuma nayi hakan ne saboda tsoran karta halakar daku acikin gidan nan don ba yadda banyi ba akan ta kyale ku amman ta kiya,shiyasa ma na amince da akaiku gidan marayun ashe zubar daku tasa ayi,' "Ba zamu ta6a yarda da kalamanki ba,saboda tun farko baki nuna kina son mu zauna acikin gidan ba,ke da mommynki,shiyasa kuka haɗa baki ke da ita,kika fara yaudararmu kina nuna kamar kina son mu ashe,so kuke ku fitar damu daga cikin gidan,saboda rashin Imani Aunty hafsat kika damƙa mu a hannun wannan mutumin,to bari kiji Ya Omar ya kashe shi har lahira!! Gabanta ne ya faɗi rassss!hankalinta yayi mugun tashi,a kiɗime tace"Ya kashe shi!" Jahad tace"kwarai kuwa Ya Omar shi ne ya kama shi da hannun shi acikin gidan gonarsa,lokacin da yake ƙoƙarin keta haddin hosana,aikuwa ya fasa mashi kai,anan wurin ya zama gawa,' Tana kai ƙarshen maganarta sehrish ta ɗaura da cewar"tun yanzu kwara kusan inda dare yayi maku!don wlh Ya Omar bazai sassauta maku ba!muddin yaji cewar kune kukayi silar da har wannan mutumin ya ɗauki su jahad ya kaisu daji,sannan ku fara tunanin irin hukuncin da kuma zaku fuskanta a wurinshi!" Wani irin wahalallan yawu hafsat ta haɗiya,tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,ba don komai ba sai don jin cewa An kashe mutumin nan!tun da har Omar zai iya kashe rai akan su hosana,tabbas ba ƙaramin so yake masu ba,kuma akansu zai iya hukunta kowa,yanzu su menene sakamakonsu? "Baku da wata mafita,shawara nake baku tun kafin hosana tayi maku tonan asiri,kwara kusan abunyi,don tace saita sanar ma Daddy da Ya Omar abunda kukayi mana!" jahad ce tayi maganar, Gaba ɗaya duk sun bi sun tsoratar da ita,la66anta har kerma suke wurin rokonsu tana cewa"Dan Allah ku yafe mun,wlh nayi dana sanin duk wani abu da mu kayi maku,har ga Allah ni bada sanina ba,mommy ce ta shirya duk wannan,Allah shine shaidata,bazan yi maku ƙarya ba,"sosai hafsat ke kuka, Ruko hannun jahad tayi acikin nata tana fadin"jahad nasan kina da sauƙin kai,dan Allah ki yafe mun,wlh nayi nadamar abunda mu kayi maku ni da mommyna,nasan naƙi ku da farko amma daga baya naso ku sosai,kuma nayi kukan rashinku atare dani,lokacin da nagane cewa Mommy ba gidan marayu tasa akaiku ba,har faɗa sai da mu kayi da ita,ko isasshen bacci bana samu a lokacin saboda tunanin wani hali kuke ciki......"ƙarasa maganar tayi tare da sanya hannu tana share hawayen dake zuba a kan fuskarta, Shiru su kayi da alama jikinsu ya ɗanyi sanyi,Sehrish tace"Jahad,idan kinyi niyya ki yafe mata,'jinjina kai jahad tayi tare da cewa"Ni dama ban ruƙe ki araina ba Aunty hafsat,na yafe maki Allah ya yafe mana gaba ɗaya," Amsawa tayi da "Amin,sannan tace"Hosana fa?dan Allah ku tashe ta inaso in nemi yafiyarta," Hannu Sehrish takai tare da bubbuga ƙafarta,farkawa hosana tayi,idanunta sunyi suntum saboda bacci, "Hosana ki tashi,ga Aunty hafsat nan tana son magana dake,"jin an ambaci sunan Aunty hafsat yasa ta wartsakewa ta miƙe daga zaune,koda idanunta su kayi arba da fuskar hafsat,nan take ta murtuke fuska rai a6ace tace"Ni bana son ganinta,na tsaneta kamar yadda suka tsane mu ita da Mommynta,Aunty hafsat muguwace bata tsoron Allah,itace takai mu wurin wannan mummunan mutumin wanda yakusa kashe ....."katse ta jahad tayi da cewa"pls hosana just forget about the past,forgive her pls,Aunty hafsat tayi nadama,kuma bada son ranta ba ta kaimu wurin mutumin nan ba,Mommynta ce ta shirya wannan," Maƙe kafaɗa hosana tayi alamar bata yarda ba,harara ta wurga ma hafsat ɗin tana murguɗa mata baki tace"Allah saina faɗama Ya Omar da daddy,ko kukan jini zatayi sai dai tayi,amma saina faɗa,saboda rashin Imani kamar wasu dabbobi haka kuka rufe mu acikin store babu abinci ga ƙishin ruwa,ko iska babu,amma ko ajikin ku mu rayu ko mu mutu wannan ba matsalarku bace,zafi kamar zai kashe mu,adaren ranar da muka kwana a store,ba don jahad tayi mun fifita ba da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya don rashin imani ku kuna can kuna shan A.c,wlh saina faɗama daddy....."fashewa hosana tayi da kuka,hada bubbuga ƙafarta,daga gani abun ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba,ya tsaya mata arai, Gaba ɗaya jikinsu yayi wani irin sanyi,musamman hafsat,duk yadda taso ta shawo kanta amma abun yaci tura,hosana ta rantse ta maya akan cewar saita faɗa ma Ya Omar,hatta jahad sai da taso ta lallasheta,amma ina ƙarshe sai ta dinga ƙoƙarin bugun jahad din, Ganin haka yasa sehrish kallon hafsat tare da cewa"dan Allah kiyi haƙuri ki tafi kawai,hosana batasan ganinki,idan tana kallonki haukanta zai iya tashi," Jiki asanyaye Hafsat ta mike,tana tafiya tana waiwayonsu yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,a haka har ta isa ƙopar ɗakin ta buɗe ta fuce da gudu tana kuka, Hannu Sehrish tasa tare da janyo hosana ta rungumeta sosai ajikinta tana lallashinta,da ƙyar ta samu hosana tayi shiru,sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,komawa su kayi suka kwanta kowa da abunda yake saƙawa aranshi, *Aunty Babba* Suna kwance ita da hayaam sai faman sharar bacci sukeyi suna jan minshari yadda kasan bijimayen sa,sun cika gadon su biyu kawai,babu wanda ya farka acikinsu balle suyi tunanin yin sallar asuba,can cikin bacci Hayaam ta dinga jin ana bugun ƙopar ɗakin nasu tamkar za'a balle ta,dogon tsoki taja tana faman yatsina fuska alamar an takurata,a ƙule tace"Wai dallah wanene ke buga ƙopar ɗakin nan"!? Muryar hafsat tajiyo daga waje cikin shessheƙar kuka tace"Ni ce,ki zo ki buɗe mun ƙopa," Jiki na rawa hayaam ta saukko daga saman gadon ta ƙarasa tare da buɗe ƙopar,gabanta ba ƙaramin faduwa yayi ba ganin fuskar hafsat sharkaf da hawaye,hankali atashe tace"Meya faru ne kike kuka"? A tsiwace hafsat tace"Ba dole inyi kuka ba!kun jefani cikin masifa!ki bani hanya na wuce,Da Mommy nake so inyi

Table of Contents

Chapters

258 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
  244. 244 Chapter 244
  245. 245 Chapter 245
  246. 246 Chapter 246
  247. 247 Chapter 247
  248. 248 Chapter 248
  249. 249 Chapter 249
  250. 250 Chapter 250
  251. 251 Chapter 251
  252. 252 Chapter 252
  253. 253 Chapter 253
  254. 254 Chapter 254
  255. 255 Chapter 255
  256. 256 Chapter 256
  257. 257 Chapter 257
  258. 258 Chapter 258
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});