Chapter 41
Chapter 41
daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren batare da sanin kowa ba,ita kanta hajiya ameenatu batasan na halarci ɗaurin auren nasu ba,a iya waya kawai ta sanar dani,sae kuma akaci sa'a ina da wani taron manyan malamai da zamu halarta anan jihar kano,wannan ne babban maƙasudin daya kaini garin harna shaida wannan ɗaurin auren....." Ae tunkan modibbo yakai ƙarshen maganar wani irin murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskar kowannansu,saboda yayi maganar ne cikin harshen da zasuji,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya abusufyan ya shiga saukewa,nan take yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarshi,duk da yayi mamakin zuwan modibbo wurin ɗaurin auran nashi saboda bai ganshi ba,amma tunawa da irin dubban al'ummar dake a masallacin kuma ya kasance ranar juma'a ne ana kammala salla aka ɗaura auren nasu,tabbas bazai iya tantance kowa dake a wurin ba,amma ko a lokacin bayan an ɗaura auren sun koma gida sai da baba buzu ya kirashi gefe guda yake sanar dashi cewa"Wani babban malami,yayi mashi alheri bayan sun fito daga masallaci,kuma yana tunanin cewar Kamar jininsu ne saboda yaga kamannin Hajiya ameena a fuskarshi,a lokacin Abusufyan bai gane wanene ba,sai yau da modibbo yayi maganar nan kwatsam ya zancen ya faɗo mashi aranshi bayan ya shiga zurfin tunani,tabbas kuwa modibbo ne, Murmushi modibbo yayi tare da kallon Abusufyan yace"nasan zakayi mamaki,saboda nazo ɗaurin auren ka batare da sanin kowa ba,uzuri ne ke gare ni a lokacin shiyasa ban nemeka ba,don nasan muddin ka ganni a lokacin saika nace akan in tsaya," ya ƙarasa maganar tare da mayar da idanunshi kan Ammi,tun kafin ya kuma cewa wani abu,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Amma yaya kasan da maganar auren nashi shine ba'a sanar dani ba?saboda me? "Saboda halinki"! Kai tsaye ya bata amsa, "Tabbas naso in sanar dake ko alokacin,saboda kinsan cewa ni bana jin shakkarki,hajiya ameenace ta rokeni akan cewar karna sanar dake,saboda hakan zai iyasa ki fusata harma ki yanke ma Abusufyan hukunci mai tsanani,kuma a ƙarshe zumuncin dake tsakaninki da ita ya tarwatse,dana nace akan zan sanar dake har kuka saida tayi mun,wannan dalilin ne yasa ban sanar dake ba,kuma ana haka daga baya kwatsam naji labarin mutuwar auren Abusufyan ɗin,hada ƙarin haka yasa akabar zancen gaba ɗaya,ashe yarinya ta fita da cikinsa ta auri wani,to kinji dalilin dayasa mu kanmu bamu san da ya'yan nashi ba,har suka kai wannan girman a hannun mijin da ta aura daga baya," Dakatawa yayi da maganar,falon yayi shiru na wani lokaci,kafin ya mayar da idanunshi kan Sgr dake zaune,yace mashi"ka kunna mata audio din nan daka kunna mun itama ta saurare shi," "Okey,"ya amsa mashi tare da,daddana wayar hannunshi,ya shiga audio din tare da kunnashi,sannan ya miƙe tare da ƙarasawa kusa da kujerar da Ammi ke zaune ya miƙa mata wayar,yatsun hannunta na kerma tasa hannu ta kar6i wayar tashi,ta ajiye asaman hannun sofa ɗin tana sauraronshi,wannan audio din na labarin da abusufyan ya bayar ne da kuma Labarin dasu sehrish suka bayar na irin ukubar da suka sha a hannun ya sayyadi,ashe ranar da abun ya faru,Sgr ya ɗauki audio na maganganun da sukayi kaf acikin wayarshi,tabbas shi ba ƙaramin jami'in Soja bane!yana Aikinsa wani lokacin tamkar jami'in sirri,Na jinjina masa,da irin baiwar da Allah yayi mashi da kuma irin kwazon dake gare shi,ta ko ina Sgr ya haɗa,shiyasa nace maku shi ɗin komai nasa Extraodinary ne~~~ Miƙewa junaid yayi tare da ruƙo hannun Mommynsu yace"Shikenan mommy tunda mun kammala discussion din,ki taso muje falo pls,kada kice baki zuwa,in ba haka ba raina zai 6aci,wlh ko abincin dare bazanci ba,indai kika ƙi zuwa gaishe da modibbo," Cike da mamaki tace"Modibbo?kana nufin mahaifin maryam oummunsu Omar? daga mata kai yayi alamar eh, Shiru tayi tana wani tunani,a iya saninta modibbo mutunne mai mutunci sosai,saboda shine ya taka ma Ammi burki a lokacin da taso Abba ya sake ta,tabbas bazata ta6a mantawa da halarcin da modibbo yayi mata ba, Ganin ta miƙe yasa junaid sakin murmushi yace"mommy zaki ko"? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, Janyo hannunta yayi har suka ƙaraso falon,ganin hankalin mutanen dake acikin falon gaba daya yana akan Audio din da ammi ke saurare,hakan yasa itama ta samu wuri ta zauna,junaid ma ya zauna gefenta,yayin da idanunshi ke akan su sehrish,sam basu lura dashi ba saboda hankalinsu duk ya tashi,a sakamakon Audio din da aka kunna,saboda sun tsani jin labarin rayuwarsu,ko miskala zarratin, Kowa ya natsu yana sauraron audio ɗin,lokacin da Abusufyan ya kammala bada tarihin rayuwarshi da abu,sai next audio ɗin ya shiga wanda Jahad ke bada labarin rayuwarsu,nan take hankalin AMMI yayi mugun tashi,jikinta har tsuma yakeyi,tuni wasu siraran hawaye suka shiga zarya a kuncinta,ita kanta Alexandra jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,tunda take arayuwarta bata ta6a jin tausayin wani ɗan adam ba,daga ita har ammin kamar yadda sukaji tausayin waɗannan bayin Allahn ba,Very heart touching story,wanda duk wani mai imani In ya saurareshi dole ya zubda hawaye,in ma baiyi kuka ba, Ganin yadda hawaye ke sintiri akan fuskar AMMI yasa Omar ya cire hanky daga aljihunsa ya miƙa mata,dama kamar yasan cikin buƙatarshi take,a fuskarta ta kifa hankacif ɗin,ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai,kowa yayi mamakin yadda Ammi ke kuka,cikin shessheƙar tace"ku kashe mun audio din nan ya isa haka,kunnuwa na bazasu iya jurar jin wannan tashin hankalin ba,' dama Audio ɗin yazo ƙarshe,junaid ne ya mike ya ɗauki wayar,tare da miƙa ma babban yayansu ita,ya kashe audio ɗin, "Shiyasa akeso ko da yaushe mutun ya kasance mai sauƙin kai,kada ya cika tsaurara al'amurransa,yanzu da ace banzo ba,da shikenan,haka zaki kora yaran nan,ke baki tsaya kinyi bincike ba,kuma baki saurari bayani daga gurin kowannansu ba kawai kin tashi kin yanke hukunci,sai daga baya kuma kizo kina danasani" daƙyar ammi ta iya furta"Astagfurullah Allah na tuba!ka yafe mun,rashin sani ne yasa na kirasu da shaggu,game da halin da yaran nan suka tsinci kansu,duk laifin mahaifinsu ne,shine silar komai,duk da daman Allah ya ƙaddara faruwar hakan babu wanda ya isa ya hana,amma Abusufyan bai kyauta ma rayuwarsu ba,meyasa bai sanar ma kowa ba don aɗauki mataki?saboda kawai yayi mashi barazana?Amma dai Allah ya tsine ma fasiƙin mutumin nan,Wlh bazan barsu ba,saboda me laifin kakansu zai shafe su?wannan wata irin mugunta ce mara kan gado,?bai tsaya a iya kan ya'yan salahudeen ba,hada jikokin duka yake ɗaukar fansa akansu,?kuma shima salahudeen ɗin daya kashe mahaifinsu ae don saboda mugayen laifukan da aka kamasu dashi ne,ɗaukar fansar ta mutun ukuce suke ɗauka,mahaifinsu da kuma mahaifiyarsu,da kuma wannan ɗan koran nasu,dukkansu Allah zai toni asirinsu,' Jinjina kai modibbo yayi yana sauraronta saida takai ƙarshen maganarta,tukunna yace"ba komai ne yasa na tako nazo ƙasar nan ba,face don abu uku,kuma ina fata zaki bani haɗin kai domin asamu maslaha atsakaninku gaba daya,saboda baza a ta6a cin nasarar gano waɗannan masu ɗaukar fansar ba,har sai ku na cikin gidan kun fara haɗa kanku,in ba haka ba,munafukan dake shirya maku zagwan ƙasa zasu samu nasarar cin galaba akanku,ta hanyar rarraba kawunanku,saboda ni inaji araina cewar masu shirya wannan maƙarƙashiyar suna ATARE DAKU!sun shiga cikinku,suna acikin rayuwarku!' Wannan maganar ba ƙaramin jijjigasu tayi ba,don sai da kowannansu ya ɗago yana kallon fuskar modibbon, "Nasan zakuyi mamaki amma nan gaba sannu a hankali zaku shaida maganata,yanzu dae bari inyi abunda ya kawoni," "AISHA" Ya ambaci sunan Ammi,muryarta asanyaye ta amsa mashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243
- 244 Chapter 244
- 245 Chapter 245
- 246 Chapter 246
- 247 Chapter 247
- 248 Chapter 248
- 249 Chapter 249
- 250 Chapter 250
- 251 Chapter 251
- 252 Chapter 252
- 253 Chapter 253
- 254 Chapter 254
- 255 Chapter 255
- 256 Chapter 256
- 257 Chapter 257
- 258 Chapter 258