Chapter 180
Chapter 180
take maganar a hankali, "Never mind,"yayi maganar batare da ya buɗe idanuwanshi ba,Juyawa Sehrish tayi da sauri ta nufi hanyar fita falon,Sai da ya tabbatar tabar wurin tukunna ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da waigawa yana kallon bayanta,har sai da ta fuce daga falon, A 6angarensu Hayaam da Abra waɗanda tun jiya suka bar Abuja,Abun da ya faru lokacin da suka isa unguwarsu,wuraren marece tunkafin Su shiga gidansu suka lura da yadda mutane ke kallonsu,tun daga nan suka sha jinin jikinsu,Har nunasu akeyi da hannu ana cewa gasu can sune ƴa'ƴanta,Sun dawo daga yawon biɗiɗin nasu,Wlh anyi asarar Rayuwa,wasu kuma na cewa,Ae laifin uwar tasu ne da bata basu tarbiya ba ita ta lalatasu,Lokacin da suka ƙarasa ƙopar gidansu,A buɗe suka samu gidan,Da sallama suka shiga sunyi tunanin za'a amsa masu amma sai suka ji shiru,gidan babu kowa,komai na gidan babu,An kwashe komai,hatta butoci da bokatai babu,Har kan fanfonsu an 6alleshi, Nan fa hankalinsu yayi mugun tashi,Tun a tsakar gidan Abra ta saki trolley ɗin hannunta,da gudun gaske suka shiga cikin ɗakunan suna kwalawa Mammynsu kira,Mammy! Mammy!!gabansu ne ya faɗi ganin ɗakin mammynsu babu komai wayam hatta katifarta,yanke shawarar zuwa makwabtansu Suka yi donsu tambayi Ina mammynsu taje ne, Suna zuwa zauren gidan suka fara jiyo hayaniyar mutane,kasa kunne suka yi suna sauraran Surutun mutanen da sukayi masu dandazo a ƙopar gidan, "Kuna ina la'anannu!waɗanda basu son ciwon kansu ba,Ku fito muci ubanku inba haka ba Mu ƙona gidan da fetur,kun tafi kun barmu da bala'e acikin unguwa,Yau sai mun fanshe haushinmu akanku,Jinin ku ya halatta" Jin wannan yasa tsoro ya kamasu,da gudu suka Koma cikin gidan,A ɗaki suka datse ƙopa,Hankalinsu Yayi mugun tashi,Sun rasa gane zunubin da suka aikata har mutane ke neman bugunsu,Suna Cikin wannan halin ne suka ji anyi masu Sallama,muryar Limamin Unguwarsu ce,ƙin fitowa su kayi har saida suka ji yace"Kada kuji tsoron komai,ku fito inason magana daku ne,Naba mutanen anguwar haƙuri Sun tafi,"jin wannan maganar yasa suka buɗe ƙopar ɗakin suka fito,Bayin Allah kowacce jikinta sai kerma Yakeyi,hawaye sharkaf akan fuskarsu, Nasiha yayi masu sosai,A ƙarshe ya sanar dasu laifin da suka aikata wanda yasa mutanan unguwar ke neman kashe su,Abunda Ya faru Bayan tafiyar Abra,tabar Mammynsu ita kaɗai kwance tana jinya ta kwana ta yini cikin mawuyacin hali a lokacinne makwabciyarta tsigai wadda suke zuwa yin gulma a kuma gidanta ne ake kulle Amal,ta shigo ta sameta a wannan halin da kyar ta taimaka mata alokacin tana ta sababi tana fadin ina ma amfanin haihuwar yara irin nata,uwarsu ba lpy sun haura kafa sun tafi gantali,a washe gari tsigai tafiya ta kamata dama bata cika zama ba,ta ba yaranta umarnin su rinka leka Mammy suna kai mata abinci ai tun ranar farko da suka taras da ita acikin kazanta basu sake komawa ba sai ma wayarta da suka sace don rashin tsoron Allah,sauran mutanen unguwar babu wanda yasan da mara Lafiya acikin gidan,kowa yazo gidan nasu Yayi sallama ba'a amsa mashi ba,Sai yayi tunanin cewa babu mutun a gidan,Basu tashi sanin abunda ke faruwa ba,Sai da azababben wari ya ishi mutanan unguwar kamar gunyar ƙwai ta fashe,aka rasa daga ina wannan warin ke fitowa,Mutane suka kasa samun natsuwa a ƙarshe da aka tsananta bincike Aka gano cewa wannan warin a gidansu ne,Matasan unguwar suka shiga cikin gidan suna bincikawa har suka samu gawar Mammy ta ru6e naman jikinta ya zagwanye,tsutsotsi duk sun mamaye jikinta suna ci,Wa'iyazubillah,lokacin da su hayaam suka ji wannan Mummunan labarin a wurin limamin nan,Anan take Abra ta sume,Hayaam kuwa har kusan Zaucewa Tayi,sunyi danasanin rayuwarsu fiye da tunanin mai tunani,Sun tsani kansu,sun muzanta a idon jama'a,A ranar basu kwana acikin gidansu ba,Saboda mutanan dake dakonsu,Malam Liman ya tafi dasu gidanshi,kafin komai Ya lafa😭 A lokacin daƙyar aka samu wasu bayin Allah da taimakon limamin nan suka kawar da gawarta,An yi mata jana'iza kenan da Sati guda,Wannan makwabciyar tasu Tsigai,Ta sanya matasa suka kwashe mata kayan gidan kaf saboda tana bin Mammy bashin kuɗi kafin ta mutu,dama kuma a wurinta suke cin bashi in zasu wurin boka. Gani Ga wane Ya ishi wane jin tsoron Allah,ya Allah ka kare mu daga aikata aikin danasani, A 6angaren Ishaq kuwa,Aunty babba ta addabe shi da kira da numbobin mutane,bata gajiya da aron waya tana yi mashi magiya akan Ya taimaki Rayuwarta,Abunda yasa Ishaq bai mayar da hankali akanta ba shine tasaba yi mashi ƙarya ba kamar in tana son ta samu kuɗi,wannan dalilinne yasa bai ɗauki maganarta Serious ba,a ƙarshe ma data isheshi da kira sai ya cire Sim ɗin wayar gaba ɗaya ya ajiye shi,Ya musanya da wani sabo,ɗaya daga cikin illar yin ƙarya kenan Gashi tajama kanta,Gaba ɗaya yanzu hankalinshi na akan Hajjaju,domin kuwa ta amince zata aureshi,Soyayyarsu Tayi ƙarfi har sun fara zancen Yin aure, *Boss Bature* Wuraren ƙarfe 12 da rabi na rana,Amrish tana ta faman zarya acikin babban falon gidan,ranta a matuƙar 6ace,Ta cika tamkar zata fashe,tun safe ta ƙwallafa rai akan zasu fita a siya mata waya,Amma Mommy ta sa6a mata alƙawarinta,daga shiga ɗaki ta shirya ta fito bata ganta ba,ashe tabar gidan cikin motarta,Sae da ta bari ta ɗauki wankan lace ta sha uban make up tukunna tayi mata tsiya,Ta sha kuka harta gaji,fuskarta duk tayi jaga jaga da hawaye,tayi kukan harta gaji,a ƙarshe ta yanke shawarar zata nemo wayarta,Yau saita bincika ko'ina na gidan har sai Allah yasa ta gano wayarta,Upstairs ta fara hawa a buɗe ta samu ƙopar ɗakin Mommynta,Shiga ciki tayi tana ƙarewa ɗakin kallo,tunani ta shiga kota ina zata fara neman wayarta,bedroom ɗin ya haɗu sosai,Katafaren gado ne side by side ɗinshi kuma drawer ce,akwae faskekiyar wardrobe,ga tanƙameman Dressing mirror,da sauransu,hannu tasa ta cire kallabinta ta ɗaure shi a qugunta,drawer chest ta fara bubbuɗewa tana neman wayarta,sai da ta duba ko'ina duk ta hargitsa kayan bata ga wayarta ba,tuni ta haɗa gumi sai zufa ke tsastsafowa akan fuskarta,tsayawa tayi ruke da qugu tana faɗin"Wlh bazan haƙura ba,Duk inda kika 6oye mun wayata yau saina gano abuna,Ae ba ita ta siyamun wayar ba,Ya haroon ne ya siyamun,don haka dole a fiddo mun wayata,indai ana son Zaman lafiya"ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki ta nufi hanyar fita daga ɗakin,tana ƙoƙarin ruke handle ɗin ƙopar ta ɗan dakata yayin da kwalwarta ke tariyo mata wani abu kamar taso taga waya a saman gadon Mommynsu, A waske ta juya tare da wurga idanuwanta kan Wayar dake ajiye asaman pillow,da farko tayi tunanin wayarta ce saboda iphone ce,Amma lokacin da ta ƙarasa gaban gadon ta ɗauki wayar sai taga ba wayarta bace, Cike da mamaki tace kodai Mommy ce ta siyamun sabuwar waya don tayi suprising ɗina'? Jujjuya wayar ta shiga yi a hannunta,a kashe wayar take, Wuri ta samu gefen gadon ta zauna,ranta ne ya bata cewar ta kunna wayar ta gani, Danna power ɗin tayi nan take screen ɗin wayar ya kawo haske,Zama Amrish tayi tana jiran wayar ta kammala buɗewa,runtse idanuwanta ta ɗan yi kafin wayar ta buɗe, A hankali Amrish ta buɗe idanuwanta kan screen ɗin wayar,ƙura ido tayi tana kallon hoton wallpaper ɗin Abun yayi mugun ɗaure mata kai!cike da mamaki tace"kai!Wannan ae hoton Yayan Sehrish ne,JUNAID ROMEO,wanda ke kawota makaranta!ya akai wayarshi tazo hannun Mommynmu,"miƙewa tsaye tayi tana ƙarewa hoton kallo,Fuskar nan ɗauke da wannan kyakkyawan murmushin nashi,tama rasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243
- 244 Chapter 244
- 245 Chapter 245
- 246 Chapter 246
- 247 Chapter 247
- 248 Chapter 248
- 249 Chapter 249
- 250 Chapter 250
- 251 Chapter 251
- 252 Chapter 252
- 253 Chapter 253
- 254 Chapter 254
- 255 Chapter 255
- 256 Chapter 256
- 257 Chapter 257
- 258 Chapter 258