Chapter 199
Chapter 199
da abu,Haroon ya basu Umarni su kashe Junaid su kuma Sun kirani a waya sun sanar dani cewa Haroon Ya basu Umarnin su kashe Junaid,Shin da sanina koba da sani na ba,"!nan take nace masu karsu kuskura su kashe shi,Su san yarda za'ae su ɗauke Junaid daga cikin motar sannan su ƙonata yarda kowa zaiyi tunanin ya mutu,Nayi hakanne saboda banaso Haroon yaji cewa Na hana su bi umarninshi don zai canja wata hanyarne,sannan Kuma Don Junaid Ya zame mun makamin da zan Yaƙe ku dashi, Ƙarin bayani, Lokacin da Jahad ta fita daga cikin motar ta tsallaka zata siya masu ice cream,Junaid Ya dinga ƙwala mata kira,Ta dinga juyowa tana kallonshi Yana yi mata bye bye,bayan mai ice cream ɗin ya sallami mutanan dake gabanshi,Yace ma Jahad madam guda nawa za'a baki,Ta juya ta bashi Amsa,A cikin wannan Lokacin kafin Jahad ta lalubo kuɗi acikin jakarta ta miƙa mashi,adai dai lokacin,waɗannan miyagun suka buɗe motar,kafin Junaid ya ankara suka shaƙa mashi cocaine a hancinshi gaba ɗaya ya fita hayyacinshi,janyoshi su kayi daga cikin motar da hanzari suka fitar dashi,wanda ya ɗauki Junaid a kafaɗarshi ya juya dashi ta baya inda suka ajiye motarsu ya tura shi aciki,Shi kuma ɗayan Ya jefa bomb acikin motar,Yana barin wurin,Gingimarin Motar nan Ta shararo da gudu,Dama already sun kira wayarshi yana akan layi suna sanar dashi cewa Babu Yaron acikin motar,Atsiyace Yabi takan motar Junaid Ya rugurguzata,Yana sauka ya antaya da gudun gaske,Nan take Bomb ɗin cikin motar Ya fashe,Dama sun ɗibar mashi adadin mintunan da zai tashi,To masu karatu Kunji yadda akai Junaid Ya tsira,Baya acikin motar lokacin da suka take motar,Ko lokacin da Jahad ke ihu tana kuka,Duk a kunnanshi bawan Allah,Yana acikin motarsu sun rufe shi,Sam baya acikin hayyacinshi sai faman shafa glass ɗin motar yake yi yana kallonta,A haka har suka tashi motar da gudu suka bar wurin bayan sun dauki vedion motar naci da wuta wanda suka tura ma haroon, Yadda akai Sgr yasan game da abubuwan daya fadi ma haroon kuwa,dama tun farko,ya dawo Nigeria ne da niyyar yin bincike,don Mommynsa tasha fadi masa cewa akwae abubuwan dake faruwa ba daidai ba acikin gidan,kuma ta sanar dashi ita bata yarda da azmee ba,wannan dalilinne yasa yazo da shirinshi,a 6oye ya fara yin bincikenshi ba tare da kowa ya sani ba,ana haka kuma Mommynsu ta kirashi ta sanar dashi game da makudan kudin dasu twins suka bukata awurinta,ta tabbatar mashi akwae abunda yake faruwa dasu wanda suka 6oye don a yadda suka bukaci kudin sam hankalinsu ba'a kwance yake ba,gashi itama ta bukaci sai sun shirya tsakaninta da Junaid wanda tana ganin hakan ba mai yuwuwa bane cikin sauki,amman sai gashi sun aikata hakan duk don ta basu kudin,hakan yasa mata zarginsu,jin hakan yasa Sgr yin amfani da Surveillance Cameras wadanda yasa a wasu bangarori na gidan ba tare da kowa ya sani ba don bai barsu a bayyane ba wasu har a cikin chandeliers(fitilun sama) na parlon gidan aka sa,ta nan yake ganin duk abunda ke faruwa har lokacin dasu twins din suka kaima haroon kudin wanda daga baya yabi ya daukesu,koda ace asirin Azmee bai tonu ba ta hanyar ya Mu'allim ba,Sgr na gab da ganota,atakaice ma kusan ya gane bata da gaskia shiyasa ko lokacin da Abu ta sanar dashi dalilin ciwon Sehrish da kuma inda tasan Azmee yayi murmushin takaici,haka lokacin da Marshal Omar ke lallaba haroon akan ya sanar dasu wanda ke bashi umarni yace Sgr yasan komae,wannan kenan. Azmee taci gaba da bayani "Tunkafin Afkuwar wannan Lamarin,Akwai sihiri ajikin Junaid,Wanda mukayi mashi turenshi,a duk daren duniya,dunƙulen jini na fita daga hancinshi batare da sanin kowa ba,Saboda bai sanar daku ba,bayan Faruwar Accident ɗin nan ni nasa aka killace mun Junaid,kuma na hana kowa Ya cutar mun dashi,Lokacin da kuka sanar cewa Junaid Anyi kidnapping dinshi,Nayi mamaki sosai,Yarda kuka tsara hakan bayan a iya saninku mutuwa Yayi,Sai kuma nayi tunanin cewa Kun 6oye mutuwar Junaid ne saboda mahaifinku gudun kada ku rasa shi,bakowa ya fara Zargina ba,Sae Sehrish da ta tsinci zoben Junaid a cikin wardrobe ɗina,tundaga nan ta fara sanya mun ido,ni kuma nayi kokarin rikitar da ita har ta fara ƴan gane gane..............." Tunkan takai ƙarshen Maganar,Omar ya katse ta da cewa"Yanzu ina Junaid Yake,"?yayi tambayar tamkar baisan inda yake ba, Shuru Azmee Ta ɗanyi kafin tace"daga bayan nan Nasa an kaishi gidan Hajiya saratu,Ɗiyar wan mahaifina wadda ke acikin garin nan,".. "Innalallahi wa'inna ilahirraji'un!!" Amrish ce ta ambaci hakan tare da ɗaura hannunta asaman kanta,Tana kuka, Hankalin kowa Ya koma kanta,Muryarta na kerma ta nuna Azmee da hannunta tana faɗin"Dama ke kikasa aka kaishi gidanmu dan baƙin zalunci?Wacece ke?Ni bansan meya haɗani da ku ba,Wlh duk na tsani kaina,In har abunda nake zargi ya tabbata,wlh saina kashe kaina,"sosai ta fashe da kuka Tunda Azmee taji hakan nan ta gane cewa wani abu ya faru acan gidan,tabbas Junaid Ya ku6uta daga wurinsu,. Gyaran murya Ya Mu'allim yayi,hankalinsu ya dawo kanshi,Anan Yake labarta masu duk abunda ya faru kamar yarda Amrish ta sanar dashi,Har zuwa kaishi asibiti da su kayi, Yana kai ƙarshen maganar,Azeemi tace"Naji daɗi da Junaid ya dawo hannunku,Amrish ke bakowa bace face ɗiyar saratu matar ƙanina Ya Sayyadi,Da saratu dani ƴa'ƴan wa da kanine,Don haka ke jininmu ce gaba da baya,babu yarda zakiyi haka Allah Ya ƙaddaro maki,Ki gode ma Allah da baki ɗaukko irin mugayen ɗabi'un mahaifinki da mahaifiyarki ba wanda hakan ne ma yasa ba'a bayyana maki mahaifin naki ba," Waro ido waje Amrish tayi,idanuwanta sunyi jawur dasu,a fujajan ta watsa da gudu ta nufi Glass cups ɗin da suka faffashe a wurin,ta ɗauko ta daddage zata Caka shi a ƙahon zuciyarta da sauri Kanal Yusuf yayi hanzarin damƙar hannunta,ƙoƙarin kwacewa tadinga yi don ta Caka ma kanta,Amma ya hana hakan,Fisge glass ɗin yayi tare da jefar dashi ƙasa,Ya ruko kafaɗunta ya jinjigata"baki da hankali ne?Saboda me zaki kashe kanki?saboda Iyayenki sun kasance Gur6atattu!Laifinki ne?ko kin manta da ayar da Allah subhanahu wata Allah ke cewa"Yana fitar da mai rai daga matacce kuma yana fitar da matacce daga mai rai,kuma yana rayar da ƙasa a bayan mutuwarta,Kuma haka ake fitar daku,acikin suratul rum Ayata 20,Bayan ita akwai surar da tayi magana makamancin wannan acikin suratul Ahli'emran Aya ta 28,don haka ki kwantar da hankalinki,Ki rungumi ƙaddararki,Bakanki farau ba,Sau nawa cikakken malami ke haihuwar 6arawo ko kasurgumin dan fashi?Ba yadda Allah bai ikonshi,kuma bawai don baya sonku ba face don Ya jaraba imaninku,Sannan Laifin da iyayenki suka aikata bazai ta6a shafarki ba,ki gode ma Allah da baki ɗauko irin ɗabi'unsu ba,Ke tsarkakkiyace,Allah ya tsarkake ki daga faɗawa halaka.......'jikinta ba ƙaramin Sanyi yayi ba,Kalaman kanal Yusuf ba ƙaramin sanyaya mata zuciyarta su kayi ba,Har taji ta haƙura da kashe kanta da tace zata yi,Jiki asanyaye ta juya ta koma wurin Sehrish,rungumeta Sehrish tayi ajikinta,gaba ɗaya suka fashe da kuka maicin rai,dole Amrish taji ba daɗi,very heart touching ace iyayenka su dukansu gur6atattune kuma 6atattu,dayawa mutane zasu dinga yi maka wani mummunan kallo,Ya Allah kasa mu dace, "Nasan bazaku ta6a yafe mun ba,Ku yanke mun duk hukuncin da ya dace dani,wlh zan kar6eshi hannu bibbiyu,Amma dan Allah ina neman wata alfarma ɗaya agare ku,"Azmee ce tayi maganar,yayin da kwalla ke cigaba da zubowa akan fuskarta, Kasa kunne su kayi suna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243
- 244 Chapter 244
- 245 Chapter 245
- 246 Chapter 246
- 247 Chapter 247
- 248 Chapter 248
- 249 Chapter 249
- 250 Chapter 250
- 251 Chapter 251
- 252 Chapter 252
- 253 Chapter 253
- 254 Chapter 254
- 255 Chapter 255
- 256 Chapter 256
- 257 Chapter 257
- 258 Chapter 258