Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 127

Chapter 127

Abban Sojoji Takun Kaarshe 3 Complete Hausa Novel 1,370 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

furta hakan tare da ɗan rufe idanuwanshi yace"nifa,basu nake kallo ba,kayan jikinki ne suka burgeni,sunyi maki kyau sosai,"ya ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye yana kallonta, "Idan kana jin yunwa in kawo maka abinci"?tayi tambayar tana kallonshi, ɗaga mata kai yayi alamar eh,sannan yace"pls,inaso in ɗan kwanta in huta kinga baccin bai ishe ni ba,idan kika kawo mun Lunch ɗin,ki ajiyemun shi saina farka zanci," Amsa mashi tayi da toh,kafin ta miƙe da sauri da sauri ta fuce daga ɗakin,saman gadon ya koma ya kwanta,bakomai bane ya faɗo mashi aranshi ba,fa ce maganar da suka yi da Major dangane da Junaid,hakanan ya dinga jin kamar yayi kuskuren barinshi ya wuce da motarshi,dama ya sani tun a time ɗin yasa security sun bi Bayan Motarshi........... *Boss Bature* Ƙarar shigowar Message,da ta ji ne yasa takai hannu tare da ɗaukar wayarta dake ajiye agaban mirror,yayin da take zaune asaman kujerar gabanshi,tana yin makeup,janyo wayar tayi tana karanta message ɗin daya bayyana akan screen ɗin wayar, _Abra,inason magana dake,amma bana so kowa ya sani,koda Aunty Laila ce_ Mamaki ne ya kamata ganin anyi mata saƙo da new number,kowaye wannan,ɗaukar wayar tayi tare da miƙewa tsaye,a lokacin Aunty babba na cikin toilet tana yin wanka, Arab gown ce ajikinta,pink colour abunka ga fara tass,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nasu,ta miƙi hanya kamar zata fita daga corridor ɗin,Sai da ta bada tazara sosai,Sannan ta dannama numbar kira,tana fara ringing aka ɗaga, Tun kafin tayi sallama,taji muryar hayaam tace"ABRAH"!tun daga kan yadda ta kira sunanta yasa gabanta ya faɗi rass, "Aunty hayaam kece"? Bata amsa mata ba,sae ma fashewa da tayi da kuka mai sautin gaske,hakan ya ƙara ɗagawa Abra hankali,a ruɗe ta shiga faɗin"Aunty hayaam meya faru dake ne?meyasa kike kuka?dan Allah kiyi mun bayani," On the other hand,Hayaam ta miƙa ma Amani wayar tare da cewa"kiyi mata bayani," Gyaran murya Amani tayi tare da ambaton sunan Abra, Duk sunbi sun ɗaga mata hankali,muryarta har kerma takeyi wurin cewa"Dan Allah kuyi mun bayani,kun sanyani acikin duhu," "Abrah!ki natsu ki saurareni,"jinjina kai abra ta shiga yi tana fadin"ina sauraranki Aunty Amani,meya faru ne naji Aunty hayaam tana kuka, Amani bata 6oye mata komai ba,game da abunda ya faru da hayaam da kuma guduwar Aunty babba daga asibitin,da kuma wasikar da ta bar mata,wasu irin zafafan hawaye ne suka soma gangarowa akan fuskar Abra,hankalinta a matuƙar tashe tace"Nashiga uku!kenan nima wata rana idan ƙaddara ta same ni,Aunty laila zata iya guduwa ta barni? Amani tace"ƙwarai kuwa!saboda bata da Imani kuma bata da tausayi,karki so kiga yadda na samu hayaam a asibitin nan a wulakance,kamar wadda tayi hatsarin mota amma a haka laila tabarta,saboda bata da amfanin da zata yi mata,To kema muddin kika kuskura kika bita wurin bokan nan rayuwarki ta faɗa halaka,Kuma wlh da zarar amfaninki ya ƙare a wurinta shikenan kin zama Waste product!Zata yi watsi dake ne,"jin wannan maganar yasa Abra ta fashe da matsanancin kuka,wani irin tsoro ne ya kamata,don Aunty babba ta zama abun tsoro a wurinta,ta girgiza da jin rashin imaninta, Da gangan Amani ta dinga tunzura abra don ta tsoratar da ita akan karta goyi bayan Aunty babba suje wurin bokannan, "Abra!ina ƙara jan kunnanki,karki kuskura ki bi ta,Kiji tsoron Allah,ki tuna cewa wata rana zaki koma gare shi,kada kiyi silar da za'a cutar da rayuwar wasu,Aunty laila bata da Imani,tanaso ta jefa rayuwarku cikin haɗari ne,kuma tana yin amfani da ku ne don ta cimma burinta,kuma da zarar amfanin ku ya ƙare a wurinta,zata yi watsi daku ne,ta kama gabanta,Ga hayaam nan dai yanzu ta gane kuskuren da tayi,tana mai dana sanin abunda ta aikata," Amani nakai ƙarshen maganarta,ta miƙa ma hayaam wayan"kiyi mata magana," Kar6ar wayar hayaam tayi tare da karata a kunnanta,Kukan da Abra keyi har cikin zuciyarta,dama tasan dole taji raɗaɗin acikin zuciyarta,ɗan uwa ba wasa ba, Cikin Sanyin murya tace"Abra,baki ga yadda na koma ba,bani da wani abu daya rage na ƴa mace a jikina,komai ya lalace,Yanzu ma bana jin kaina amatsayin mace," Wani sabon kukan Abra ta ƙara fashewa dashi,cikin shessheƙa tace"Aunty hayaam wlh bazan bi ta ba,sai dai taje ita kaɗai,Ashe ba son mu take yi ba,bata ɗauke mu abakin komai ba,Amfani kawai take yi damu don ta cimma burinta,Ni wlh bansani ba Aunty hayaam,harfa tambayarta nayi ina kike amma tace mun wai batasan inda kika tafi ba,kinacan kina yawon gantali,Ashe kina gadon asibiti rai hannun Allah,yanzu haka fa da nake yin maganar nan,tun jiya muka iso Enugu da ita,Yanzu haka ma shirin zuwa wurin bokan muke yi, Hayaam tace"Abra,ki natsu ki saurare ni,kada ki bari tasan da shirinki naƙin binta wurin boka,saboda bata da imani tana iya kasheki,in kika 6ata mata rai,Abunda nake so dake shi ne,Duk wani kuɗi dake a wurinta,ki tattarasu gaba ɗaya ki sanyo su acikin jakarki,muguwar rabi da kwata na kuɗin dake a hannunta nawa ne,amma saboda tsabar rashin Imani ta kwashe hada nawa ta gudu dasu," Jinjina kai Abra tayi yayin da take share hawayenta, "Aunty hayaam,yanzu tana acikin toilet,bari nayi sauri na tattara kayana,in biyo mota in dawo nan," Hayaam tace"Yawwa,kiyi sauri kada fa kiyi kuskuren da zai sa ta gane cewa guduwa zakiyi ki barta,". "In sha Allah bazan bari ba," .daga haka su kayi sallama, Ajiyar zuciya hayaam ta sauke tare da kallon Amani dake zaune gefen gadon,tace"Har hankalina ya kwanta,So nake Aunty laila ta ɗanɗani kuɗarta,taji irin raɗaɗin dana ji acikin zuciyata, Murmushi Amani tasaki,tare da cewa"Nafi ki jin daɗi Hayaam,A shirye nake dana taimaka muku wurin ganin kun gyara rayuwarku,"acikin ranta kuma tace"Ita kuma waccen bijimar,Sai nasa ta tsani kanta,duk wani makusancinta saina kwace shi ya dawo a ƙarkashin ikona,So nake ta gane kuskuran da ta aikata arayuwarta," A 6angaren abra kuwa,tun bayan da suka kammala yin wayar,jiki na rawa ta koma Room ɗin nasu,A hankali ta tura ƙopar ta fara leƙawa ciki,don taga ko ta fito daga wankan,Ajiyar zuciya ta sauke,ganin bata fito ba,da sauri ta faɗa cikin ɗakin,Jikinta sai kerma yake yi,asaman bedside drawer,ta samu jakar Aunty babba,hannu tasa ta ɗauki handbag ɗin,tare da zagayawa ta Other side ɗin ta ɗauko ƴar purse ɗinta,saboda tsabar sauri jin Aunty babba na motsi kamar zata fito daga cikin toilet ɗin,aikuwa a gigice ta buɗe ƙopar ɗakin ta fuce,da gudun gaske,mutanen dake kai komo a cikin hotel ɗin sai kallonta sukaye,wasu kallon burgewa suke yi mata saboda rigar jikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,gashi bata sanya mayafi akanta ba,ƙafafunta ko takalma babu, Hankalinta bai kwanta ba,har sai da ta fito daga cikin hotel ɗin,gudu gudu sauri sauri ta miƙi hanya tana tafiya tana waiwayon bayanta kada ace Aunty laila ta biyota,Masu motoci sai parking sukeyi agabanta suna yi mata tayin shiga motarsu,amma taƙi sauraron kowa saboda gudun kada wani ya cutar da rayuwarta,kamar yadda aka yiwa Hayaam,baiwar Allah ta tsorata sosai,gashi babu wanda ta sani a garin,haka bata san ko ina ba,ba ƙaramin galabaita tayi ba, *Koya Abra zata ƙare?Shin ina Aunty Babba dake a cikin toilet tana wanka?Batasan an yashe ta ba* *Boss Bature* ❤🤍❤ Kano state Wuraren ƙarfe 6 na marece,Slowly motocin Sgr suka shiga cikin unguwar batare da jiniya ba,saboda patient ɗinsu da suka ɗaukko,a back seat na motar Abusufyan suka kwantar da ita,Abusufyan shi ne ke driving ɗin motar,fuskarnan tashi a washe,kamar wanda

Table of Contents

Chapters

258 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
  244. 244 Chapter 244
  245. 245 Chapter 245
  246. 246 Chapter 246
  247. 247 Chapter 247
  248. 248 Chapter 248
  249. 249 Chapter 249
  250. 250 Chapter 250
  251. 251 Chapter 251
  252. 252 Chapter 252
  253. 253 Chapter 253
  254. 254 Chapter 254
  255. 255 Chapter 255
  256. 256 Chapter 256
  257. 257 Chapter 257
  258. 258 Chapter 258
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});