Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,247 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsareta suyita shan firarsu har dare yai sosai batareda sun saniba sai hajiya tazo takoresa sannan yake tafiya,bunayya nasan hajiyarsu sbd yanda kula dasu ba kamar momynta ba,ita abun harma mamaki yakebata, dik irin soyayyarda momy kemata bata tab’a zama atareda itaba na tsawon kwana biyu ko uku tana kula daita amatsayinta na uwa ba,amma hajiya komai nasu akule take dashi. Hadda wanka idan lkc yai itake sakasu ta takurasu dole suyi, hakama b’angaren ibadah dalokaci yayi atare sukeyi, hakama b’angaren karatin addini yanzu bunayya tanayi, harma hadda tafarayi hizifi biyu kuma Alhmdllh abun nashiga sosai dan ya ramadan takurata yakeyi saitai tilawa sbd bata mayarda hankali sosai abunka da yarinta. Wasa wasa har bunayya takwashe wata uku a gidan batareda taga momyn taba, jin dadin zamanta a gidan yasa bata wani damuba amma yanzukam tafara damuwa,haka itama momy a kullum cikin damuwa take sbd har yanzu hajirasu dady tace bazasu gantaba, dakyar da sud’an goshi ta amince ramadan dasu nabila suka rakata taje suka wuni acan, bak’aramin dadi momy tajiba dataga yanda bunayya tacanja,gaba daya tasauya kamar baita ba, sai dare sannan suka dawo gida. Haka tacigaba da rayuwa a gidan cikin tsintsar farinciki da jin dad’i, saidai har yanzu takasa gane son ramadan takeyi bawai iya shakuwar yaya da k’anwace tashigeta ba,haka shima yafahimci hakan. Danhaka baiyi wasaba dasauri yasanarda ita,a tinaninsa zatai facali da maganarsa kokuma taki amsar tayin soyayyarsa,amma saiyaga akasin hakan dan dikda bata taba soyayya ba kuma batasan yatakeba hakan baihana ta amshi soyayyar sa ba. Ranar ramadan farincikinsa kasa boyuwa yai har saida yasami mahaifiyarsa da mahaifinsa yafada masu,suma kuma sunyi farinciki sosai, nan shima abban ramadan yasamu hajirasu yafada mata. Itama tanuna farincikinta sosai musamman yanda taga tarbiyar bunayya tacanja sosai tagyaru. Washe gari abban ramadan yasami dadyn bunayya a office dinsa, bayan sungama gaisawa angama yar tattaunawa saiya fara fada masa sak’on ramadan. Tsintsar mamakine ya bayyana a fuskar abban ramadan sbd ganin yanda yanayin fuskar dadyn bunayya tai, amaimakon yaga tsintsar farinciki a fuskar tasa saikuma yaga akasin hakan. Cikin hanzari dady yamike tsaye cikin fushi da b’acin rai tareda dukan table dinda ke office din sannan yafara magana “wai meyasa yaran nan idan zasuyi abu basa neman shawara, dika dika nawa bunayya take dahar za’ace anasanta da aure,yaushe ne girman yazomata kodan ganin wannan girman jikin ne, to gsky ni bantashi aurarda ita ba kagayamasa yai hkr,watakil zowa gaba idan takara girma hankali yagama shigota k’ila na amince,but now gsky ayi hkr, that’s all”. Mamaki yagama cika abban ramadan, gaba daya rayuwar turawa ta birkitamasa kwakwalwa komai nasa yacanja, kasa cemasa komai yai kawai yamike tsaye tareda fadin “ohk....ba damuwa,zan fadamasa sakonka insha Allah,nabarka lfy” yafada tareda ficewa. Shikam dady ko ajikinsa yazauna yacigaba da aikin gabansa. Lkcnda abban ramadan yafadamawa ramadan abunda dady yace saida yai kwallah sbd ya matuk’ar shak’uwa da bunayya gakuma wata sonta daketa faman azalzalar zuciyarsa. Itakam bunayya dataji batawani damuba tacemawa ramadan karya damu zatai magana da dady,tasan zai amince sbd tafi kowa sanin dadynta. Bayan sunyi magana dashi ramadan saita kira dady,dik yanda tai amma haka dady yakafe yace sam bai aminceba, tin abun yana wasa harya b’aci,kuka taketayi tana rok’onsa amma yakafe daga karshema saiya kashe wayar kawai. Daren ranar haka tayisa cikin bacin rai dakyar tasamu safiya tawaye dan bata iyayin baccin kirki ba, Washe gari kwatsam saiga takardan samun admission dinta a Federal university dake kalgo l/gvmnt acikin kebbi state. Jifa tai da takardar tafice dagudu bedroom dinsu tafada kan gado tareda fashewa dawani matsanancin kuka, safiyya tashigo ta taddata ahaka gashi hajiyarsu batanan,taitai tadaina kukan amma taki danhaka ta tashi tafice izowa dakin ya ramadan sbd tasan shikadai ne zai iya rarrasanta bayan hajiyarsu. Tana kawowa parlor sai taci karo dashi zashije kitchen,nan tafada masa abunda ke faruwa sannan tafice zowa aikinta, dafarko kamar karyaje saikuma dai yadaure yatafi. Koda yashiga dakin har yanxu kukan take,ahankali yazo yazauna kusa daita tareda zubawa kyakkyawor surarta ido. Aslm....my fans, kuyi hkr dajina shuru jiya wlh mamana ce batada lfy dan Allah kusakata acikin adduoinku,ngd sosai dakulawa. #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _15/16....._ Dik yanda yake tausayawa kansa na rashin iya mallakarta amatsayin matarsa ahalinda yaganta yanzu yafi tausayinta,yasani tabbas bunayya na sansa haka shima sonda yake ganin bak’aramin wuya zasushaba idan har akace dole saisun rabu. Ahankali yakira sunanta cikin tattausar muryarsa mai ratsa jiki da sanyawa gangar jiki kasala,wacca a dik lkcnda ta daki dodon kunnenta koda acikin bacci ko cikin duhune zata iya ganesa kai koda ma acikin dibbanin mutane ne “BUNAYYA....!!!” jin muryansa yasa ahankali tadan sausauta kukan nata “tashi muyi magana” ba musu kowa ahankali ta tashi a zaune kwallah bazubar mata sai sheshekar kuka takeyi, shuru yai yana kallonta yayinda itama tai shurun nantake d’akin yad’auki wani yanayin tsawon yan dak’iku sai sheshekar kukanta kakejiyowa. Ahankali kuma yafara magana “bunayya inaso kiyi hkr kidaina kukan nan haka,wannan kukan yana matuk’ar d’agaman hankali banasanshi kokad’an,wannan abun daya faru damu mud’aukesa amatsayin k’addararm...” bai k’arisaba tai saurin taryesa da fadin “mekake nufi ya ramadan..? kana nufin wai murabu kenan?”. Gyara zamansa yai yana fuskantarta sannan yacigaba da fad’in “bunayya inaso kisani bawani d’a nagari dayake cin nasara arayuwarsa batareda yanayin biyayya wa mahaifansa ba,shin baki example ga iyayenmu,dik girmansu da matsayinsu idan har hajiyarsu tai magana koda abun bai masu dad’iba bazasu taba k’etare wannan maganar ba bazasu taba mata musuba saidai su rungumi abun su karb’esa komai d’acinsa komai rashin dadinsa,sbd haka muma inaso muyi koyi dasu bunayya”. Saiya janye fuskarsa daga kallonta sannan yacigaba da fad’in “dikda nasan rashinki agareni tamkar babbar asarace wacca hamshak’in d’an kasuwa yakeyi, wlh wlh wlh bunayya inasanki so mara misaltuwa amma bazan iyayin musu da mahaifana ba,tinda dady bayasan aurenmu shkn muhak’ura watak’il ma wannan rabuwar tamu shine alkhairi a tsakaninmu”. Kalmarnan ta rabuwa dataji saida k’irjinta yai wani bugawa dak’arfi wasu kwallah masu zafi suka zubomata bakinta na rawa tace “kak...kak...kaima yanzu ka goyi bayan murabu kenan,haba ya ramadan idan kamin haka bakamin adalciba wlh” dafe kansa yai dayake masa ciwo mai tsanani sannan yace “kifahimta bunayya, mai biyayya wa iyayensa har abada baya tab’ewa maybe rabuwar tamu itace mafi alkhairi a tsakaninmu,kiyi hkr bunayya Allah yahad’a kowa da rabonsa” yana gama fad’ar haka yamike sauri zai fice. Dasauri ta tashi dagudu taje ta rungumesa ta baya tana fadin “ni wlh bazan iya auren wani bakaiba karka barni ya ramadan dady baisan irin sanda nakema bane shys” rintse idanuwansa yai wasu zafafan kwallah suka zubo masa,ahankali yarabata da jikinsa sannan yafice dasauri. Tsaye tai tana kallonsa harya fice,anan tazube tasake fashewa da wani sabon kukan,haka taita rerasa tsawon lkc anan bacci yakwasheta batareda tasaniba. Washe gari tin 8am ramadan yabi jirgin safe yafice agadaz gun dangin mahaifiyarsu kasancewar ita buzuwace yar agadaz hajiya maccha kenan,bunayya batasaniba sai bayan kusan kwana uku sannan taji abakin su nabila,anan takara tabbatarda lallai tarasa ramadan har abada,aikwa ranar takara tino da abunda tabari kwana uku yadawo mata sabo,har safiya tawaye bata iyayin bacci ba, Nantake damuwa ta bayyana a jikinta idanuwanta suka kukkumbura sbd yawan kuka. Sannu ahankali tintana kuka harta fara hkr dole hajiya kuma tana k’okari sosai wajen mata nasihohi masu ratsa

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});