Chapter 17
Chapter 17
olready mashkur yakira momynsa danhaka koda suka isa ana jiransu,yana fitowa yazo yad’akkota yadora kan gadonda ake d’aukan majinyata sannan aka fice daita,emergency aka fice daita inda doctor zainba haroon wato momyn mashkur tashiga domin gudanarda aikinta. Cikin b’acin rai umman ruwaida tafara magana “mashkur dan Allah kayaimaka kabama iyayenka hkr amaida yarinyar nan tinda dai anriga angano komai gsky tafito suyi hkr sumaidata inda tafi sani inda tai rayuwa,shin taya rana daya zasuce surabata dasu,dama ace sunmata mugun riko ne dasai ace mumaidata hanunmu amma harma munsamu sun rik’ata cikin amana,wlh ni namafi tausayin ita uwar tata sbd ance tanacan hawan jininta yatashi rai hanun Allah dik sbd anrabata daita,shin yakake ganin a lkcnda aka raba uwa da y’arta batareda wani daliliba,rabasufa tamkar raba hanta da jinine”. Nannauyan numfashi mashkur yasauke kamin yace “abunda kika fada gsky ne umma,nima kuma nayi wannan tinanin,insha Allah zanyi iya kokarina naga bunayya takoma hanun iyayen rik’onta,yanzudai bara mufara ganin komai yazama normal tukuna”. Tsawon 1hr dashiga da bunayya momy tafito tamasu bayanin tasamu bacci,gdy sukama Allah sannan suka zauna zaman jiran farkawarta. Mashkur bin bayan momynsa yai suka tattauna matsalar dakuma yanda zasu shawo kan matsalar dake tasowa a ahalinsu,acikin k’ankanen lkc suka samo mafita dakuma yanda zasu shawo kan matsalar. Sai dare sannan bunayya tafarka,koda tafarka mashkur bayanan sai faman rigima ake daita akan tasha magani tashi abinci sannan amata injections dinda ba’akarisaba, itakwa sai kuka take tana fadin “dan Allah narok’eku kubarni natafi gun iyayena kubarni natafi naga mahaifiyata,nasan yanzu tanacan acikin wani mawuyacin hali sbd rashina,wai meyasa bakuda tausayine meyasa meyasa” tasake fashewa da kuka. Tausayinta ke ratsa jikin umma da momy umma harta kasa hkr da ganin yar tata acikin wannan halin saita fita waje dasauri tana sharar kwallah, Anacikin wannan yanayin mashkur yadawo daga masjid,a kofa yatadda umma tana sharan kwallah,dasauri yashiga tambayarta abunda ke faruwa nan tafadamasa,numfashi yasauke sannan yashiga ciki. Har yanzu kuka take sosai ta fizge cannula dinda aka sanyamata drip daita hanunta sai zubarda jini yake,dasauri yaje yad’akko plaster da kad’a sannan yariko hanunta yasanya mata jini yabar zuba,kuka take sosai tana fadin “da me kataimakeni ka maidani gun iyayena dan Allah nasan yanzu momy na tana cikin mawuyacin hali sbd rashina akusa daita,dan Allah ka kaini gun momy da me” tausayinta yamamaye zuciyarsa da gangar jikinsa gaba d’aya, janyota yai ya rungume yana bubbuga bayanta alamar rarrashi,ahankali ahankali kowa ta sausauta kukan. Ahankali yajanyeta daga jikinsa sannan yatallafo fuskarta da hannayensa suna kallon juna yafara mata mgn “Is okay bunayya,zan maidaki gun momy da dady amma saikinsha magani kinci abinci kuma kinbari anmaki injection,kinga jikinki ba kwari ga zazzabi sosai,so kiyi hkr har kwana biyu kacal jikinki ya warware saina kaiki dakaina gun momy da dadyn ki,kinji ko” gyada masa kai kawai tai tasan zai maidata tinda dai yafada sbd tasan halinsa zai yi tinda yace zaiyi. Dakansa yad’akko maganin yabata tasha sannan taci abinci sosai,daganan aka mata injection din sannan ta kwanta hanunta sakad’e dana mashkur har bacci yadauketa. Da darema haka yasakata agaba taci abinci sosai sai a lkcn tatina da wayarta saidai wayar tanacan hanun dadyn ruwaida, mashkur yasakata agaba yana janta da fira hartad’an fara sakewa tana yar dariya idan akayi abun dariya. Saida akayi sallar isha sannan yafita,suna sallah akafara kiran wayarsa,koda suka gama anmasa kusan 7miss calls kuma new number ce,danhaka bayan yagama yafito masjid saiya kira layin, ringing d’aya ana biyu aka d’aga, muryar dadyn bunayya yaji acikin wani yanayi yana magana “mashkur.....nine dadyn bunayya” cikin girmamawa mashkur yace “au....dady kaine” yace “eh nine mashkur,naita neman layin bunayya amma baya shiga shine naje school d’inku nanemo number d’inka sbd kai nasan zakafi saurarata” mashkur yagyara tsayuwarsa sannan yace. “Incedai lfy dady?” dady yacigaba da magana “mashkur nasan mun aikatawa iyayen bunayya babban laifi, laifinda bakowane bil adam ne zai iyayin yafiya wa wanda ya’aikata irin wannan laifin ba, kuma wlh nayi nadamar aikata wannan laifin ahalin yanzu, jolde batada laifi acikin wannan lamarin,dik nine ummulhaba’isin wannan lamarin, tsintsar son yaya dakuma kaucewa tashin hankalinda ya fuskantomu a lkcn shys na aikata hakan, ina matuk’ar kaunar maryam kuma banasan rabuwa daita,nasani koda maryam bata haihuba bazan taba rabuwa daitaba amma gori da wulakanci ne nakemata gudu shys nad’auki wannan matakin, Sannan itama a lkcn batada wani buri daya wuce taga gudan jininta maana ta haihu tasamu yaya kota halin kakane,shys kawai nayanke wannan hukun a lkcn, a yanzu kuma gashi abunda na aikata yazameman nadama da dana sani, a yanzu haka muna hospital da maryam rai a hanun Allah hawan jininta yatashi yanzuma yafi na da din,anyita kiran layin bunayya amma baya shiga sbd dikta farka bunayya kawai take kira shys naje school dinku domin kaucewa zargin mutane sbd banasan kowa yasan wannan lamarin,dan Allah mashkur kataimakeni domin shawo kan iyayenka,kuma kataimakeni bunayya tadawo”. Nannauyan numfashi mashkur yasauke “Hmmm....!” sannan yafara magana “shkn dady,dama munyi magana da momyna akan lamarin,yanzu jira muke su dady sudawo sbd sunje Uganda acan hospital dinda abun yafaru, amma very soon zasu dawo insha Allah,zamuyi dik yanda zamuyi domin ganin anmagance wannan lamarin insha Allah, bunayya kuma batada lfy itama tak’i kwantarda hankalinta sai kiran momy take a yanzu hakama muna hospital daita ammadai taji sauki Alhmdllh”. Jin bunayya ba lfy nantake hankalin dady yatashi matuk’a fiyeda d’azun dayace momy batada lfy,cikin damuwa yacewa mashkur “mashkur dan Allah ka kulamin da bunayya sosai karka bari wani abun na damuwa yasameta kajiko” dan murmushi mashkur yai sannan yace. “Toh insha Allah, gobe insha Allah zankawo bunayya gun momy” jin haka yasanya dady cikin farinciki zaiga abar k’aunarsa” dasauri cikin mud’i yace “Ohk...toh saikunzo” mashkur yace “Ok....Allah ibama momy lfy” yace ameen sannan sukai sallama. Jikin bunayya Alhmdllh danhaka washe gari mashkur yashirya yakai bunayya kebbi gun momynta kamar yanda yai alk’awari bisa amincewar momyn sa dakuma izininta dana umman ruwaida, yanda bunayya taga jikin momynta sai kuka yadawomata sabo, dakyar mashkur ya rarrasheta yasamu tadaina kukan, dazasu dawo dakyar yasamu yadakkota sbd tace bainda zataje tabar momynta cikin wannan halin,dakyar yad’akkota suka dawo yola adamawa. ................... Tafiyarsu dadyn mashkur Uganda tazoda tashin hankali,suna zowa kai tsaye gun gomnar k’asar sukaje suka fadamasa abunda yake tafe dasu,nan aka kira shugaban hospital din,kundin jariranda aka haifa a shekara goma sha tara dasuka wuce aka d’akko nantake kowa aka gano file dinsu bunayya tareda yar uwarta ruwaida sannan aka d’akko na d’anda momy tahaifa dik a ranar, nan aka tabbatarda cewa bunayya itace yar uwar ruwaida wacca tace abokiyar tagwaicinta. Ta hakan ne kuma suka gano doctor haji mansur wanda dady yasamu sukai aikin canjen jinjiraye guda biyu wato bunayya da babynsu, aikwa nantake aka saka cigiyar nemansa,acikin yan kwanaki aka ganosa aka gurfanardashi agabansu dady. Dafarko maganar taso tayi zafi amma da’aka fahimci juna sai abun yasakko aka fara fahimtar juna, mahaifinsu ruwaida yanada zafi sosai shi soyai yakai zancen kotu,dakyar likitan yasamu yashawokan abban ruwaida tareda taimakawar gomnan jihar,tarar kud’i akacisa sosai sannan asibitin ta koresa tareda makasa kotu domin kwatar hakkinta na b’atamata suna dayake tsawon shekaru ashe aikinsa kenan. Sudai abban ruwaida anbiyasu tararda aka doramasa kuma Alhmdllh tinda sun tabbatarda bunayya yarsu ce itace wacca aka masu exchange da mataccen d’a wanda banasuba, Bayan ankammala komai saisuka tattaro suka dawo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34