Chapter 3
Chapter 3
cikekkiyar bafulatana ce gaba da baya, mahaifinta hamshak’in d’ankasuwa ne kamar yanda kakanta ma yake hamshak’in d’ankasuwa. Su atarihin gidansu kasuwanci shine gadonsu danhaka dik wanda yataso a gidan mace ko namiji kasuwanci shine abun yinsa. Suntara dukiya wuce tinanin mai karatu ankuma tara masu ita wacca ko jikokin jikokinsu bazasu iya cinyetaba. Kakan jolde Alhj Abdullahi shikad’ai ne iyayensa suka haifa shikuma yahaifi Ahmad da Aminullah, Aminullah shine mahaifin maryam jolde, sbd alkunya irinta fulani yasa sukecewa Ahmad shine ubansu ba Aminullah ba, kamar yanda shima yayan ahmad suke cewa Aminullah shine ubansu. Maryam su takwas ne mahaifiyarsu fatima ta haifa maza bakwai mace daya wato ita, sai abokiyar zaman mahaifiyarsu tanada biyar maza hudu mace daya Ruk’ayya. Muhammad, Abubakar,Umar, Uthman,Ahmad,Abdullahi sai Sulaiman sai Maryam, sune yan uwan jolde, dayan dakin kuma El-mustapha, Aliyu, Aminullah, Ibrahim Sai Rukayya. Rukayya atare akayi aurensu da maryam da yayansu Muhammad da umar da El-mustapha, yanzu yayan rukayya biyar Muhammad kuma uku el-mustapha ma uku umar hudu sai ita data haihu yanzu. KADEL KABIR KAMAL, haifaffen k’asar kebbi a birnin kebbi L/gmnvt, amma asalinsa shuwa arab ne kasuwanci ne yakawosu garin kebbi inda anan ne mahaifinsa Alhj kabir yahad’u da mahaifin maryam jolde a lkcnda suka hada hannun jari domin yin kasuwanci atare, tanan ne alakarsu tahadu har suka zama aminan juna harkuma suka hada yayansu aure maryam da kadel. Kadel shine nafari a gidansu wanda dama su hudu ne iyayensu suka haifa, kadel kamal hafsat sai humairah. Wannan kenan. ........................ Bayan shekara uku da haihuwar Bunayya suka tattara suka koma Australia da zama, dazuwansu aka sakata school tafara karatu. #/Vote #/Share #/Comment #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _5/6....._ Sannu ahankali bunayya tafara karatu cikin nasara da ikon ubangiji,soyayyarta acikin zuciyar iyayenta kowa sai dad’a k’aruwa take,hakama ahalinta na dika b’angaren biyun sai dad’a sonta da k’aunarta sukeyi. Nanny’s biyu takeda masu kula daita sbd momynta tana yawan tafiye tafiye k’asashe k’asashe kasuwanci haka shima abbanta,yanzukam suda Nigeria sai idan bunayya sunyi hutun school saisuzo anan suyi hutun. Wata iriyar soyayya take samun agun iyayenta musamman mahaifiyarta wacca kokad’an batasan ganin b’acin ranta, hakama mahaifinta idan kaga yanda yake mata zaka rantse da Allah itakad’ai ce yarsa bashida wasu yayan sbd tsabar kaunarda yake nunamata, Dahaka rayuwarta tacigaba da gudana cikin tsintsar so da k’auna dakuma cikekkiyar kulawa. .................. _After 15 year’s....._ Cikin sauri sauri take shirinta na zowa school bayanda tagama sanya uniform’s d’inta wanda yake riga iya guiwa girmanta dark blue da t-shirt fara aciki mai girman hanu iya guiwar hanu, sai white socks da takalma. Kanta ba hula ko d’ankwali tatufke sumarta gu d’aya tasako da jelar izowa gadon bayanta. A duk’e take kusa da bed d’inta tana gyara takalmanta, ahankali tad’ago tamike tsaye tareda juyowa domin d’aukan school bag d’inta, woww masha Allah nafurta azahiri batareda ma nasan nafurta ba sbd ganin kyakkyawor halittarda nai. Dikda ba make-up a fuskarta amma hakan baihana bayyanar tsintsar kyanta a fili ba. Faffad’ar fuska kyakkyawa kuma fara tas wacca take d’aukeda golding eyes nd’ siririn hanci mai d’an girma da tsayi daidai fuskar, bakinta d’an k’arami mara girma sosai,sumarta mai cika da bak’i wulik kuma mai tsayi ssi. Dikda sanye take da uniforms amma hakan baihana bayyanar kyakkyawor surarta a fili ba, k’itjinta a cike yake taf da dukiyar fulani daka kalla kasan acike yake,hakama bayanda masha Allah hips dinta barakallah dan har rigarta tad’an d’aga daga baya sbd girman hips dinta, gaban rigar yafi bayan dan tsayi, kai atak’aice dai kyakkyawa ce san kowa k’in wanda yarasa. Dasauri tashuri jakarta tafice harda d’an gudunta sbd dagani tai letti. Kai tsaye a dining room tafice inda ta tadda iyayenta acan suna breakfast, dasauri taje ta zauna tana fadin “gud morning momy...gud dady” cikin farinciki suka amsa mata cikin faraa abban yashafa kanta yana fadin “baby kinyi letti yau,ya’akayi hakan tafaru ne” d’an b’ata fuska tai tareda tab’e d’an k’aramin bakinta tace “su jasmine ne suka d’auken hankali jiya mukaita chart har 12, shys nai letti”. Cooker dinsu ne yazo yafara zubamata abincinda yasan tafiso take kuma yin break dashi,bayan yagama nan tafara ci sukuma su dady suna firarsu. Kad’an taci tamik’e tana fadin “am satisfying dad” yace “ok darling, Samuel yana jiranki tin d’azu” shagwabe fuska tai cikin sigar shagwaba tace. “Oh...nooo dady, nifa kai nakesan ka kaini yau” yar dariya yai tareda rik’a hanunta yace “angama sweetheart yau hukuncin yamotsa kenan” itadai momy kallonsu kawai take. Mikewa yai yana saka takalmansa tareda fadin “oya...lets go” cikin faraa taje tarungume momynta tareda sumbatarta a kunce tana fadin “bye momy” itama ta sumbaceta a goshi tana murmushi tace “Ok...bye sweetheart” nan tafice tana dan tsalle. Koda suka isa tini har an shiga class bakowa a waje, danhaka dagudu tafice izowa class tanama dadyn nata bye bye, shima bye din yamata yana kallonta harta haye step izowa class dinsu sannan yafice. Sai 10am sannan suka fito break,damacan ita baruwanta dacin break tin a gida takeyin abunta datazo school saidai taci chocolate da sweet dinta,tin fil azal haka take har teachers dinsu sunsanta dashan chocolate da sweet any time zaka samesu acikin school bag dinta shys koda yaushe taketa fama da ciwon mara sbd zak’i. Mimi da jasmine sune k’awayenta waenda suka hadu a secondary school dinnan tasu tin jss 1 har izowa yanzu dasuke ss 3 wato ajin k’arshe, suma dikansu yan Nigeria ne zamane yakawo iyayensu anan Australia. Bayan su jasmine sungama break sai suka koma class, 1:30pm suka tashi daga school suka koma gida. Daisarta tai wanka tacanja kaya izowa gajeren wando iya guiwa da riga t-shirt fara sannan tafito parlor, ganin momynta bata parlor yasa tahaura sama, a bedroom din dadyn ta tacimmata tana linke masa kaya shikuma yafito daga toilet yana saka kaya, cikin sallama tashiga tareda fadin “hy momy....hy dady” cikin faraa dady yace “welcome sweetheart” ta amsa da “hy dady” tareda kwanciya kan gado. Kallonta momyn ta tai sannan tace “tashi kije kici abinci mana” toh tafada sannan tamike tsaye tafice. Kai tsaye dining room tafice taci abinci, bayan tagama takoma bedroom dinta takwanta, wayarta taciro tabude music tafara sha, daga haka har bacci yad’auketa. Sai kusan 5pm sannan tafarka,wanka tasakeyi kasancewar tana fashin sallah yasa batai batun yin sallah ba,bayan tashirya cikin wata gown girmanta iya guiwa da wata yar hula baka sannan tafice parlor. #/Vote nd Comment. #/Aufana for life. _*AURENTA ZANYI....*_🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _7/8......_ Koda taje parlor momyn ta nakan laptop tana aiki, zama tai a kujerarda ke kusa daita tana fadin “momy...hala dady London zaije” gun d’ayar matarsa kenan momyn ammar. Batareda tad’ago ba tace “eh,kinsan yau kwananta ne” tab’e baki tai batareda tasake cewa komaiba, can takwallawa cookie dinsu kira “roben...roben where are u wai..” tafad’a da k’arfi, dagudu wanda takira da roben yazo yana fadin “yes ma, am sorry ma am here” wata muguwar harara tagalla masa tareda watsa masa harara kamin tace. “Oya..go and help me with some food, am so feeding hungry wlh” dasauri yace “ok ma” tareda juyawa izowa kitchen, kwanciya tai kan kujerar tareda fara latse latsen wayarta. Acikin yan mintinanda basufi 5 ba yakawomata abincin tafaraci tana cigaba da latsar phone d’inta. Bayan tagama yakwashe kayan yakai kitchen. Around 8:30pm tafara shirinta cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34