Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gyara zamansa yana fuskantarta,tasan halinsa sarai yanzu zai fara mata sharri saikawai tasha mur,aikwa wabakin boka,cikin murmushin tsokana yafara fadin. “Am....hamdallah gsky kina kokari sosai,Allah dai isakamaki da alkhairi,kina kokari sosai wajen had’eman k’anwarnan tawa, gashi make-up yana matuk’ar yimata kyau amma kokad’an batasanyi bare takoya taiya,but...don’t worry insha Allah zansan yanda zaayi muma muiya wannan make-up din” hararan gefen ido tamasa saiya kwashe da dariya. Tana hararansa tace “kagane da mee...idan baka tashiyin tafiyar nanba saina fita nabarma motar wlh” yana toshe bakinsa sbd dariya yace “Allah yahuci zuciyar sarauniyatar kyawawan k’asar kebbi,tuba nake sarauniyata, da girman kujerarki” nan yatada motar sannan suka wuce. Kai tsaye wani had’adden park sukaje wanda yake d’aukeda wuraren hutawa da shak’atawa masu k’ayatarwa acikinsa, gu d’aya suka samu suka shimgid’a wani carpet mai kyau da laushi sannan suka zauna. Ordering kayan fruits yamasu different colors had’eda juices kala kala aka cikamasu gabansu dasu. Ahankali suka fara sha suna yar fira ahankali ahankali, bayan y’an mintina sai mashkur yamatso kusa da bunayya kasancewar a gefen damansa take,hanunsa yasaka acikin aljihunsa yaciro wata yar akwati akan kwalin akwatin antubutu “special gift”. Mik’awa bunayya yai yana fadin “happy birthday to uuuu.....happy birthday to uuu...happy birthday happy birthday, happy birthday to uuuuu....., happy born day my lovely sister nd’ my bride to be insha Allah” waro idanuwanta tai tareda wage d’an k’aramin bakinta tafurta. “Wowww.....thanks sooo much my brother, tnx allot da mee...na am very proud of u nd’ am very appreciate to u my big brother” hamdallah ma wage bakinta tai cikin mamaki sbd sudika sunmanta da ranar. Bunayya tace “kaga wlh nifa harnama manta wlh, amma nasan koda kowa zai manta momy na bazata tab’a mantawa da wannan ranar ba komai rintsi, shys nake k’ara k’aunarta acikin zuciyata nake kara santa fiye da kowa nawa a duniya, ina matuk’ar kaunar momy na” murmushin farinciki suke sudika. Hamdallah tace “am sorry nidai tawa kyautar sai munkoma school sbd yanzu yazoman a bazata ba shiri” sukai dariya tace “bakomai yar uwa” ahankali ta bud’e kyautar mashkur saiga wani tsadajjen zoben gold yana kyalli yana shining tsabar kyau tana kara bayyanar masa. Kara matsowa dab daita mashkur yai sannan yamiko cikin tafin hanunsa yakuma duko da fuskarsa suna kallon juna,ahankali yafara mata magana cikin tattausar murya da tausasan lafuzza waenda bata taba jin irinsu agaresaba “and then ina rok’on kibani dama k’anwata domin mallakarki amatsayin matata ta sinnah kuma uwar y’ayana insha Allah, the all what I mean is...I really love u with all my hert with full confidence my sister” tashi yai yagyara wandansa sannan yakarayarda k’afarsa d’aya d’ayar kuma yaduk’a akan guiwarta sannan yad’ora hanunsa daya tareda furta. “Please my sister, will u marry me.....?” yajefamata tambayar kai tsaye kuma a lkc d’aya. Tinda yafara magana har izowa yanzu a dazk’are take tana kallonsa cikin tsintsar mamaki, gaba daya yacikata da mamaki,tinda take dashi koda da saud’aya mashkur baitab’a nunamata alamar wai yanasanta da soyayya kokuma aure ba sai yanzu, danhaka abun yazomata a bazata,hakan yasa takasa gasgata abunda ke faruwa a yanzu. Batasan sadda kwallah suka fara zubomata ba waenda kasa bambance shin na farinciki ne kokuma akasin hakan, saidai tatsinci kanta dajin wani irin farinciki dakuma jin nishad’i had’e da kunyarsa ta mamayeta,mamaki take wai itace mashkur dinnan mai girman kai da rashin kula y’ammata harma da wulak’antasu wani lkcn,shine wai agabanta a durk’ushe yana neman soyayyarta. Rufe fuskarta tai da tafukan hannayenta cikin yanayin kunya,mirtsinarta hamdallah tai cikin dariya da farinciki saita kyalkyale da dariya tareda rungume hamdallah d’in, hakan ya bama mashkur amsar cewa ta amince kenan. Murmushin jin dad’i yai tareda mik’ewa tsaye sannan yakamo hanunta na dama yasanyamata zoben gold din a yatsanta nakusa da k’arshe saika yamata kyau sosai,hasken yatsunta suka had’e dana zobenwsaiyake bada wata kalar kyan mai d’aukan hankali, kissing dinsa yai sannan yace. “Inaso ranarda za’amin walimar kammala second degree dina ahad’e data aurena insha Allah,nanda d’an lkc k’ankane zan mallaki k’anwata fatima amatsayin matar aurena kuma uwar yayana insha Allah” kunya dikta k’ara mamaye bunayya hartakasa kallonsa yanzu,shikwa ba abunda yake sai dariya yana kallon kyakkyawor fuskarta. Suna a zaune kwatsam saiga ruwa yasakko nanfa kowa akafara guduwa domin kiyaye kai, itakam bunayya zamanta tai acikin ruwan yana ware hannayenta tana juyi acikin ruwan,damacan bunayya tanasan ruwa sosai kamar kifin cikin rijiya tariga tasaba dasu sosai bare kuma yau datake acikin farinciki. Wasa tadingayi sosai acikin ruwan tana dariya tana tsalle,shikwa gogan tsaye yai acikin wata rumfa dasuke aciki yazo yakwashe sauran kayan hamdallah nacikin mota itakad’ai. Kallonta yake yana murmushi yanda take wasa acikin ruwan, veal dinda tai rolling dashi ya kwance sumarta a waje,hakama abayarda jikinta bottoms din rigar sun b’alle wandanda ke ciki na jeans da yar singlet dinda ke ciki yana hangosu sosai,ruwa ya kwantarda singlet din har tai showing kana ganin shayin brez d’inta, kallonta yake yajingina da bango ya hard’e hannayensa gu d’aya, shifa ji yake kamar ma yaune yafara ganinta, cikekken halittar k’irjinta yake kallo dakuma bayanta idan tajuya. Wannan shine karo na farko daya fara jin yana sak’a abu a zuciyarsa akan bunayya, musamman yanzu dayake kallon kyakkyawor surarta musamman halittar k’irjinta dasuka fara d’aga masa hankali sbd ganin cikarsu,gashi a rayuwarsa ba abunda yafiso agun mace kamar dukiyar fulani sannan matasan zama. To saigashi bunayya tahad’a dika biyun koma nace uku, kyau gaba dakuma baya dika,rauninta kad’an ne wanda yasan idan yajajirce dik zai taimaka mata wajen gyarasu koda bazasukai 99% ba. Yana cikin wannan tinanin saiya tino da hamdallah danhaka yakwallawa bunayya kira ta waigo tagansa,dasauri tagyara abayarta sannan taje suka fice tana wani sinne kai. Acikin mota ma kanta a k’asa yake takasa had’a ido dashi,tamayishu tak’i magana dik yanda yaso yajata fira amma tak’i sai hamdallah ce kawai ke tayasa firar har suka iso school. ................... Tindaga wannan ranar bunayya tashiga wasan b’uya da mashkur,tinda sukaje park yau kusan kwana uku kenan baisake sakata a ido ba har yau. Nemanta yake ruwa a jallo amma baigantaba kuma yasan bataje gidaba,dik inda yasan tana zama yaje amma baya ganinta, Baisan cewa bunayya tashiga kullene ba,tasakawa kanta sark’ar k’arfe da pard lock tarufe kanta daga lecture sai lecture take fita,dasun dawo kuma tashige shkn,wai ita dik dan karyaganta ne yanzu kunyarsa takeji sosai. Around 8:30pm bayan sundawo daga masjid saitaje wani d’an kanti dake cikin school din, street sket ne ajikinta na roba sai wata yar singlet pink color,k’aramin hijab ne ajikinta wanda bai wuce yadi biyu ba. Buiscuit ne ahanunta da ice-cream da chocolate da sweet acikin wata bakar leda, tana cikin tafiya tana rera yar wak’arta,hankalinta nakan wayarta datake jin music kawai saitaji anjanyota da k’arfi anmanna bayanta da bango,rintse idanuwanta tai dasauri acikin tsintsar tsoro da tashin hankali sbd tama d’auka fad’uwa zatayi ak’asa saitai saurin furta “Innalillahi wainna ilaihi rajiun”. Dariyarsa taji yana kallon fuskarta dakuma yanda jikinta yashiga rawa sbd tsoronda taji, jin sariyarsa yasa tagane ko waye, danhaka ta bud’e idanuwanta ahankali sai akan fuskarsa tasauke idanuwan nata. Kallon kallo suka faramawa juna kamin ita tad’auke nata idanun cikin yanayin kunya, wani killer smile yai kamin yakai yatsansa tindaga kan goshinta har izowa kan doogon hancinta har izowa gementa yana fadin “tsalki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawor fuskar”.

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});