Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,247 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jiki dakuma irin riba da nasararda mai hakuri kesamu acikin rayuwarsa,dahaka tasamu harta fara hkr tana sakewa. ...................... Sannu ahankali har aka kwashe kimanin wata biyu da faruwar wannan lamarin. Wannan shine rabuwar bunayya da yayanta ramadan, tini tafara karatinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali gakuma shirye shiryen shagalin bikin ya Amir da aunty mardiyya da yaya affan da nabila sunfara,gida haryafara cika da bak’i na nesa dana kusa sai faman shirye shirye suke. Yanzu komai yamata sauki sbd idan taje school tin 8am sai 6pm take dawowa, gida kuma yanzu acike yake gwanin birgewa danhaka yanzu tafara mantawa da damuwarta saidai idan ta tinane takejin damuwar tazomata amma datai adduah kokuma tasami abunda zaisa tamanta shkn nantake saita mantarda abun acikin zuciyarta. Sannu ahankali akafara gudanarda shagalin biki,yanzukam bunayya anfara saka atampa, jiya akayi kamu suka saka material ja gown har kasa akamasu make-up, wow Masha Allah naso kowa kuganta yanda tai kyau sosai,ko amare basufita kyauba, Yau kuma tinda sassafe akamasu lalle ja,abunka da fararen fata kuma jinin shuwa arabs lallen yamatukar yimasu kyau sosai musamman ita,dan itakam diktafisu kyau, yau kunshine kawai zaayi danhaka suka saka kid’ansu sukaita cashewa abunsu sunayin nishad’i. Washe gari akai bridal shower suka saka gown ta atampa yellow white and black color, sunsha make-up sosai sunyi matuk’ar yin kyau bakad’an ba,abun gwanin birgewa bunayya sai nishad’i suke,sunsha rawa sosai, sai kusan 6:30pm sannan aka turo motoci suka d’aukesu. Washe gari asabar around 10am dot aka d’aura auren 12pm dot aka fice royal event inda zaayi Arabians day,amare biyu mardiyya da nabila dakuma matan ya amir da yaya affan suka saka gown fara tanaja akasa gwanin ban sha’awa kowacce da tata designe,sukuma su bunayya suka saka jallabiyoyi masu shegen kyau difference colors,hakama su momyn bunayya wato iyaye mata jallabiyoyi suka saka masu tsadar gaske,suma su dadyn bunayya jallabiyoyin suka saka da alkyabbu,yaukam antina da al’ada ahalin gidan kebir kemel,ansha shayi anyi rawar arabs daga bisani akaci abinci akai picsis sannan aka watse. Da dare around 10pm aka kai amare gidajensu. Dik wannan shagalin da akayi ashe mahabub d’an abokin dadyn bunayya yana nan yakafe bunayya da ido batareda tasaniba, tini yasamu phone number d’inta sannan yafadawa mahaifinsa yaganta kuma tamasa yana santa. Bak’aramin dad’i mahaifinsa yajiba harma yace “damacan wlh inatasan namawa Alhj kadel mgn,inasan nahad’a zuriah dashi kodan mukara dank’on anokantakarmu, ashe Allah yana sane da abunda ke raina,to Alhmdllh naji dadin wannan abun wlh Allah yasanya albarka aciki” mahbub yace ameen. Washe gari dadyn mahbub yasami dadyn bunayya a office dinsa,dady yamatukar jin dad’i daganin abokinsa,bayan sungama gaisawa da yar fira,sai dadyn mahbub yafadawa dady abun alkhairinda ke tafe dashi. Toh kamar dai yanda yayiwa abban ramadan yanzuma haka yayiwa dadyn mahbub yakuma kara da fadin “kagane maishaddah, bunayya fa bawata mai shekaru bace yarinyace sosai girman jikin ne kawai mutane kegani amma batada wasu shekarunda zaace har amata aure ba,gsky ni banshirya yimata aure ba sai zowa nan gaba,kaga yar uwarta saida takammala karatinta na matakin degree sannan namata aure to haka itama haka kuma sauran yan uwansu,sbd haka ayi hkr dan Allah, Allah yabashi wata wacca tafita kawai, that’s all”. Bak’aramin mamaki dady yabama dadyn mahbub ba, shifa yana ganin amintakarda ke taakaninsu tawuce ma yazo yafada masa wai d’ansa yanasan yarsa takaiga saidaima yafadamasa yayiwa yarsa miji kawai,ashe abun bahaka bane,tsananin mamaki hanasa magana yai kawai saiyace. “Ohk...no problem Allah yahad’a kowa da rabo na alkawari” yace ameeen. A b’angaren bunayya sam batamasan wace wainar ake toyawa ba,kwatsam sai lbr taji agunsu mariya wai abban ramada yafadawa hajiyarsu shima kuma dadyn mahbub ne yakirasa yafadamasa abunda dadyn bunayya yamasa sbd sam baiji dadin abunba kokad’an. Itafa bunayya wannan al’amarin na dadynta yafara bata tsoro, takasa gane dalilinsa nayin wannan abun,saidai itakam tinda yarabata da yayanta ramadan to komawa zai rabata dashi indai ba momyntaba toko ajikinta. .................... Bayan sati daya kacal dafaruwar wannan lamarin kwatsam kuma saiga wani d’an mak’otansu Dr. Jamal yazo yanasan bunayya, ranarkam su bunayya sunsha mamaki,dik irin tsoro da gudun zuciyar hajirasu dady dayakeyi baihana yazage yadinga cin mutunci da masifa agabanta ba kawai sbd yaron yaturo wani uncle dinsa har gidan yanaso abashi dama yafara zowa gun bunayya,itakanta hajiya abun yamatukar bata mamaki. Yana gama masifarsa kawai yafice fuu cikin tsananin fushi da bacin rai. Mamaki yamatukar cikasu gakuma tarin tambayoyi tinjim a zuciyoyinsu, shin miye dalilinsa nak’in amincewa ya fitarwa da bunayya miji...? Shin miye manufarsa nak’in amincewa a aurarda bunayya dawuri....? Shin menene dalilinsa nak’in amincewa samari su rab’i bunayya dasunan soyayya ko aure....? waennan tambayoyin ne suke neman amsoshin su. ........................ Ahaka rayuwa tacigab da tafiya tana gudana cikin walwala. Izowa yanzu bunayya sunkusa fara exam ta first semester, danhaka yanzu karatu suke ba wasa, tini takoma hostel da zama sbd karatu yafara zafi. #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _17/18...._ Zaune suke acikin room d’in hamdallah sabuwar k’awarda bunayya tai anan FUBK, wata yar mitsitsiyar rigace ajikinta ta bacci sai d’an pant,itakuma hamdallah towel ne ajikinta da’alama daga wanka take. Abinci sukeci atare indomie da dafaffen kwai,sunaci bunayya na chart itakuma hamdallah tana duba wani littafenta, bunayya tace “yar uwa” kamar yanda suke kiran junansu kenan “kinsan Allah idan bamuyi dagaskeba Mr habeb saiyabamu mamaki da muguntarsa,kinga dama yanajin haushinmu da surutu awajen lecture” hamdallah ta tab’e baki tareda fadin “hmm..bari kawai yar uwa,nima naga alamar idan bamu nunamasa munsan kanmuba bak’aramin mamaki zai bamuba wlh”. Bunayya tace “bari kawai,aikwa zamu bashi mamaki insha Allah, Allah dai yataimakemu yakuma azamu akanshi,sbd bak’aramin mugu bane wlh,zai iya cutarmu koda gb dinmu yai kyau” hamdallah takara gyara zamanta tana fadin “Allah yafisa yar uwa,muyita addu’ah kawai dakuma karatu” nan suka sake dakko wata firar har suka kammala cin abincin. Bayan sungama sannan bunayya tashige toilet domin yin wanka,koda tafito tini hamdallah tashirya tsab acikin gown ta material yellow da d’an mayafi wanda tad’an d’ora akanta kasancewar ba d’an kwali akanta. Cikin sauri bunayya tashirya acikin wandan jeans dark blue da riga fara wacca tad’an sakko mata tarufe matasan zamanta, saita taje sumarta sannan ta tufketa gu daya sannan tasaka yar hula akai, saikuma d’an k’aramin mayafi data dora kan shoulder d’inta, daganan tasaka tirare sannan tadauki handout d’inta da phone d’inta suka fice. Tin 8am dasuka fara lecture sai 6pm sannan suka fito gaba daya, dik agajiye suke bazasu iyayin girki ayanzuba, danhaka kawai suka fice wani sabon restaurant da aka bud’a nan domin suci abinci, Koda sukaje wurin acike yake kuma samari sunfi yawa,danhaka kawai sukai takeaway suka fice. Suna cikin tafiya saisukaji anamasu magana a bayansu, saisuka tsaya batareda sunjuyoba, cikin bacin rai yafara magana “ruwaidah ya inata magana kinajina kuma zaki kyaleni, kinsan banasan iskanci koh koni sa’anki ne dahar zan dinga kwallah maki kira kinaji kuma ki kyaleni,tukuna ma meya kawo school dinnan a wannan lkc...?” dik maganarda yake kallonsa kawai suke dan basuma fahimci inda yadosa ba. Bunayya ce tacemasa “kai mallam,mufa bamu fahimci inda zancenka ya dosaba, inma wani abun kake nema kai hkr dan bamu gansaba” tana gama fadar hakan tajuya zasu tafi saiyai saurin shiga gabansu. Cak suka tsaya cikin bacin rai saiyacigaba da fadin “wlh banasan iskanci,yanzin nan saina sassab’amaki wlh” abun nasa mamaki ma

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});