Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dinda aka shiryamata, danhaka tana fitowa suka fice dining room inda aka cika wajen da abinci kala kala masu kyayatarwa,ni kaina abun yamatuk’ar k’ayatardani ba kadan ba. Nan suka zauna aka shiga savin nasu, ahankali suka fara ci suna shan fira har suka kammala sannan suka koma parlor,itadai bunayya dik firarda akeyi bada itaba asalima hankalinta yana kan phone dinta tana chart. Around 10pm tamasu saida safe tashige bedroom d’inta tai kwanciyarta. Washe gari dakyar momy tasakata tai sallah tai wanka sannan tasake kwanciya, sai 12pm dot sannan tafarka,bayan tafarka tai wanka tacanja kaya izowa doguwar riga mai dogon hanu bak’a girmanta har kasa. Bata shafamawa fuskarta komaiba tadaisaka tirare sannan tafita, a parlor ta taddasu momy da dady suna wani aiki akan laptop, nan tamasu barka da safiya sannan tajekan dining tai breakfast. Bayan tagama sannan tadawo parlor,kwanciya tai akasa kusa da dadyn ta tad’ora kanta akan cinyarsa,shikowa hanunsa yadora akanta yana shafa sumarta yanakuma cigaba da aikinsa. Momy ce tad’ago tadubeta tace “kishirya kayanki gobe zamu fice kebbi” Ohk...kawai tace sai momy tacigaba da aikinta. ..................... Washe gari around 10am suka fara shiri,nanfa akafara kwasar rigima tsakanin momy da bunayya wajen saka kaya,momy tanaso koda jallabiya ce bunayya tasaka sbd outside da habuja ba d’aya bane da kebbi, kuma tasan matuk’ar akaga shigarda bunayya keyi baza’aga lefin kowaba sai ita,gashi yanzu kokadan batasan abunda zaisake shiga tsakaninta da hajiyar kadel,to matuk’ar kowa taga yanda suke kula da bunayya dakuma tarbiyyarda suka bata ba abunda zai hana sukoma yar gidan jiya. Danhaka ta dage sai bunayya tasaka jallabiya itakowa tace bazata sakaba sbd zafine da jallabiyar gashi sau daya ta taba sakata lkcnda sukaje saudiya aikin haji,shima sai idan zasufita take sakawa dasun dawo gida tacire shkn. Dakyar da sud’an goshi tayarda tasaka shima saida dady yasaka bakinshi ya lallab’eta amma saida tai kuka tasaka. Around 12pm dot jirginsu yad’aga izowa kebbi state, sai kusan 4pm sannan suka sauka. Abban ramadan wato kanen dady wanda kebinsa da d’ansa ramadan dakuma bodyguards guda hudu ne sukazo tarbonsu,bayan sungama gaisawa sannan suka fice. Kai tsaye kantamemen gidansu da aka gina masu sabu atareda sabon companyn su aka wuce dasu,koda suka isa tini angama komai ank’ara tsabtaceshi tsab,komai tsabtsab tastas, gidan upstairs ne hawa biyu acikin GRA,bayan sunsaukesu sannan suka fice. ...................... Washe gari around 10am suka shirya domin tafiya gidan hajiyar kadel, nanma dakyar bunayya tasaka wata jallabiya red color mai shegen kyau itama saida tasaka wandan jeans blue da t-shirt fara akasa dan dasunje cire jallabiyar zatai sbd bazata iya kayan zafin nanba, ga zafin gari gakuma na kayan jiki. Motoci hudu sukaje dasu,tin a kofar shiga bunayya ke kallon yanayin gidan tana tab’e baki daga bisanima tamayarda hankalinta kan wayarta. A babban parlon hajiya suka taddata zaune akasa ta kishingid’a da matashi,cikin matuk’ar girmamawa suka risina suka shiga gaidata tana amsawa fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa masu,itama bunayya yanda taga iyayenta sunyi haka tai, cikin sakin fuska itama ta amsa mata tana tambayarta karatinta ta amsa mata da “Fine” tana zama kan daya daga cikin dank’ara dankaran kujerunda ke cikin parlon. Suna anan saiga abban ramadan da matarsa hajida maccha tareda yayanzu mata biyu nabila da mufida sunshigo, cikin farinciki momy da hajiya maccha suka rungume juna hajiya maccha tazo takama hanun bunayya cikin fara’a bunayya tagaidata itama cikin sakin fuska. Suma su nabila sukazo gun bunayya suka zauna sannan suka gaisa, nan suka jata suka fice izowa side dinsu daita. Wunin ranar dai anan sukayisa, sai dare sannan suka koma gida, Hakama washe gari suka sake shiryawa sukaje bagudo gidansu Hajiya jolde,anan bunayya taga tsintsar so da k’auna dakuma tarin gata,hatta kakarta wacca akasaka mata sunanta wato hajiyar momy kamar ta had’iyeta dan so. Aranarma anan suka wuni har dare, sai 8pm sannan bodyguards dinsu sukazo suka wuce dasu. ...................... Bayan sati d’aya da dawowarsu momyn ammar da iyalinta suka sauka k’asar,itama koda taiso ankammala gyara nata side din,side dinsu bunayya ke daga dama nata kuma ke daga hagu kowanne hawa biyu ne. Yanzu yayan momyn ammar bakwai maza uku mata hud’u, aunty Mardiyya itace tafarko sai Amir da ammar waenda suke kusan tagwaye sbd bawani tsere a tsakaninsu, sai munawara murjanatu muslimat saikuma auta affan wanda yaci sunan kakansa kabir. Aunty mardiyya da Amir dik sun kammala karatunsu na matakin degree sai ya ammar dake 200level, munawara itace sa’ar bunayya sauran kuma dik k’annenta ne. A ranarda suka tare aranar kadel yatarasu sudika a babban parlonsa na side din hajiya jolde wato momy yamasu nasihoho masu ratsa jiki akan zaman lafiya sannan yarok’i su momy da karsu hargitsa masa gida kuma karsu shiga tsakanin yayansu, sukuma yayan yamasu tasu nasihar akan su k’aunaci junansu, daga bisani yarufe taro da addu’ah kowa yawatse. ..................... Sannu ahankali kowa suka fara gudanarda sabuwar rayuwarsu acikin sabon gidansu, yayinda ad’ayan b’angaren companyn Bunayya NLT Company yafara aiki, tini komai ya kammala nasa kama da d’aukan ma’aikata da dai sauransu, aunty mardiyya da ya amir ma and’aukesu hakama baba k’arami wato kamal babban dan abban ramadan wato kanen kadel kenan shima and’aukesa, hakadai akaita d’aukan ma’aikata manya da k’anana aciki. A b’angaren mr. bunayya kowa wannan dawowar dasukai Nigeria bak’aramin babban damuwa da tashin hankali yazamemata ba, sbd yanzu a kullum gida take bata fita koina sab’anin can london datake yawanta san ranta. Danhaka tafara neman mafita. Tin 10am su momyn ta kefita aiki danhaka dasun fita take ficewarta, hakama da dare bata iya zama saitad’an fita mika k’afa gashi batasan wuraren shak’atawa dayawa ba. Tini ya ammar yasakamata ido sosai har saida yagano inda take zowa,nantake yafahimci abubuwa dayawa agareta kuma ya tabbatar da dadynsu yasan tana fita tinda some times yakan dawo gida batareda ta dawoba. Dikda yasan rayuwarda sukai a outside daban danan amma baidace ace yar gidansu tana zowa club ba, danhaka yaje yasamu dady yamasa maganar. Ga mamakin ammar sai dady baiwani nuna damuwarsa ba saima cemasa yai karya damu zaimata magana kawai. Ganin haka yasa yadan daga kafa kwana biyu saikuma yaga bata daina fitarba yanzuma sai 4am take dawowa gida. Danhaka yasami ya Amir yafada masa komai, sai Amir yace yabari zaimata magana, Amir yakirata yamata magana hmm nantai cikin ya amir da masifa ita wallahi bawanda yaisa yahanata yin yanda takeso,bawanda yaisa yahanata jin dadin rayuwarta, dama shys aka maidasu nan dan adinga shiga rayuwarta. Amir baice daita uffanba tana gamawa tafice abunta, still da daren ranar tasake fita. Washe gari kamin yaje koina saiyaje gun abban ramadan yafada masa komai abunda ke faruwa, abban ramadan yace “dama tinda naga yanayin yarinyar nan nasan dole waennan matsalolin zasu faru, yaya da yaya jolde sunsakewa yarinyar nan sosai, saikace yar gold,amma karka damu Amir insha Allah zand’auki mataki akai” amir yai gdy sannan yafice. Washe gari around 9am abban ramadan yatura su nabila yace dik yanda zasuyi sutaho masa da bunayya karsu kuskura suzo bada itaba, aikwa haka akayi suka mata karya sukace hajiyar dady ce tace suzo daita tanaso taganta, batai musuba kowa tashirya cikin wando da riga matsattsu sai yar hula data d’ora akanta, sab’anin su dasuke sanye da hijabs dinsu. Komai bata d’aukaba sai wata yar jaka datake saka phone dinta, nan suka fice. Suna zowa kai tsaye suka fice

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});