Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daita parlon hajiya inda ita hajiyar ke zaune tahad’iye rai dakuma abban ramadan, tana ganin haka k’irjinta yafadi ras ras, cikin sakin fuska abban ramadan yacemata “yata bunayya zauna inaso zanyi magana dakene “ ba musu ta zauna dikda tsoro da fargabane fal a zuciyarta na rashin sanin abunda zai faru daita ba, amma haka tadake a fuskarta take nuna batada wata damuwa. Ahankali yafara magana “yayankine yazoman dawata magana shine nace bara naji daga bakinki kema” nan yafadamata dik abunda ya amir yafada, hajiya tafara magana cikin kakkausar murya. “Dik acikin danginmu ba mai irin d’abiar taki wlh saidai idan can ne dangin uwarki kika dakkota, to bara kiji nan bakamar kasar arna bace sannan muba irin iyayenki mukeba dasuka sake maki kinayin abunda kikeso shashasha mara hankali wacca tai gadon hauka awurin uwarta,damacan nasan zaarina wlh dole asamu wanda yadakko halin danginsu acikin abunda zata haifaman.....” bata k’arisaba dasauri bunayya ta taryeta da fadin. “He...he tsohuwa kada ki kuskura ki zagarman mahaifiya wlh dan kinga na kyaleki, am not tolerate wannan zagin naki kinjik...” bata k’arisaba abban ramadan yawanketa da kyawawan marika waenda saida taga taurari namata yawo, dan tinda tazo duniya ba’ataba mata irinsu ba. Aikwa batasan lkcnda tafasa wata iriyar k’ara ba tareda dafe kuncenta. Belt dinda ke kugunsa yaciro yafara zabgamata aikwa nan bunayya tafara tsala ihu tana neman d’auki, haka yazage yabulalemata jikinta tsab sannan yad’auketa yaturata acikin daki yarufe. Gaba daya bunayya tafice daga hankali dikta daburce, tai kuka kamar ranta yafita tinma tana iyayinsa da sauti har muryarta ta disashe kwallah suka kafe, tinda take a rayuwrta ba’ataba mata irin wannan dukanba, kai atarihin rayawurtama ba’ataba dukanta ba. Tana cikin kuka har bacci ya d’auketa, sai kusan 4:30pm tafarka ga yunwa ga kishi amma haka wani baccin yasake fizgarta sbd azaba. More comment more typing pa, naga kun rage comments kodai lbrn ne baimakuba abari. #/Comment nd’ Share. #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI.......*_🌷 _Wattpad@Aufana8184_ _13/14....._ Haka takwana itakadai acikin d’akin ba cin abinci bare shan ruwa, har izowa yanzu baccin wahala take,jikinta dikyai tabo tabo na duka, ita sallah bama’a maganarta. Hajiya maccha ce tasaka bakinta a zancen sbd sanin halin abban ramadan idan yai fushi ransa yab’aci to yanada wahalan sakkowa, danhaka tashiga bashi hkr amma daga k’arshe saima yace ta tafi tanashi wuri dole yakoyawa bunayya hankali yagyara mata zamanta, bata daina bashi hkr ba har saida tasamu nasara akansa. Dasauri taje tabud’e kofar dakinda bunayya take a ciki, ak’asa tahangota a kwance yanda tazo kayan jikinta har yanxu haka suke bawani abun da aka canja,hakan ya tabbatar mata dacewa yanda take a jiya haka take har yau. Dasauri taje ta tallafo fuskarta data kumbura sosai sbd kuka,nantake wani irin taisayinta ya mamayeta,ahankali takama ta mik’arda ita tadora hanunta kan shoulder d’inta tana taimaka mata har suka fita. Dakyar hajiya maccha tasamu tagasawa bunayya jikinta sbd kukanda take dan azaba sai kiran dady da momy take,sabon kuka yazomata yanzu sbd ganin irin dukanda abban ramadan yamata, gani take dik duniya anmata abunda bawani wanda yatab’a mata kamarshi sai kuka take sosai tana kiran iyayenta. Dakyar ajiya tasamu tasha tea sannan tacanja mata kayan jikinta tasakamata na sa’arta nabila riga da wando masu kyau, har yanzu kuka take tana kiran iyayenta . Dakyar hajiya maccha tasamu tadaina kukan,nan tashiga mata nasihohi masu ratsa jiki akan takare kanta namatsayinta na y’amace kodan tazama uwa tagari agun y’ayanta, Da’alama kam nasihar tashiga jikinta dan tai shuu tana sauraren abunda hajiyar kefada,daga bisani hajiya tafita tabarta acikin d’akin. A ranar hajiyar dady tasaka aka kirawo mata dadyn bunayya,yana zowa yaga yanayin fuskarta yasan akwai damuwa, kamar yanda yasaba haka yadurkusa har k’asa yagaidata, ko kallon kirki bata masaba barema ta amsa gaisuwarsa,zama yai akasa itakuma tanakan kujera. Ahankali tafara magana cikin kakkausar murya “nakirakane domin yasanya maka albarka akan irin tarbiyyarda kabama y’arka fatima,lallai kayi k’okari sosai sannunka,amma kasani kadel ni Sam bazan d’auki wannan iskancin da lalacin ba,wai yanzu acikin zuri’ata za’asamu wacca take zowa night club kuma ma wai mace ba namiji ba, eh...toh wlh kasani idan har kai bazaka iya kula daitaba ni zan iya shys ma na tura aka d’akkomin ita, daga yanzu kuma tadawo nan da zama sbd naga alamar ku bazaku iya tarbiyyantarda ita yanda yadaceba,wato ku gaku sarakunan san yaya”. Tinda tafara magana dady baice uffanba harta gama,bayan tagama yarisinarda kansa kasa yace “Allah yahuci zuciyarki, ayi kr insha Allah baza’a sakeba,za’a gyara” tab’e baki tai tareda fadin “tashi kabani wuri” haka yamike kowa yafita yana kara bata hkr. Yana fita yadoshi parlon abban ramadan,kan hanya gaba daya kansa yad’auki zafi lissafinsa dikya jagule, hankalinsa yamatukar tashi sbd yafi kowa sanin halin hajiyarsa haka kuma yafi kowa sanin halin bunayya, yasani bunayya batada tsoro danhaka zata iya mayarwa da hajiya magana idan tamata magana ko fad’a,itakuma hajiya yasan bazata bartaba, danhaka hankalinsa amatukar tashe yake sbd baya kaunar abunda zai taba yar gold dinsa. Dazuwansa hankali a tashi yashiga tambayar abban ramadan ina bunayya yana buk’atar yaganta, nan abban ramadan yacemasa yaje yatambayi Hajiyarsu idan ta amince sai kaishi gunta yaganta amma idan bata aminceba saidai yai hkr. Abun yabashi matuk’ar mamaki sbd irin yanda abban ramadan ke girmamasa amma yau shine yakefadawa haka, saidai sam bazai iya zowa yatinkari hajirasu da wannan maganarba sbd sanin halinta baram ma yanzu datake hassale dashi,danhaka bayanda yaiya haka yafice batareda yaganta ba. Hakama dayakoma gida momy tashiga tambayarsa bunayya k’arya yasamu ya k’irkira yafada mata, hajiya ce taje tamata hutu kamin anema mata admission tafara karatu, jin hakan yasa bata wani d’aga hankalinta ba saidai na rashin ganin abar k’aunar tata tsawon kwana daya sannan yanzu gashi har zatai zama mai tsayi batareda ita akusa daitaba. Dik yanda dady zaiyi domin ganin hajiya jolde bata damuba saida yai yadinga janta da firar office. A b’angaren bunayya kowa hajiya maccha ce tayita kula daita harta fara warwarewa daita dan dafarko k’in sakewa daita tai barekuma su nabila da yaya ramadan daketa janta ajiki, ahankali ahankali harta fara sakewa dasu sbd taga ba sarki sai Allah. Tafannin girki ma dakyar taiya fara cin tuwo da miya saidai kullum ramadan nakan hanyar restaurant wajen yomata takeaway, amma yanzukam tanacin shinkafa hakama tuwo, aikwa bak’aramin dady ramadan da hajiya maccha sukeji ba. Saidai tafannin kayan sakawa kam haryanzu takasa iya saka atampa wai zafi musamman yanayin k’asar dabata saba dashiba, fahimtar hakane yasa hajiya maccha tabar takurata akan saka atampa saidai ahankali ahankali take sakata tasaka. Har yanzu idan sukaje gaishe da hajiyarsu dady da abban ramada basu amsa mata, ramadan ne yai iyayinsa har suka fara amsa mata,hakan kowa bak’aramin dadi yayiwa hajiya maccha da yaya ramadan ba. ....................... Sannu ahankali bunayya harta kwashe wata biyu a gidan,saidai abun mamaki bunayya tasake sosai dasu nabila da yaya ramadan, yanzu idan kaga yanda take gudanarda rayuwarta sam bazakace ita bace kayanda take sakawa daine har yanxu bata dainaba amma komai nata yacanja. Atare da hajiya dasu nabila suke shiga kitchen suyi aiki,hakama aikace aikace gidan dik atare sukeyi tin bata iyayi sbd bata sababa harta iya. Gakuma wata shak’uwa data shiga tsakaninta da yayanta ramadan,tsintsar shak’uwa ce tashiga tsakaninsu, itake had’amasa break hakama d’akinsa itake gyaramasa kullum, haka zai

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});