Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,265 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Dan murmushi tai tareda juya fuskarta gefe d’aya,ahankali yafara mata magana “bunayya meyasa kike b’oyemin kanki,bayan kuma kinsan ganinki yazameman tamkar cin abincina,rashin ganinki kuma tamkar rashin shan ruwanane,tsawon kwana uku kinsakani nadawo kamar mahaukaci,dik na karad’e school dinnan da inda muke zama harma da inda bama zama dik naje nemanki amma bake,haba so kike kishirwar rashinki da yunwar ganinki sukasheni” dasauri ta girgiza kai alamar bataso saiyacigaba “to meyasa kike b’oyeman kanki, nifa wannan kunyar tana nema tafara cutardani,gsky bazan iya jure wannan ba,yanzuma hamdallah ce tafad’aman inda kikai shine nabiyoki hadda guduna” dariya tasub’uce mata lkcnda taji yafadi wai hadda gudunsa dan kawai yaganta. Shima dariya yai sannan yagyara tsayinsa tareda fadin “muje narakaki” sai itama tagyara sannan suka jera sunacigaba da tafiya. Magana yake mata tana saurarensa “am....dama jiyane nakira dady na nafad’amasa komai tsakanina dake,nakuma cemasa kina matuk’ar k’aunata har cikin zuciyarki nima kuma ina matuk’ar kaunarki har cikin b’argo na, danhaka munbasa dama yaje yasami abban ruwaida suje sunemaman aurenki agun dady,kuma inaso nanda wata biyu kacal kizamo matata uwar yayana”. Wani murmushi tai Na farinciki hadda rufe fuskarta kamin tace “waya fad’ama ni inasanka,to kayi kuskure dabaka fara neman izininaba dakuma jin amincewata ba, ma’ana inasonka ko bana sanka, sbd haka kai saurin kiran dady kafad’amasa yadakata har saina bada izini” tana maganar tana masa wani kallo cikin murmushi, tana gama maganar kuma saita juya tashige hostel dinsu. Murmushi yake yana kallonta har tashige sannan yashafa sumarsa da sajensa yajuya yafice yana fadin “zaki gane kurenki idan kikaji ansaka rana nanda wata biyu kacal. ....................... Labari mai dad’i yarizk’e abban ruwaida, shikuma abban ruwaidah yakira su abban ramada yasanardasu yaran sun had’a kansu sunkuma fahimci junansu,a yanzu haka sune suka bada damar atsayar masu da zance d’aya. Nan hajiyarsu dady tabada damar sati na tafe azo ayi komai,tanaso ayi komai lkc daya hadda saka rana dakuma sadaki,amma za’ayanka sadakin ne kawai baza’a biyaba har sai ranar d’aurin auren. A dika ahalin biyu bawanda baiyi farinciki da murna da wannan lamarin ba,musamman momyn bunayya dakuma su dadyn mashkur,abban ruwaida saida yai sadaka ranar sbd gdy ga ubangiji daya tsaramasa wannan lamarin acikin ikonsa da buwayarsa. Tofa dik wainarda ake toyawa dadyn bunayya baisaniba,hakan kuma yafarune ta umarnin hajiyarsu,tace kar wanda yafad’amasa har sai ana gobe zaayi tambayar, danhaka abban ramadan dasu ya ammar bawanda yafada masa. Toh rana bata k’arya saidai uwar d’iya taji kunya,gobe Friday itace ranarda zaayi engagement din bunayya da mashkur had’eda yanka sadaki dakuma saka rana. Shiri na musamman momyn bunayya keyi,danginta kusan su goma da yara yammata sa’annin bunayya dama yayyaenta waenda sukai aure dik sunzo,gidanfa yacika taf da mutane sai shirye shirye ake ana girke girken namu na kaji dana raguna da snacks kala kala. Dady side din momyn ammar yake shys baisan wainarda ake toyawa ba, sai kusan 1pm sannan yafito yashigo side din na momy, abunda yaga anayi yamatuk’ar bashi mamaki sbd shidai baisan ana wani bikin a dangin momy ba, gashi kuma yaga su yaya hauwa dasu aunty kuluwa dik sunzo. Bedroom dinsa yafice yace akiramasa momy tasamesa d’akinsa. Koda taje ta taddasa yana neman wani file d’in,batareda yad’agoba yake tambayarta “maryama tawa,wane biki akeyi a gida hala dahar akek’in fad’aman saidai naga ana shagali” hararansa tai dikda baya ganinta tatsuke baki sannan tace “ai wlh kyaleka kawai nai ina duban hankalinka, kana nufin kai bazakayi shirin tarban bak’inda zasuzo bane koyane” d’agowa yai yamatso kusa daita sannan yace “hajiyaaa....nifa banma fahimci abunda kike nufi ba” mamakine yacika momy ganin zahirin gsky a fuskarsa. Gyara tsayuwarta tai sannan tacigaba da magana “Alhj kana nufin kaceman bakasan gobene zaayi baikon bunayya da mashkur ba hadda yanka sadaki dakuma saka rana ba” files dinda ke hanun dady ne suka fadi lkc daya tareda furta “what.....!!! har saida momy taja da baya cikin firgici. Nantake idanuwansa suka kad’a a lkc d’aya,k’afafuwansa nema sukai sukasa d’aukansa hakan yasa dasauri yadafe gado sannan yazauna, tsorone yakama momy dasauri tarikosa tareda fadin “kadel lfy kowa, wai meyake faruwa ne daga nafadama zaayi baikon su bunayya shkn mood dinka yacanja” kasa cemata komai yai sai mik’ewa yai tsaye yafara zarra acikin dakin kamin yadubeta yace “waye yai wannan had’in” momy tace “yaradai sune suka had’a kansu sannan manyansu suka shiga gaba,hajiya kuma itace tasaka ranarda zaayi baikon” waro idanuwansa yai tareda furta “hajiya kuma,kardai kiceman hajiyarmu” tace “Eh ita”. Dafe kansa yai tareda furta “innalillahi wainna ilaihi rajiun,shkn sungama dani,to amma wlh anyanka ta tashi” cikin tsintsar mamaki momy tace “mekake nufi da hakan kadel...?” batareda yadamu dakowace yake magana daitaba yace “ina nufin bazan taba amincewa da wannan had’inba, sam bazan amince da wannan lamarinba” mamakin momy karuwa yai. Tacika taf da mamakin dady, cikin mamaki tace “kadel meyasa bakasan dik wani namiji yarab’i bunayya,meyasa kake k’in amincewa dadik wani namiji dayazo neman auren Bunayya,meyasa...meyasa kadel” dasauri yafurta “sbd AURENTA ZANYI....maryam” yafad’a dak’arfi har saida momy taja da baya dasauri tareda dafe bango, nantake kwallah suka fara zubomata na mamaki da rakaici. Gaba d’aya dady yafice acikin hayyacinsa yadawo tamkar mahaukaci,cigaba yai da magana cikin kakkausar murya yana zazzaro idanu yana nuna momy yace “bawani d’a namijinda yadace da bunayya, nine nan namijinda yadace ya aureta, inaso kisani maryam, tin lkcnda bunayya tafara mallakar hankalinta girma yafara kamata tin lkcn matsayinta yacanja a zuciyata,nikaina bansan lkcnda zuciyata takamu da tsananin SO dakuma K’AUNAR bunayya ba,bansaniba maryam”. Kwallah momy keyi masu zafin gaske bakinta har rawa yake hakama jikinta karkarwa yake kamar maijin sanyi, bakinta na rawa tace “kak...kak...kadel,yau kaine dakanka kake fad’ar kanasan y’armu bunayya da aure, kadel wace amsa katanadarmana wacca zamubama ahalinmu biyu,kadel kayi tinani mai kya mana,koda badan kaiba,kodan ni kadel”. *Aslm...my fam. am kuyi hkr kwana biyu najina shuru,jikin ummanmu ne sai ahankali,amma Alhmdllh tafara samun sauki sosai,muna gdy da adduoinku,kucigaba da sakata acikin adduoinku dan Allah,Allah ibata lfy mai d’orewa Ameen.👏 #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _29/30....._ Kuka momy keyi mai tsanani tana fad’in “haba kadel haba haba...wannan wane irin gurb’ataccen tinanine zuciyarka keyi,kada kabari zuciyarka ta rinjayenka mana,katinafa bunayya y’a take agaremu ba k’anwa ko y’ar uwa ba,kadel taya zaka furta wannan kalmar ta SO tsakaninka da bunayya” shikansa kwallah yake zubarwa waenda yakasa sanin namiyene. Cikin muryar kuka yake fadin “nima bansan sadda abun yashiga zuciyata ba Maryam,nadade ina d’awainiya da SON bunayya,wannan dalilin ne yasa nahana kowanne namiji ya rab’eta dasunan soyayya ko san aure badan komaiba saidan naji saukin samun kanta wajen amincewa dani, wlh maryam bazan taba iya rayuwaba idan ban auri bunayya ba,nikad’ai nasan irin k’aunarda nakemat....” bai k’arisaba momy tai wata k’ara mai sautin gaske tareda furta “ya’isa haka kadel,banasan nasakejin wannan maganar”. K’ararda tai yasa hankalinsu aunty kuluwa yatashi sukayo d’akin dagudu domin ganin abunda ke faruwa, momy naganinsu taje da gudu tarungume aunty kuluwa tana kuka mai tsanani,gaba daya hankalinsu yatashi matuk’a ganin momy da dady suna kuka,tambayarsu suka shigayi a firgice abunda ke faruwa. Dakyar momy taiyayin magana cikin sheshekar kuka “kufad’amasa yajanye k’udurinsa na auren bunayya dan Allah,nayi nayi amma yadage akan saiya aureta wai,nikuma wlh bazan iya zama da y’ata a matsayin kishiyata ba,wlh mutuwa zanyi dik yak’i daina wannan maganar”. Gaba daya sun rikita kwakwalwar su

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});