Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,275 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

idan har aka tabbatar ba gsky bane kamanceceniya ce kawai kuke zanbar maganar har abada insha Allah”. Tini kwallah sungama wankewa bunayya fuska dakyar taiya gyada masa kai alamar tayarda,nan suka dunguma suka fita,sudika akai tafiyar dasu,dayake unguwar batada nisa da wannan unguwar nantake suka isa,atare gaba daya hadda momyn mashkur dakuma security’s hudu suka tafi. Shima gidan kam sai kallo kawai sbd shima bak’arami bane,amma shi yafi kama da gidajen sarautu,sbd komai nasa irin na gidan sarauta ne, daisarsu mahaifin ruwaida Alhj sunusi suka fara cin karo dashi yana alwalar magrib,yana ganinsu baiko k’arisaba dasauri yamike tsaye arazane,waro idanuwansa yai tareda dafe kirjinsa kamin yakwallah kiran “Hajiya...hajiya maimuna kina inane?” wacca yakira da maimuna tafito daga wata kofa dasauri a firgice sbd irin kiranda yake mata. Tana zowa taga bunayya da ruwaida atsaye gu daya,tsananin mamakine ya bayyana k’arara a fuskarta kamin tamatso kusa dasu ta tab’a bunayya takuma taba ruwaida, dik hakan baimasuba har saida tariko hannayensu atare,kwallah ne suka fara ambaliya a fuskarta kamin tajanyosu sudika ta rungume tana fad’in “tabbas naji ajikina wannan ranar zatazo,naji ajikina komai daren dad’ewa zan ganki da idona ko araye ko amafalki kokuma a lahira,ashe araye zan ganki” shafa fuskar bunayya tai cikin wani irin yanayi naban tausayi tace, “Bansan miye dalilinsu ba narabani dake,bansan memuka masuba suka rabamu dake” kwallah sungama wankewa bunayya fuska tas bakinta har rowa yake tafara magana “in..in...inaso kibani lbrn ya’akayi kuka rabu dani tin ina acikin tsumman goyo wato jinjira..?” momyn su mashkur ce tai saurin cewa ku dakata, Is okay...wannan zancen ba’anan yadace ayisaba,kuyi hkr gobe mushirya gaba daya mutafi kebbi gun iyayen ita bunayya,acan yadace ayi wannan zancen domin gano gskyr wannan lamarin,yau by 8pm VC zai dawo insha Allah,so kunga gobe saimu tafi gaba daya”. Nan suka d’unguma suka shiga cikin gida atare, Alhj Mahmoud mahaifin ruwaidah yakasa zaune yakasa tsaye da farinciki sai nan nan yake da bunayya,haka itama ruwaida da momynta,kai incemaku kowama sai nan nan yake daita kamar suhad’iyeta. Saidai ita dik wannan baya gabanta,tarin tambayoyinda ke gabanta sunma hanata sukuni,tamatsu safiya bata wayeba taganta kebbi,abincima k’inci tai gashi su ruwaidah sunhad’amata kala kala kuma dik waenda takeso ne dan mashkur ne yabasu wannan satar amsar. Dik yanda sukaso bunayya tasaki jikinta takasa sunyi sunyi tak’i daga karshema saita sakamasu kuka,danhaka suka kyaleta ruwaida bataji dadin hakan ba taita rarrashinta tak’i,cikin b’acin rai takyaleta,dataga tak’i dainawa saitaje tafad’awa mashkur. Kuyi manage da wannan mahade anjina da maraice, ngd sosai da k’auna.love u all my fam.💋💔 #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _23/24....._ Dawowarsa kenan da masjid sallar isha,jallabiya ce ajikinsa maroon color da carbi kansa ba hula,koda yashigo parlor ammin sa dasu ruwaida dik suna zaune anacin abinci kamar yanda yake al’adar gidan bayan sallar isha a babban parlor ake had’uwa aci abinci atare, gaida ammin sa yai ta amsa su ruwaida ma suka gaidasa sai ammi tace. “Mashkur yarinyar nan takasa sakewa damu,kaje kaida tafi sabawa dakai kagani abincima tak’ici tin d’azun,ni airport zamuje da yaran nan d’akko dadyn ku” ohk momy....yafad’a sannan yafice izowa dakinsu ruwaida inda bunayya take. Ahankali yatura k’ofar d’akin yashiga cikin sallama,can yahangota ta tattakure akan gado,k’arisawa yai ciki yaje yazauna sannan yamata alama da hanu yana cewa “zonan” ba musu kowa kamar kazarda kwai yafashewa a ciki ta taso tazo tazauna tareda sadda kanta k’asa. Matsoda fuskarsa yai daidai tata sannan yafara mata magana “meyasa kikak’i cin abinci bunayya?” cikin murya irinta marasa lfy tace “banajin yunwa kaina ke ciwo” hanunsa yakai yatab’a goshinta saiyaji yanada zafi, kallonta yai wanda itama shid’in take kallo amma yana kallonta saitai saurin d’auke idanuwanta akansa, numfashi yasauke kamin yace “ina zowa” tareda mik’ewa yafita. Bayan yan mintina yadawo d’auke da magani a hanunsa da ruwa a glass cup, bayan yazauna saiyace “oya...karb’a kisha” juyamasa kai tai alamar aa tareda fadin “nifa komai nawa baya ciwo,iyayena nake tinani inaso naga momy da dady domin jin gskyr abunda waennan mutane suka fada, shin taya akayi har izowa wannan lkcn basu sanardani cewa basune iyayena na gsky ba, kai mashkur nifa har yanzu ban gasgasta abunda kuka fadaba,sbd da’ace momy da dady basune mahaifanaba da tini nasani koda su basu fad’amanba dole wata rana duniya tafad’aman sbd nasan dole momyn ammar taman gorin wannan abun,amma hakan bata taba faruwa daniba,bawanda yatab’a ceman su dady basune suka haifeniba, Mashkur tinda nataso bayan so da k’auna dakuma tarin gata bansan komaiba,bantaba sanin miye d’acin rayuwa kokuma bakin ciki ba har izowa yanzu,momy da dady sun nunaman gata fiye da kowa a duniya,hakama ahalina biyu dangin mahaifina da dangin mahaifiyata,a yanzu haka inada tarin miliyoyin kud’i a account dina waneda dangin mahaifiyata suka bani a lkcn haihuwata,haka kuma inada motocinda suka kai bakwai ko takwas waenda mahaifiyata da mahaifina dakuma dangina ke bani a dik lkcn birthday sbd tsintsar kaunarda sukeyi agareni,natabbata da sunsan ni ba yarsu momy bace dabazasu bani suba,har gobe bawani abu a duniya wanda momy na keso fiye dani,hakama dady na yafisona sosai akan sauran yayansa,tsintsar sonda yake nunaman yasan yan uwana sukejin haishina, Mashkur taya zan yarda da wannan labarin da kukazoman dashi, tayane mashkur...?” nannauyan numfashi mashkur yasauke batareda yace komaiba sbd kuka take harda ciccika,gashi shikowa baya k’aunar kukanta kokad’an, saida ta sausauta sannan yafara mata magana. “Bunayya inaso kigane wani abu,itafa rayuwa ba abunda bazata iyayiba domin cimma burinta,sannan inaso ki fahimci wani abun,kiyi duba da koda kamanceceniyar da kikeyi da ruwaida sannan idanma ace wai kamanceceniya ce kawai to kiduna mahaifiyar ruwaida wacca itace ruwaidan tabiyo sak,sannan kiduba sauran yan uwan rwaida guda uku,dikansu kunada kamar jini dasu,itakuma ruwaida kamarku tama b’aci wanda inba tagwayeba baza’ataba samun irin wannan kamarba,kamar jini bahaka takeba, sannan bunayya kiduba dangin can dadyn ki dakuma momynki akwai wanda akace kike kama dashi koda ba momynki ko dadynki ba..?” shuru tai tana tinani kamin tafurta kalamr “a..a” saiyace “to kingani,sannan mahaifiyar ruwaida bata taba saninkiba kuma bata taba ganinkiba saidai taji lbrnki agunsu ruwaida amma tana ganinki tagane cewa ke yarta ce wacca tahaifa acikinta” saiya gyara zamansa sannan yace “So yanzudai koma miye kiyi hkr kici abinci har gobe muje muji gskyr lamarin agunsu dady, danhaka kisakko kici abinci sannan kiyi wanka kifito parlor” girgiza masa kai tai alamar bataci. Hanunsa yakai kan cikinta tareda fadin “wannan cikin nakine zakice bazakici abinciba,ina maza sakko nabaki dakaina kinsan banasan kina zama da yunwa koh” badan tasoba kuma bayanda taiya sbd da me d’inta bayasan musu,bata sakkoba shiya dibo abincin yazo yafara bata tanaci,saida taci sosai ashe wata wahalalliyar yunwa takeji batasaniba sai a lkcn,bayan taci sannan tasha ruwa. Dakansa yad’akko mata towel yabata sannan yacire mata mayafinda tawani lullube kanta dashi yace “oya...tashi kiyi wanka” ba musu tamike tareda karban towel din sannan tashige bathroom. Koda tafito harya kawomata kayanda yasiyo mata d’azun,nan tabude tadakko wata sleeping gown mai kyau pink color mai hade da wando,sakawa tai sannan tafeshe jikinta da tirare sannan ta kwanta. Washe gari ma bata fito breakfast ba sai kaimata akayi,saida dadyn mashkur daya dawo gida da dare shine yaje sakansa har gunta yaganta tagaidashi cikin girmamawa. Around 10am dot kowa yashirya aka fara shirin tafiya,iyayen ruwaida sunzo acikin dank’ara dank’aran motocinsu har uku,anan kuma aka

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});