Chapter 21
Chapter 21
aunty kuluwa sam sunkasa fahimtar inda zancensu yadosa,cikin rashin fahimta yaya hauwa tace “wai jolde me kike nufine,kunsakamu acikin rud’u kun rikitamuna kwakwalwa, kumana kyakkyawan bayaninda zamu fahimta dan Allah mana” momy kuka take sosai kamar ranta zai fita,shikowa dady yadafe kansa da hanunsa d’aya. Dakyar momy ta sausauta kukanda take sannan tafara masu bayani sbd tasani yau ranar bayyanar asirinda suka dad’e suna rufewa ce tazo,saidai bata tab’a tinanin kadel ne silar fallasar wannan sirrin ba,nannauyan numfashi tasauke had’eda shesheka sannan tafara magana cikin muryar kuka. “Kuyafeni aunty kuluwa, dan Allah kugafarceni sannan kuyiman kyakkyawor fahimta akan kuskurenda na aikata abaya wanda babuwani mahalukinda yasani sai kadel da doctor haji,saikuma ainahin iyayen bunayya dasuka sani yanzu” mamakine yabayyana k’arara a fuskokinsu aunty kuluwa,sai momy tacigaba da magana. “Hak’ika sai yanzu ne nake nadama dakuma dana sani mai tarin yawa,batareda dogon nazari dakuma zurfin tinaniba nabiyewa kadel muka aikata babban lefin wanda akarshe yanzu nine narufta aciki,saidai wlh insha Allah koda zan rasa dik abunda na mallaka ne bazan taba bari hak’ar kadel tacimma ruwa ba” yaya hauwa tace “munajinki jolde” sai tacigaba da magana “a lkcn shekarun baya lkcnda nake neman haihuwa ido rufe a lkcn ne na amince akamun dashen kwayayan haihuwar kadel a mahaifata, cikin ikon ubangiji kowa saiga ciki ya bayyana a mahaifata,nayi matuk’ar farinciki hakama ku dangi musamman ni sbd koba komai zan rabuda gori da wulakancin uwar mijina wacca a kullum takeda burin rabani da mijina, bayan cikina yaisa haihuwa mukaje asibiti nahaihu, To saidai wani iko na ubangiji sai haihuwar tazo da matsala sbd babyn yamutu tin aciki,dagani har kadel munshiga tsananin tashin hankali musamman ni sbd a lkcn banaji bana gani idanuwana a rufe suke domin samun d’a, to hakan ne yasa kadel yasamu wani doctor haji yarokesa yakuma biyasa mak’udan kud’i domin yab’oye mutuwar babyn mu tahanyar yin exchanging babyn mu dawani babyn, haka kowa akayi sai aka canja namu babyn da bunayya. Amma asali mu namu babyn yamutu, nad’auki bunayya nakuma so ta tamkar y’arda nahaifa acikina kai har gobema jinta nake a zuciyata amatsayin d’ana dana haifa yamutu,saidai ashe shi kadel bahaka yad’auketa ba, bunayya tahad’u da mashkur makaranta wanda yana ganinta yafara bincike akanta sbd tana matuk’ar kamanceceniya da wata kanwarsa ruwaida,koda komai ya kamkama ashe bunayya tagwayece ita ruwaida itace abokiyar tagwaicinta, dafarko abun yadauki zafi daga karshe Allah yadaidaita komai iyayenta na haihuwa suka barmana ita har abada. Mashkur da bunayya sun hada kawunansu,shine yanzu akesan amasu aure,saiga kadel yafitoman da wannan sabon lamarin wanda kwakwalwata takasa d’aukansa, dan Allah aunty kuluwa kutaimakeni kurokaman shi karya bari wannan maganar tafita waje” takarisa cikin kuka. Wata iriyar harara dady ya wurgamata kamin yace “ina fadamaki maryam, kidaina fadin najanye wannan maganar,shin kinkowasan irin kaunarda zuciyata keyiwa bunayya,to kisani auren bunayya babu fashi matuk’ar ina numfashi”. Cikeda mamaki momy take kallonsa kwallah nazubarmata tace “nikwa indai ina numfashi a duniya wlh wlh wlh bazaka taba auren bunayya ba koda zan rasa komai nawane kowa” saiya tab’e baki taredayin dan murmushi sannan yaduka yadauki files dinsa dasuka fadi sannan yafice abunsa. Kallonsa momy take harya fice cike da tsintsar mamaki kamin tafashe dawani matsananin sabon kuka, al’ajabi da tarin mamaki yacika su aunty kuluwa. Dakyar yaya hauwa tace “hmm....lallai jolde kinyi babbar asara dakika amincewa namiji d’ari bisa d’ari kika d’aukesa tamkar ubanki dakika rasa shekarun baya,to yanzu kinga yamaki halin nasu ko,namiji...namiji....namiji d’an kunama dik wanda yad’auki namiji uba tabbas zai mutu maraya har abada,yanzu gashi y’arda kika raina da hanunku yakesan yamaidamaki ita tazama kishiyarki” aunty Kuluwa tace “kuma wlh idan batai dagaske ba saiya nunamata cikekken hakinsa sbd kina nan kwance kina kuka zaije yai yanda zaiyi ya aureta sbd kunyace ke garesuba mazan nan, dik yanda kikaga anamaki laf laf laf aikin banzane bazai hana gobe yatsulamaki tsiyarda harki mutu bazaki saki yarda dawani d’a namijiba”. Yaya hauwa tasake cewa “danhaka yanzu bazama zakiyiba kinata kuka tashi zakiyi kiyi tinanin mafita” cikin disasshiyar murya momy tace “toni yanzu mezanyi ne, idan nagad’i wannan lamarin awaje asirinmu zai tonu ne” cikin takaici aunty kuluwa tace “to ina ruwanki,yatonu din, ai tinda kuka aikata dole asirinku yatonu komai daren dadewa,sbd haka kid’auka kawai ranar tonon asirin ce tazo” momy tai shuu natsawon mintina. Can tadago tadakko wayarta takira bunayya,ringing daya ana biyu tadaga,batajira komaiba tace “bunayya kidawo gida ina buk’atar ganinki bada jimawaba,komai kike kidawo yanzu kuma kekadai” tana gama fad’ar hakan takatsen kiran. Bayan dakamar 3hrs kowa saiga bunayya taiso a firgice, momy naganinta tafashe da wani matsanancin kuka aikwa dagudu bunayya taje tarungumeta nantake itama kwallah suka fara zubomata tana tambayar momy cikin tashin hankali abunda ke faruwa,dakyar momy taiya fadamata komai ba abunda ta b’oyemata. Dasauri bunayya taja da baya cikin firgici da yanayin mamaki tareda furta “what....! meya sami dady na momy,sbd natabbata akwai abunda ke damunsa kokuma wanine yamasa asiri,taya dady dayake mahaifina zaice wai nice zai aura,kai ina momy wasa yakeyimaki” momy ta jijjigata tace “kidawo hayyacinki bunayya dagaske yakeyi babu alamun wasa a tattare dashi kokuma wani yanayi na sihiri ko maye, a yanzu haka har yaje can gun hajiyarsu yafad’a gabad’aya ahalinmu dika biyun ba wanda baiji wannan lbrn ba”. Kuka bunayya tafashe dashi tana fadin “wannan wace irin k’addara ce,wace irin kaddara ce wannan,yau dady na dabakinsa ke furta kalmar SO izowa gareni,koda acikin mafalki bantaba tinanin wannan ranar zatazoman ba, innalillahi wainna ilaihi rajiun,Allahumma ajirni fil musubitii haza wa akhlifni khairan minha” takarisa tareda fashewa dawani kukan. Itama momy kukan take zuciyarta cike da nadamar amincewarda tayiwa dady. Suna cikin wannan halin saiga dady yadawo, aikwa yana ganin bunayya dasauri yaje gunta yafara magana kamar zauracce “bunayya y’ata karki yarda dadik horewar kunnenda jolde zata maki kinji,nine namijinda yafi dacewa nazama mijinki,ina matuk’ar k’aunarki bunayy....” bai karisaba bunayya tai wata iriyar k’ara tareda dafe kunnayenta tana kuka. Rik’o hanunta yai tai saurin kaucewa tareda mik’ewa tsaye taja da baya tana kuka,shikowa binta yake yana fadin “karki gujeni bunayya,wlh zan iya mutuwa idan har ban aureki ba,ina matuk’ar Sonki ina kaunarki acikin zuciyata bunayya” juyawa tai dagudu tashige d’akinta tarufe tafada kan gado tana kuka matsananci,itama momy kuka take sosai kamar ranta yafita. Gaba daya dady yafita a hayyacinsa,zowa yai kan k’ofar dakin na bunayya yaita bugawa yana fadin “I really love u more than allot bunayya, dan Allah kitaimakeni ki aureni” tanajinsa saita dafe kunnayenta tana kuka mai tsanani. Dakyar momy taiya mik’ewa tsaye taje tad’akko key car tafito sannan taje tafito da bunayya bayan wucewar dady,mota suka shiga momy taja suka fita. Kai tsaye gidan hajiyarsu dady tawuce sbd yanzu tasan komai yariga daya b’aci, bayan sun iso saita fara shiga side din hajiyarsu ramadan,hajiyar ya ramadan ta matuk’ar tausayawa momy akan halinda take ciki,itakam sam bataga lefin momy ba kokadan tabbas dady yafita laifi. Suna zaune acikin parlo kwatsam saiga hajiyarsu dady tashigo fuskarta d’auke da tsintsar fusi da bacin rai saikuma ga abban ramadan yabiyo bayanta dasauri. Batajira komaiba tai cikin momy da masifa da zage zage da cin mutunci “wawiyar banza wacca bata gaji arziki ba mai farar k’afa dangin mayu, shine kikaje kisamo y’ar wasu kikazo kika lak’abawa d’ana amatsayin jininsa,to wlh k’aryarki tasha k’arya maryam,Allah yatoni asirinki yau kuma wlh saikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34