Chapter 1
Chapter 1
[7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _Alhamdulillah....all praise is due to Allah am back again ma people, hope zaku bani had’in kai wajen yin comment n’ sharhi, wannan bana kud’i bane kamar mujarrabi, so just follow me domin jin sak’onda nakesan naisar, love u all ma people._💔 _Page 1/2..._ UGANDA CITY......... K’ayateccen gida ne kantameme mai girman gaske wanda yake acikin wata katafariyar unguwa mai d’auke da manyan shaharrun y’an kasuwa, daga ganinsa tabbas kaima zakasan cewa gidane wanda ya amsa sunansa na gida. K’ayateccene mai kyan gaske, hawa biyu ne wato upstairs fentin gidan kuma maroon and white color ne and then yana d’auke da get biyu ta gaba data baya ne. A gaban gidan kuma akwai flowers kala kala masu kyalli da shek’i waenda ke kara haskaka haraban gidan, dagacan gefe kuma maka makan motoci ne kala kala na hawa waenda aka ajiyesu a gunda aka tanadar domin ajiyesu. Kutsawa nai domin bamawa idanuwana hakk’insu izowa cikin gidan domin nasan dik had’uwar compaunde din gidan batakai cikin gidan ba. K’ofarda zata sadaka da cikin gidan nashiga, wow masha Allah barakallah kaga inda ake b’arin naira tamkar ginarta akeyi ba nema ba. Dank’ara dankaran kujeru ne royal chairs Golding color masu kyan gaske nafara hangowa saikuma dana daga kaina izowa wani gun saina hango manyan hotunan masu gidan kala kala, saidai har nagama ganin hotunan banga na yaran gidan ba watodai alamar ko ba yara a gidan kokuma dai haka kawai ne ba’a d’oraba. Ina shirin bin wata k’ofa saikuma naga mutum wanda naga hotonsa a bangon falon yafito daga wata k’ofa dasauri yana sanye da jallabiya bak’a yakuma sake bin wata k’ofar yafice. Da’alama dai shine mai gidan. Bayan dakamar 5mnts saigashi yafito rik’e da wata mata wacca dagani matarsa ce dan itace naga hotonsu mak’ale atare, da’alama kuma nak’udace takeyi kokuma dai batada lfy ne. Sai wani irin nishi takeyi jikinta nata karkarwa kamar maijin sanyi tarik’e hanunsa daya gam dayan kuma yana kan shoulder d’insa, jini kemata zuba sosai ak’asanta dakyar take takawa shikuma sai sannu yake mata dagani dai shima hankalinsa amatukar tashe yake. “Uwani...jalila kuna inane wai” naji yafad’a amatukar tashin hankali. Dasauri wata mata tafito daga wata k’ofa d’auke da wasu kaya waenda dagani na mai haihuwa ne tana fadin “Alhj gamunan zowa” tana fitowa itama dayar saigata tanabin bayanta. Dayar ce tazo dasauri takama dayan hanun matar domin taimakawa Alhjn, nan suka rankaya izowa waje. Koda suka fito kowa tini anfito da motarda za’a d’auketa aciki gefen motar kowa dik hadiman gidan ne maza da mata ke tsaye kowa yai jugum jugum wasu har matsar kwllah sukeyi sauran matan kuma kuka suke suna fadin “Allah i saukeki lfy hajiya, Allah i baki abunda kike bid’a rayayya mai albarka”. Nandai aka shiga daita cikin motar sannan waenda aka kira da uwani da jalila suma suma shiga shikuma Alhj yakoma a gaba kusa da driver. Kai tsaye wata katafariyar hospital suka nufa, dazuwansu kasancewar anan ne ake kula da’ita dakuma abunda ke cikinta nantake aka karb’eta aka shiga daita izowa labour room sukuma suka zauna zaman jira. Tsawon awa biyar bawani good labari dasukaji nurses sai faman zarya suke daga d’akin zowa waje, sudikansu sunkasa zaune sunkasa tsaye musamman shi Alhj wanda gaba daya yakasa zama tamkar shine ke nak’udar. Saida takwashe kusan 7hrs sannan wata nurse tafito tacemasa yashigo cikin labour room din. Dasauri yabi bayanta izowa ciki, yana shiga yahangota zaune rungume da baby tanata faman kuka hawaye faca faca a fuskarta, dasauri yak’arisa gunta tareda zama kusa daita, damuwa da tashin hankalinsa suka karu fiyeda da din. Cikin razana yasa hanu ya karb’i babyn bakinsa na rawa wajen fad’in “la....la...lafiya hajiya jolde, meke faruwa ne” gaza cemasa komai tai kawai saita rungumesa tana wani irin kuka mai cike da tsintsar ban tausayi. Daya daga cikin nurses din ne tafara masa bayani “am dafarko dai muna masu baku hkr akan abunda yafaru wanda zamu kirashi da k’addara daga ubangiji, koda yaronku yazo duniya bashida rai yariga daya mutu tin a ciki, tsabar wahalarda yasha ce ta nakuda yasa har lkcnda yadace yafito waje yawuce bai fitoba, so am very sorry Allah isake baku wanda yafisa mai albarka”. Gaba daya jikin Alhj yai sanyi baisan lkcnda kwallah suka tsiyayo masa ba saiya kalli babyn kyakkyawa dashi tamkar bacci yakeyi, sumbatarsa yai tareda mannasa a kirjinsa yana zubda kwallah masu zafin gaske. “Kadel arka yarda da abunda nurses dinnan ke fada karya sukeyi ni d’ana bai mutuba bai mutuba wlh yana nan daransa bai mutu ba” sumbatarta yai a goshi cike da tsintsar tausayi sannan yajanyota yarungume yana fadin “kiyi hkr jolde kidaure kicinye wannan jarabar da ubangijinki yake jarabtarki daita acikin littafen rayuwarki, kiyi hkr”. Yanata magana koda ya ankara ashe tini tasuma a jikinsa, cikin tashin hankali ya ajiye babyn yashiga jijjigata yana kiran sunanta amma ina tasuma ba rayuwa. Dasauri nurses sukayo kanta aka shiga ceton rayuwarta, gaba daya hankalin Alhj kadel yagama tashi yarikice, dik yanda nurses sukaso yafito waje amma yaki dole suka kyalesa, tsawon lkc ana kanta amma yabun yaci tura, abun yafi k’arfin nurses din danhaka suka sanarda likita. Damacan doctor haji shine family doctor nasu kuma damacan yasan hajiya tanada hawan jini da asma toh yanzuma sune suka tashi bayan dakyar aka samu d’azun suka kwanta datana labour yanzu kuma gashi sun sake tashi. Dakyar da sud’an goshi aka samu asmar ta kwanta jinin kuma yafara komawa noraml, nan suka mata wasu injection aka saka mata oxygen da drip tafara bacci. Dasauri Alhj kadel yashiga office din doctor haji domin sanin mafita akan halinda yake ciki shi da iyalinsa. #/Vote #/Share #/Comment #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _Page 3/4_ Koda suka shiga office d’in kasa zama yai sbd yanda hankalinsa yake matuk’ar tashe,shikansa doctor haji hankalinsa atashe yake sbd yasan matsalar tasu ta haihuwa musamman ita hajiya jolde. Cikin tashin hankali Alhj yafara magana muryarsa har rawa take sbd yanda zuciyarsa kemasa suya. “Doctor miye mafita,doctor kataimakeni kada matata tasami matsala sbd na tabbata idan har ya tabbata wannan babyn yamutu tabbas itama koda bata rasa ranta ba toh zata samu gagarumar matsala a rayuwarta,ina matukar k’aunar maryam bana son komai yafaru daita,kataimakeni doctor” Gaba daya kan doctor haji ya d’aure yakasa samun mafita, can yad’ago yakalli Alhj kadel yace “nifa Alhj kana bani mamaki,wai na taimakeka kamarya kenan...? Inace babyn har a hanunka yake katabbatar cewa ya mutu,to kuma me kakeso namasa ne ko so kake nadawomar da ransa ne”. Dasauri Alhj kadel yamatso kusa dashi yace “ka fahimceni doctor,inaso nafad’ama wani sirrin,shi kansa wannan cikin dakaga anhaifa a yanzu bawai yashiga mahaifa bane ta hanyar jima’i, aa yashigane ta hanyar yin dashen kwayayan halitta nawa izowa mahaifarta sbd wani babban dalili, Inaso kasani doctor yau kimanin shekara goma sha biyar kenan da auren mu ni da maryam amma sau daya ta tab’a haihuwa yaron kwanansa biyu kacal Allah ya amshi abunsa. Tindaga lokacin maryam batasake koda b’ari bane bare haihuwa gashi tanasan yaya ido rufe, nikuma iyayena suntakurani har saida nak’ara aure inda yanxu nakeda yaya hud’u maza biyu mata biyu. Maryam tanasan yayan nawa sosai amma dayake mahaifiyarsu masifaffiya ce sai take hana yaran suzo gun maryam,bayanda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34