Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,240 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

inda take sai nurses da doctor kawai. Around 12pm dot mutan bagudo suka sauka,hmm.....abun mamaki agun y’an kallo,mamakine yacika mutanenda ke cikin asibitin ganin yanda dank’ara dank’aran motoci tsala tsala ke roshing acikin hospital d’in kuma dik na ahalin gidansu momy ne, uncle Muhammad ne wato babban yayan su momy wanda takebi yazo,shahararren d’an kasuwan nan wanda duniya tasani tareda k’annensa biyu maza uthman da Aminullah tareda mahaifinsu Alhj Ahmad, saikuma kannensu mata uku wato manyan hajiyoyin nan masuji da naira tak’ama dakuma alfahari,aunty kuluwa da yaya hauwa sai kuma kanwar momy Rukayya. Atare suke da bodyguards d’insu suna take masu baya har suka iso gun momy, bunayya naganinsu taje da gudu tarungume uncle Muhammad tana fadin “oyoyo my uncle” shima yarungumeta tareda shafa sumarta. Bayan sun gaggaisa dasu abban ruwaida da dadyn mashkur dan shima yazo sannan yaje sukai magana da doctor. Acikin yan mintina aka kammala komai sannan aka d’auki momy aka fice daita India. Mashkur yakoma school tareda bunayya,uncle Muhammad dasu abban ruwaida sune suka tafi India din, Tsawon sati daya da kwana uku suka kwashe acan ana kula da momy,Alhmdllh kuma tasamu sauki sosai,a ranarda suka cika sati biyu aranar suka dawo gida Nigeria momy har y’ar k’iba tayi masha Allah gakuma hasken ciki datai wanda yak’ara fito da yarintarta dakuma ainahin kyanta, bak’aramin dad’i bunayya tajiba aranarda suka dawo itakuma washe gari tazo tinda sassafe sbd yanayin karatinsu yafara zafi gakuma mashkur sunagab da kammala karatinsu. Uncle Muhammad yazauna dasu abban ramadan da abban ruwaida dakuma dadyn mashkur had’eda sauran yan uwan momy maza,inda ya tattauna dasu akan matsalarda take faruwa a yanzu har yanzu momy tana gidanta bata koma gidan dady ba. To magana tai nisa har suka kaiga yanke shawara akan za’a aurawa mashkur bunayya nanda wata d’aya kacal, batun dady kuma abban ramadan yace abarmasa komai hanunsa shi zaisan yanda zaiyi dashi momy kuma tacigaba da zama a gidanta har izowa lkcnda zasu zauna da hajiyarsu dady domin shawo kanta tinda dai ba’asaki da ciki sannan yanzu komai ya daidaita ayafi juna kawai. To Alhmdllh anan shawara tatsaya akai addu’ah sannan aka watse. Haka kowa akayi momy tacigaba da zamanta acikin katafaren gidanta dakuma d’ankaramin cikinta wanda yakeshan kulawa sosai dakuma y’arta abar k’aunarta. Bayan kwana uku dayin zamansu uncle Muhammad akai k’ayataccen baikon y’ayan shahararrun y’an kasuwa dakuma ma’aikatin gomnati had’e da yanka sadaki dakuma saka rana wata mai zowa, mashkur da bunayya. Baikone akayi nagani na fad’a idan kaga yanda akai baikon kaikace wani d’aurin auren d’an sarki ne,uncle Muhammad yasaki naira yanunawa momy tsintsar sonda yakemata a fili amatsayinta na k’anwarsa shalelensu, hakama sauran yan uwansu dik sunyi tasu bajintar,mashkur da bunayya suna school labari yarizk’esu. Ranar bunayya saidatai kwallan farinciki sbd lbrnda momy tabata, nan taji k’aunar momyn tata tak’ara mamaye zuciyarta, tayi tinanin abunda yafaru yan uwan momy zasu gujeta su daina sonta kamar yanda suke santa abaya amatsayin y’a d’aya tilo agun yaruwarsu,ashe abun bahaka bane har yanzu suna k’aunarta basukuma daina d’aukanta matsayin yarsu tajini ba. ..................... Ahankali komai yafara dawowa daidai sbd shirye shiryen shagalin babban bikinda zaayi wanda ba’atab’ayin irinsaba atarin ahalin uku,dika b’angarorin uku shirye shirye akeyi musamman momy datafi kowa farinciki da zumud’in zowan ranar. Tini tatura kud’i Dubai domin ayomata kayan d’aki set biyar,yayinda shima abban ruwaida ke nasa shirin domin nuna tasa bajintar,dadyn mashkur kowa kantamemen gida yake ginawa d’ansa naji da gani upstairs hawa biyu had’eda tikitin zowa honeymoon natsawon wata biyu. Ab’angarensu uncle Muhammad kowa,hotel hotel yake kamawa domin manyan bak’inda zasuzo nasa dana momy tindaga bagudo har kebbi ak’alla yakama hotel goma sha biyar tareda zirga zirgan bak’in, saikuma shirin garar gidan miji dayad’auki nauyi wacca zaiyi, aunty kuluwa shahararriyar mai gyaran amare tad’auki nauyin d’akkowa daga mai duguri domin tagyaramata y’arta amarya bunayya. Hakama b’angaren abban ramadan suna nasu shirye shiryen taryan bak’insu dakuma shirin ranar d’aurin aure sbd ana zaayi tinda nan ne gidan uban amarya. B’angaren umman ruwaida ma nasu shirin suke,saikuma b’angaren ango daketa faman shirye shiryen angonci amma b’angaren amarya kam shuru kakeji ita karatintama tasaka agaba, Kai zan yacemaku koinama shirye shirye ake sosai na shagalin bikin y’a d’aya tilo agun hajia maryam jolde. Dadyn bunayya abun duniya yataru yamasa yawa,komai yajagulemsa lissafinsa yajagule gaba d’aya yarasa yanda zaiyi,neman momy yake ruwa a jallo sbd yanzu gaba d’aya tadaina fita office tinda wannan lamarin yafaru,yanzu jinyar kanta take dakuma rainon cikinta. Yarasa yanda zaiyi gaba d’aya yafita hayyacinsa ga rashin bacci gakuma abubuwa dasuka k’ara jagulemasa waenda yasani tabbas momy ce kad’ai zata iya warwaremasa su sbd damacan itace abokiyar shawararsa. #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _33/34....._ Rayuwa tacigaba da tafiya cikin farinciki da walwala,bunayya karatinta tasaka agaba sbd yanzu kwana biyu kacal suka ragemasu sufara zana jarabawa,yayinda a b’angaren ango mashkur kowa yaketa k’okarin ganin yakammala project dinsa nanda sati d’aya kacal zasu kammala komai na degree dinsa nabiyu. Kimanin sati d’aya kenan rabon mashkur yasaka bunayya a ido sbd yanayin karatinsu sudika gaba d’aya,bawanda keda lkcn kansama acikinsu kowannensu k’okarinsa yaga yasamu sakamako mai kyau. Saidai mashkur kam gaba d’aya bayajin dad’i sbd rashin ganin hasken idanuwarsa kuma sanyin idanuwansa,haka itama bunayya tana kewar yayan nata amma kunya tahanata tanemesa bare ta tambayesa koda agun abokanan karatinsa ne, a wayama bawani cika yin waya sukeba,hakan yasa kewar junansu tamasu katutu acikin zukatansu. Sannu ahankali har su bunayya sukafara zana jarabawan first semester ta 200level, abun ba sauk’i kokad’an saidai ace Alhmdllh amma sunashan fama kam,any time suna wajen karatu dikta rame tak’arin haske sbd dama can bunayya badamuwa tai dacin abincin kirkiba sai mashkur yaita fad’a koya sakata agaba sannan takecin tuwo ko shinkafa,ita bartadai da kayin mak’u lashe,to bare yanzu da exam tasa ruwanta shkn sai k’arisawa kawai. A ranarda sukacika one week da fara exam aranar mashkur yakammala komai suka fara shirin tafiya gida,tin 3pm yasaka anemomasa bunayya amma baagantaba kaf school din sai kusan 5pm sannan akazo aka fad’amasa suna cikin exam,kokad’an baiji dadin hakanba yaso matuk’a yaga bunayya sbd yana k’ishirwarta sosai,gashi kuma tin 2pm akazo d’aukansa amma sbd ita yahana sutafi har wannan lkcn, neehal k’anwarsa ta uku da’akazo d’aukansa daita tace “haba brother,kazo mutafi mana,aunty bunayya fa takace nanda wani d’an lkc za’akawoma ita kaita ganinta kana kallonta har kagaji,tomeyasa zaka wani tsaya kace dole saikaganta yanzu,wlh mungaji sosai ni yunwama nakeji momy kuma sai kira take inacemata har yanzu bamuko tasoba bare har mu’isa gida” sauran yan uwanta najin tayi magana nan suma suka saka nasu bakin sunamasa magiya. Aiko badan yasoba dole yashiga mota suka fice batareda yaga abar k’aunarsa ba. Bayan su bunayya sunfito hamdallah kefad’amata mashkur yasaka akirata amma lkcn tana d’akin jarabawa harya wuce,yaune suka kammala dik sun wuce gida yan masters degree din nan, bunayya kamar tai kuka dataji lbrn nan hamdallah taita mata dariya. Haka itama suka cigaba da zana exam dinsu ahankali,dik bayan kwana biyu mashkur yakan kirata susha soyayyarsu kamin daga bisani yabarta tacigaba da karatinta na exam. Sannu ahankali lkcn biki ke k’ara k’aratowa yayinda aketa cigaba da shirye shiryen shagalin bikin. Aunty kuluwa tini takira mai gyaran jiki domin tafara aikinta sbd sati biyu kacal yarage afara bikin sbd haka tanaso amata gyaran

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});