Chapter 14
Chapter 14
Kukan shagwaba tafara masa shikwa sai kallonta yake yana murmushi,ganin bashida alamar rarrashinta yasa saitai shuru tana hararansa tace “bazaka rarrasheni ba” murmushi yai yace “bazanyiba sbd k’aramun kyau kike idan kinayinsa,sainaga kyakkyawor fuskarnan taki tana k’aramun haske da kyalli musamman yau da hamdallah tak’ara gyareman ita,bazan b’oyemakiba bunayya kinyi kyau sosai,kinada kyau sosai dan kecema kikayiwa kwalliyar kyau ba itabace tamaki kyauba”. Kunyace takamata saita rufe fuskarta da mayafinta tace “kod’awar taisa haka,ninasan yanda kake fad’ar wannan kyan baikai hakan ba” murmushi yai yace “yamawuce hakan” saitai murmushi kawai tana wasa da y’an yatsunta. Kallonta yake har yanxu musamman bobbs d’inta da mayafinta ya yaye, tana fahimtar hakan saitai saurin jan mayafin tagyara,kunya takamasa sbd yasan tagansa. Shuru yad’an ratsa motar kowa da abunda yake sak’awa ransa, can yakalleta yace “Shkn fushi yak’are koh” murmushi tai tareda rufe fuskarta da tafukan hannayenta,shima murmushin yai saitace “to ai dama kaine” yace “nine nayime,dan nafadi gsky” tace “uhm...” sbd tafara gajiyawa da firar shima ya fahimci hakan sbd yafi kowa sanin halin kayansa danhaka yakyaleta. Tafiya tayi nisa tin ana fira har bunayya tagaji takwantarda seat tai bacci, ahankali yake driving kuma yana kallon kyakkyawor surarta dakuma kyakkyawor fuskarta,wani irin murmushi yai wanda shikad’ai yabarwa kansa sanin maanarsa, hanunsa yakai yajanyo mayafinta daya yaye a lkcnda tagyara kwanciyarta,bobbs d’inta dik sun bayyana danhaka yasaka mayafin yarufemata jikinta sannan yasauke nannauyan numfashi yamaida hankalinsa kan tukinsa. Around 4:40pm suka isa garin yola adamawa, suna isa saiya tadata sannan suka kama hanyar unguwarsu, mik’a tai tagyara zamanta, ahankali harsuka iso gidan. Wani kantamemen gida ne wanda yake zagaye da police suna gadinsa, agaban gidanma wasu manyan police masu jini a jikane ke gadinga su hud’u kowannensu d’auka da bindigogi bayan waenda ke zagayar gidan saboda tsaro. Suna ganin mashkur dasauri sukazo suna kwasar gaisuwa sai daya daga cikinsu yana sosar kai kamar mara gsky yana yar dariya yace “oga koitace madam d’in” saitai mashkur yai dariya yace “kaganka oshere bakarabuwa da sa’ido koh, tome kaganine dazakace koitace madam?” oshere yace “toh oga tinda mukedai anan bamu taba ganin kazo gidannan dawata ba bayan k’annenka su samirah,kaga kowa ai dole muce koitace madam yau aka kawomana mugani” dariya kawai yai bunayya najiran taji amsarda zai basu saikawai yadanna hancin motar izowa cikin gidan. Kallon gidan tadingayi kamar government house kokuma dai gidan wani babban ma’aikacin gomnati, kai yafidai kama da gidan gomna kokuma vice dinsa kokuma IG na police sbd yanda tsarin gidan yake. Yana isa gunda aka tanadar domin parking din motoci yai parking saiga wasu security’s sunzo dagudu suka amsa key din motar sannan suka bud’e bayan motar suka fito da akwatinda ke ciki suka fice izowa cikin gidan. Mashkur dakansa yabudewa bunayya murfi tafito sannan yajera atareda ita yanad’an tsokanarta har suka iso kofar shiga, suna bud’e kofar saiga wasu yan mata guda uku sukazo dasauri suka rungume mashkur da’alama kannensa ne suna fadin “welcome brother” shima cikin farinciki yake amsa masu kamin yajuya ga bunayya yace masu “am this is urs sister bunayya,bunayya waennan sune k’annena ramlat da raliya twins sai kanwarsu rumaisa,aikwa mai kama dake ruwaidah sai rashid auta, rufa’i kebina da haihuwa” murmushi tai tace “masha Allah,ashedai da me kai tsohone dik waennan kannenka ne” saisukai dariya yace. “Am....yaudai gatanan nakawomaku nacika alk’awari” sunji dadi sosai kamar hadiye bunayya cikin farinciki d’ayar tariko hanunta sunamata sannu da zowa. Kamar su had’iye bunayya, suna zaune parlor saiga momynsu tashigo dama itama tin d’azun sutake jiran isowarsu,kana ganinta kasan itace mahaifiyar mashkur sbd yanda yake kama daita sosai, Itama tsintsar so tanunawa bunayya,yaudai bunayya taga soyayya kamar yar gold haka suka dinga tarairaya daita,mashkur yace “wai ina ruwaida da rumana ne?” momyn su tace “nice na aiketa tareda security gidan adda maryam,amma yanzu zasu dawo sbd tindazu suketa tsumayinku,ta matsu bataga bunayya ba. Bunayya tai murmushi, yammatan janta sukai suka shige ciki sukabar mashkur da momynsa a parlor kasancewar bakowa gidan suna gidan biki a family nasu ake biki. Suna ciki su ruwaida suka dawo,bunayya nazaune tashigo aibatasan lkcnda tamike a tsaye ba dasauri tareda kurawa ruwaidah ido,suma su ramlat kallon ruwaidah da bunayya suke sunaso sugano bambamci tsakaninsu amma sunkasa. Bunayya matsawatai kusa da ruwaida tana kallonta cikin tsintsar mamaki,bawanda yaiya cewa wani komai sbd halinda suka tsinci kansu na tsananin mamaki,sai kallon kallon sukemawa juna. “Bunayya and ruwaida” sukaji anfad’a ta kofar shigowa,hakan yasa suka waiga domin ganin mai shigowa, mashkur da momyn sa da ra’uf ne sukagani,mashkur na murmushi ya rungume hannayensa. K’arisa shigowa sukai mashkur yamatso dab dasu yai tsaye yana kallonsu daya bayan daya, wani killer smile yai kamin yafara magana “hmm....Alhmdllh,yau nacika burina da nadad’e inata burin naga nacikasa wanda saiyau Allah yabani ikon cikasa, a yaudai nahad’a y’an uwa biyu yan uwa najini waenda su kansu basusan su y’an uwan juna bane maana bunayya da ruwaidah waenda suke hassana da hussaina” kallon mamaki da rashin fahimta bunayya kemasa. Matsowa tai kusa dashi cikin tsintsar mamaki tace “what...what....what do u mean mashkur, kaman bayani mashkur mekake nufi ne...?” kallon cikin idonta yake yace “bunayya ina nufin ruwaida yar uwarkice ta jini wacca kukafito ciki d’aya daita kuma tagwaye,ke abokiyar tagwaicinta ce amma bansan wacece hassana kokuma hussaina acikinku ba,but...of course ruwaida yar uwarkice”. Wata yar dariya tai sannan tace “Nooo...mashkur wasa kakeyi wlh,ni nikad’ai mahaifiyata tahaifa wlh nikad’aice Allah yabata a duniya,bayan ni batada wata y’a a doron duniya kuma bata tab’afadaman mu yan biyu bane,kuma bata taba bani labarin cewa mu yan biyu ne tahaifaba,sbd haka wannan labarin naka k’aryace,zan iya amincewa da kamanceceniya ce mukeyi da ruwaida amma bawai ace mu yan biyu bane,sbd babu dalilinda zaisa na amince da hakan”. Wani murmushi mashkur yai sannan yace “nikwa nakeda kwararan hujjoji akan hakan, kuma yanzu zan bayyanemaki su” saiya cigaba da magana “bunayya tin farkon had’uwata dake a restaurant nafara nunamaki idon sani sbd ganin tsintsar kamanceceniyar da kike da k’anwata ruwaida,nayi dik yanda zanyi wata alaka tashiga tsakaninmu domin natabbatarda cewa ked’in ba yar uwata tajini bace amma nakasa sbd rashin sakewata da mata,hasalima ni ko sabgar matan school din bana shiga hatta yan department dinmu bakowa nake alaka dashiba bare ku yan 100level, cikin ikon ubangiji ina nan ina neman yanda zanyi nasamu kusanci dake kwatsam sai Allah yajefani ta bayan hostel dinku naje neman wani saina tadda waencan yan iskan school din zasu maku fyada,nan nataimakeki wanda wlh harga Allah bansan ke bace kawai nayine domin taimako saikuma aka dace ashe kece. Wannan dalilin taimakon dana makine Allah yai ikonsa kusanci yashigo tsakaninmu har muka shak’u da juna wanda takaiga ahalina suka sanki kema kuma naki ahalin suka sanni. To saidai wani abunda bakisaniba shine,a dik zamanda nai dake inatafaman bincike akankine domin tabbatarda zargina,akwai watarana danakaiki clinic lkcn kina ciwon mara period dinki yai to a lkcn ne nasaka nurse tadiboman jininki naje nakai aka gwada dana ruwaida kuma tsab yazama iri daya,hakama mahaifiyar ruwaida jininku daya sbd itace mahaifiyarku ta asali,sannan koda makaho yatab’aku zai gane ku jini dayane,kamanceceniyar ku harma tai yawa sbd wlh bawanda zai iya banbanceku, shaidata ta k’arshe itace,inaso muje gun ainahin iyayenku kigansu suganki sannan sumana cikekken bayani ruwaida twins ce kokuwa,idan twins ce ta’akayi suka rabu da yar uwarta,nikuma namaki alk’awarin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34