Chapter 26
Chapter 26
Dahaka dahaka har suka iso garin habuja ammafa sunci kwakwa sosai, 6pm dot suka iso garin habuja, sungaji sosai amma haka suka hkr ba halin kama hotel sbd dady yaga hotunansa an manna koina ana nemansa wanted. Danhaka kai tsaye suka fice flyt dama by 8pm jirginsu zai d’aga. Har suka kammala komai nawani cike cikensu dika wani ikon Allah amma bawanda yagane dady kokuma ace sai bunayya ta bud’e face d’inta ta yaye nikab d’inta kodan halinda wannan kasar tamu take a ciki na saka boma bomai a koina amma dik Allah yab’atarwa da ma’aikatan basira da hankali. Haka shima dady sam basu hankalta suka fahimci kasumbarsa da sumarsa dik nasakawa ne ba ainahin nasa bane, ahaka har suka shigo gunda jirgi yake jira kawai suke abada izinin shiga jirgin sushige sai kwatsam wata CCTV camera tafara nuna danja tana nuna alamar akwai matsala, can d’ayarta tafara nuno hoton dady dana bunayya wanda aka nunawa na’urar idan tahango masu irin faces din, can itama d’ayar tanuna location dinda suke. Ai dady bai ankaraba sai ganin wata danja yai ja tana kallonsu, aikwa bunayya naganin hakan dasauri ta yaye nik’ab d’inta tama cire hijab din gaba daya sannan tagantsarawa wanda yake rik’e daita ciza a hanu dole yasaketa dayaji zafi sannan tagudu. Dafarko dady yaso yabita amma dayaga komai ya kwab’e ya jagule saiya fara neman hanyar guduwa, suma yaran nasa hanyar guduwa suka kama, malamansa kowa rikicewa sukai suka daburce. Dagudu security’s sukabi dady da yaran, sukuma malaman aka kamasu aka fice dasu,itama bunayya aka fice daita, dady da yaransa kuma sai abakin get aka kamasu sbd tini har ansanar anrufe get bakuma wata hanyar gudu, dady daya rikice saiyaibatun haura katanga sai d’aya daga cikin security’s din yaharbamasa bindiga a k’afa,hakan yasa yafad’o ba shiri, koda bunayya suka iso wajen taga halinda dady yake ciki dagudu taje gunsa tanata kuka mai tsanani tarike hanun dadyn wanda tini yasome. Daganan aka d’aukesu aka fice dasu. ................... Momy na a zaune tai tagumi tanata zubarda kwallah saiga kiran uncle Muhammad yashigo wayarta, aikwa dasauri tad’aga jikinta har yana makyarkyata,cikin zumud’i uncle yalabarta mata bayyanar dady da bunayya a flyt din habuja zai hau jirgin k’asar Abu Dhabi, aidan farinciki saida momy tai sujudul shukru, amma dataji an harbe dady a k’afa saikuma taji ba dad’i taji ranta yab’aci. Around 4am dot aka iso da bunayya kebbi state dady anfice dashi babbar asibitin dake habuja yayinda sukuma yaransa aka fice dasu station aka rufe, hmm farinciki da murna dakuma kuka aka rasa wanda zaayi, kowa sai kukan murna momy ta rungume bunayya sukaita kuka. Gidan yacika sosai da mutane maso zowa Allah ikyauta ikara tsarewa, dama kuma ga yan biki dasukazo. Dole tasa aka d’an d’aga bikin izowa offer week dole. Farinciki agun mashkur kamar yatake kan jariri dandai bunayya nacikin mutane ne dasaiya rungumeta ko sanyi yaji, hhh Lol. Sai washe gari suka koma yola taredasu dadynsa shima dandai su dady sunsakashi agabane amma baiso tafiyarba sbd dama yai kewar y’ar k’anwarsa sosai yanaso sud’an shiga labule,amma ina su dady suka hana, bayanda yaiya dolensa yabisu suka fice. Tsaro na musamman uncle Muhammad yasaka daga gidan momy har gidan aunty kuluwa da yanzu aka kai bunayya akafara mata gyaran amare har family house dinsu momy, security’s masu tsananin tsaro yad’akko suna takewa bunayya baya dik inda zataje guda biyar, yanzuma tinda aka fara guaran nan koina anhanata fita, acikin gidan aunty kuluwa ma ba koina take shigaba, daga parlon aunty sai bedroom dinda take sai toilet shkn. .................... Yanzukam hankalin kowa ya kwanta sbd yanda akebama gidajen dika biyun tsaro na musamman daita kanta bunayya. Gyara namusamman akemawa amarya bunayya,acikin yan kwanaki fatarta tamurje tacanja, hakama acan cikin jikinta dik ank’ara matseta da matsi dakuma kazar amarya datakeci, gakuma tirarikan tsuguno datake amfani dasu masu kyau na y’an mai duguri. Koda tacika sati d’aya da fara gyaran ita kanta saida tasan amarya ce takuma tabbatarda lallai ita amarya ce, dik wanda yaga bunayya saiya shaida lallai ita amaryace, koda mace yar uwarta taganta saitaji sha’awar inama itace bunayyar sbd yanda fatarta tacanja tai laushi tai sentsi sai kyalli take tana shining kamar tauraruwa asararin samaniya. A ranarda za’afara gudanarda shagalin bikin aranar aunty kuluwa tasaka aka tsattsaramata lalle ja da bak’i mai shegen kyau sannan akamara saloon aka gyara sumarnan aka bazota har gadon bayanta tana kyalli gwanin birgewa, kai masha Allah readers naso kuga irin kyanda amarya bunayya tai, but...karku damu ni naganemaku Lol. Sannu ahankali aka fara gudanarda shagalin biki inda aka fara da kamu, acikin shahararre kuma katafaren gidan ya Amir aka gudanarda kamun, amarya tai kyau sosai kayanta pich color zani da riga na wani tsadajjen material akamata d’inkin yoruba sannan aka d’aura mata dan kwali aka saka mayafi aka rufemata fuska. K’awayenta kuma material suka saka see green color sukai gown dashi, hamdallah namak’ale da bunayya hakama ruwaida, dik wanda yaga ruwaida yaga bunayya yasan twins ne saima maganarsu ake wajen kamun sbd kamanceceniyar su tai yawa sosai. Tin anan ya ramadan yamak’alewa ruwaida harya fad’awa bunayya da momy shifa tamasa,aikwa me momy zatayi banda dariyan farinciki, haka akai kamun cikin tsintsar farinciki aka watse. Daganan gidan momy aka wuce da amare, suna zowa tacire kayan nan takwanta kan gado sbd tagaji sosai, sallah ma dakyar momy tasamu tayita wai ita adole tagaji. Tawani manne a cinye momy kamar zata shige cikin momy ne,da’alama dai yau shagwab’ar tamotsa ne Lol bunayya ba’a girma. Angofa yayi kewar amaryarsa sosai yanzu tinda aka fara shagalin nan ko awayama baicika samuntaba, saiyai kusan 6miss calls kan yasamu ad’aga wani lkcnma wayar bata hanunta,bayanda yaiya dole yake hkr amma badan yaso hakanba. To yanzuma shine yakira ruwaida takawomata wayar, danhaka tad’aga tafita. Washe gari Arabian day amma shi a wani katafaren holl ne zaayishi Royal event. Tin 3pm akafara shirya amarya saikusan 5pm aka kammala sannan aka d’auketa izowa gunda za’a gudanarda event din. #/Comment Nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _37/38...._ Ranar yau ta ahalin shuwa arabs ce, tinda yau ake Arabians day, dik girman holl din Royal event saida yacika taf da shuwa wasuma harsun rasa gun zama sai tsaye sukayi. Amarya da yayyenta mata da yan uwanta mata dakuma k’awayenta dakuma iyayenta mata da maza dan hatta abban ramadan yaje, momy dataje batawani jimaba tafice wai ita kunya. Anci kuma ansha anyi ankuma gudanarda al’adu daban daban na yaren shuwa, daga bisani akai pictures sannan aka watse kowa yakama gabansa. Washe gari itace ranarda za’ayi walima itace kuma ranarda zaa d’aura auren mashkur da bunayya, da dare kuma a gudanarda dinner amma ita a yola zaayita sbd abokanan mashkur ne suka d’auki nauyinta. Har safiya tawaye bunayya bata rintsaba sai faman juyi take akan gado zuciyarta acike da tarin mamakin wai itace za’ad’aurawa aure gobe, a wani b’angaren kuma tarin kewar mahaifiyarta ne yamata katutu yahanata sakewa,gakuma tinani da tausayin halinda dadynta yake aciki,musamman idan ta tino da irin daddad’ar rayuwarda sukai abaya tindaga Australia har London. Bata ankaraba kwallah suka fara bin kuncenta,ta d’auki abunda yafaru amatsayin k’addarar rayuwarta kawai, zakuma ta dauwama tana yiwa mahaifan nata adduah dakuma fatan dacewa gobe k’iyama, sunrik’eta rik’o nakwarai sunkuma kula daita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34